SHAFA A KAN HUFFI DA SAFA DA BANDEJI
Addinin Musulunci addinin sauki ne da rangwame, babu takura ko tsanani a cikinsa. Daga cikin ire-iren wadannan sauƙin su ne bayar da damar yin shafa a kan huffi ko takalmi sau ciki ko safa, idan aka sanya su bayan an yi alwala.
Don haka, a qarƙashin wannan babi, akwai bayanai kamar haka:
1. Menene huffi da takalmi sau ciki da safa?
2. Hukuncin yin shafa a kan huffi.
3. Sharuɗɗan yin shafa a kan huffi.
4. Siffar yadda ake yin shafa a kan huffi.
5. Tsawon lokacin da za a ɗauka ana amfani da shafa a kan huffi kafin a cire a yi alwala.
6. Abubuwan da suke ɓata shafa a kan huffi.
7. Hukuncin shafa a kan karan ɗori ko bandeji.
8. Abubuwan da ake shafa a kansu guda biyar su ne huffi, takalmi, safa, rawani, sai kuma karan ɗori ko bandeji ga mai larura, ko hijab ga mace, idan tana wurin da ba za ta iya buɗe kanta ba yayin shafar kai.
9. Al-Imam Muslim ya ruwaito hadisi daga Hammam, ya ce Jarir Ɗan Abdullahi (رضي الله عنه) ya yi bawali sai ya yi alwala, sannan ya yi shafa a kan huffi, sai aka tambaye shi me ya sa ka yi haka? Sai ya ce, na ga Manzon Allah ﷺ Ya yi yadda na yi, ya yi bawali sai ya yi alwala sannan ya yi shafa a kan huffinsa.
10. Malam AlHasanul Basri ya ce, “Sahabbai guda saba'in suka ba ni labarin cewa Annabi ﷺ Ya yi shafa a kan huffi.”
Shafa a kan huffi yana cikin abubuwan da Annabi ﷺ ya yi, kuma ya ce a yi, sannan ya ga ana yi bai hana ba. Don haka, dalilin yin shafa a kan takalmi da safa shi ne hadisin
11. AlMugeeratu Ɗan Shu'ubah ya ce, (رضي الله عنه) Manzon Allah ﷺ ya yi alwala, sai ya yi shafa a kan huffi da takalmi.()
12. An kuma ruwaito daga Malam Yahya Al-Bakka'u ya ce ya ji Abdullah Ɗan Umar (رضي الله عنه) yana cewa, “Shafa a kan safa, kamar shafa ne a kan huffi.” (Albani ya inganta shi). () 13. Waɗannan su ne kaɗan daga cikin hujjojin da malamai suke kafa hujja da su a kan shafa a kan huffi da takalmi da safa.
14. Huffi ana yin sa da fata, kamar su ɗaya da takalmi, irin takalmin masu aikin ɗamara, sai dai shi ƙasansa da fata ake yi.
15. Safa kuwa kamar yadda muka sani, akwai mai kauri da mara kauri, mafi yawa kuma bayan an saka ta ana sanya takalmi a kan ta.
YADDA AKE SHAFA AKAN HUFFI.
A taɓo ruwa da hannu ɗaya na dama, sai a ɗora hannun daman a kan saman huffin daga wajen `yanyatsu, sai a taho zuwa sama har zuwa idan sawu sau ɗaya da hannu ɗaya. Wasu malamai suna cewa sai an shafi sama da ƙasa, sannan aka yi yadda ya kamata, amma dalili mai ƙarfi ya nuna saman huffin kawai ake shafawa, kuma sau ɗaya kawai, kamar yadda aka ruwaito daga Sayyidina Aliyu (رضي الله عنه) ya ce, “Da addini da ra`ayi ake yin sa, to da shafar qasan huffi shi ya fi fiye da samansa, amma na ga Manzon Allah ﷺ yana shafar saman huffinsa.”
SHARUƊƊAN SHAFA A KAN HUFFI.
kafin a yi shafa akan huffi akwai buƙatar a cika waɗannan sharuɗɗa:
1. Ya zama lokacin da aka saka huffin a ƙafa an yi alwala an wanke ƙafar. Amma idan mutum ba shi da alwala ya saka huffin, to ba zai yi shafa a kansa ba, saboda hadisin Mugeerah (رضي الله عنه) ya ce, na kasance tare da Manzon Allah ﷺ a lokacin tafiya sai na karkato domin na cire masa huffinsa, sai ya ce, “ƙyale su, domin na sanya su a ƙafata ina da alwala.”()
2. Idan za a yi wanka wajibi a cire huffin domin yin wanka, kamar yadda hadisin Safwan (رضي الله عنه) ya tabbatar. Imam Ahmad ya ruwaito, Albani ya ce “Isnadinsa hasanun ne,” wato yana da kyau.
3. Kafin a yi shafa a kan huffi ko takalmi ko safa, sai sun zama masu tsarki tukunna, domin ba za a yi shafa a kan najasa ko abu mai najasa ba.
4. Kula da lokacin da aka ɗeba masa na yin shafa a kan huffin, a zaman gida kwana biyu (awa 24). A lokacin tafiya kwana uku (awa 72). Daga nan sai ya cire ya sake alwala. Dalili shi ne hadisin Abi Bakrata (رضي الله عنه) ya ce, Manzon Allah ﷺ ya yiwa matafiyi sauƙi kwana uku da dararensu. Shi kuma mazaunin gida kwana ɗaya, shi ne zai yi yana shafa a kan huffinsa. Sai idan janaba ta same shi, sai ya cire domin yin wanka.
5. Ya zama ya rufe ƙafa zuwa iyakar inda ake wanke ƙafa, wato zuwa idan sawu. An ruwaito daga Umar da Aliyu (رضي الله عنهما) cewa za a iya shafa a kan jaurabain wato safa ko da ba ta da kauri.( In ji Imamun-Nawawi a cikin littafinsa, Sharhul Muhazzab).
6. Ya zama huffin mallakinsa ne ba na sata ba ne ko qwace, ko kuma an yi shi da abin da aka haramta ga maza kamar alhariri, ko fatar mushe wadda ba a jeme ta ba (Al-Mugni). ()
7. Idan mutum ya sa huffi ya yi shafa a kan sa zai ci gaba da barin sa a qafarsa, amma idan ya cire shi, wajibi ne ya wanke ƙafarsa, idan ya zo yin alwala ta gaba.
ABUBUWAN DA SUKE WARWARE SHAFA A KAN HUFFI
1.Ƙarewar lokacin da Shari'a ta bayar, idan a zaman gida ne kwana daya, a lokacin tafiya kwana uku. Idan wannan lokacin ya wuce, sai a cire a wanke ƙafa, kamar yadda mafi yawan malamai suka rinjayar.
2. Idan janaba ta sami mutum zai yi wanka. Wajibi ne ya cire huffi, domin ba za a yi wanka da huffi a qafa ba.
3. Idan mutum ya cire huffi daga qafarsa, alhalin ya yi alwala kuma ya yi shafa a kansa, to dole ya wanke qafarsa tun da ya cire huffin da ya yi shafar a kansa.
4. Idan huffin ya yage har mafi yawan ƙafarsa yana fitowa, sai ya cire huffin ya wanke ƙafarsa, ya kuma ɗunke huffin.
5. Idan ya sa huffi guda biyu ko safa guda biyu, kuma ya riga ya yi shafa a kan na farkon, sai ya cire na biyun, to shafarsa tana nan, amma idan na saman ya shafa sai kuma ya cire shi, sai ya yi maza ya shafi na qasan, saboda ya cire wanda ya yi shafar a kansa.
6. Dukkan hukuncin da muka gabatar a kan huffi, ya shafi takalmi sau ciki da kuma safa mai kauri da mara kauri, kamar yadda ya gabata daga hadisi da kuma fatawoyin sahabbai da tabi`ai baki ɗaya.
Shafa a kan karan ɗori ko bandeji da aka ɗaura saboda karaya ko rauni. Idan mutum ya sami larura ta karaya ko rauni, aka yi masa ɗori, ya samu ya shafi wurin ɗorin a lokacin alwala ko wanka, ba sai ya wanke wurin ba saboda larura.
Idan ya ji ciwo a wurin da ake alwala kamar fuska ko hannu ko kai ko ƙafa, yana da hali huɗu:
Idan wajen ya buɗe kuma idan ya wanke babu wata fargaba, sai ya wanke wurin da ruwa, idan likita ya ce babu komai ana iya wankewar.
Idan wurin ciwon ba a ɗaure yake ba, amma idan ya zuba ruwa ya wanke ciwon zai ƙaru ko ya yi jinkirin warkewa, amma idan ya yi shafa a kai babu komai sai ya yi shafar.
Idan wajen ciwon yana buɗe, amma ba zai iya wankewa ko shafa a kai ba, sai ya ɗaure da bandeji ya yi shafa a kan bandejin.
Idan mutum ya ji rauni sai likita ya ɗaure wurin da bandeji, idan ya zo wanka ko alwala sai ya yi shafa a kan wurin, kuma haka zai riƙa yi har zuwa warkewa.
(A duba littafin Al-Fiqhu Al-Muyassar).
Allah ne masani .
Zamu ci gaba insha Allah.
0 Comments