DALILAN DAKE HADDASA MATSALAR RASHIN KARFIN MAZAKUTA (CAUSES OF ERECTILE DYSFUNCTION)




Rashin karfin mazakuta na nufin matsalar rashin cikakken karfin al’aurar namiji ko raguwar karfin al’aura yayinda aka fara saduwa ko kuma rashin mikewar al’aura yayinda ake bukatar fara jima’i. Bincike ya nuna cewa wannan matsala tafi yawa ga masu shekaru 40 zuwa 70, kuma tana karuwane a lokacinda mutum yake manyanta. Saidai duk da haka akwai matasa da dama masu irin wannan matsala. Wasu daga cikin dalilan wannnan matsalar sune kamar haka:

1. Ciwon suga, hawan jini da yawan kolesterol a cikin jini (diabetes, high blood pressure and high cholesterol). Irin wadannan matsalolin zagayawar jini a jiki da danginsu (blood circulatory problems) sune matsoli na farko masu haddasa rashin karfin mazakutar namiji ga mutane da dama.

2. Ciwon daji (cancer) na iya yima jijiyoyin jini ko hanyoyin sadarwar kwalwa illa, wanda wadannan hanyoyi suke taimakawa wajen mikewar gaba kamar yanda muka yi bayani a 
baya.

3. Hadari (accident) wanda ka iya shafar sashen al’aura ko wani bangaren kwalwa mai taimakawa wajen mikewar al’aura.

4. Yawan damuwa akan matsalolinda suka faru da mutum na rayuwa da kadaici (depression).

5. Shan sigari (smoking). Taba ko sigari na cunkushe hanyoyin jini. Tana iya sanya karancin zuwan jini ga al’aura, daga nan sai asamu rashin karfin gaba. 

6. Shan giya da kwayoyi (alcoholism and drugs). Matsalar yawan shan-giya na iya haddasa rashin karfin namiji koda kau mutum bai sha giyarba lokacin jima’i, domin kuwa tana zama cikin jini. Haka kuma, shaye-shayen kwayoyi don maye da wasu nau’in kwayoyi da akeba mararsa lafiya a asibiti (their side effects), kamar kwayoyin maganin ciwon daji (anti-cancer medications).

7. Rashin kwanciyar hankali ko fargaba yayin jima’i (anxiety). Idan mutum yana tunanin cewa bazai iya biyama iyalinsa bukatar jima’i ba (misali sabuwar amaryarsa ) saboda wata matsala da yake fargaba, ko kuma yana tunanin cewa baya gamsar dasu, toh yana iya jefa kansa cikin wani halin fargaba da zaisa ya rasa karfin gaba lokacin saduwa.

8. Karancin sha’awa wanda kai tsaye nada alaka da rashin cikakkiyar lafiyar mutum.

9. Karancin sha’awar saduwa da wata macen cikin matan maigida. Hakan na faruwa idan matar batasan yanda zata jawo hankalin maigidan taba wajen kwanciya. Wannan dalili na haddasa matsalar rashin karfi. Wasu dalilan kuma nada alaka da maigidan kan bukatarsa. Shiyasa wasu mazajen ke kara aure.

10. Yawan Kiba (obesity) na hana maza karfin mazakuta, kuzari da kuma haddasa kankancewar al’aura. Da sauransu.

Idan aka samu daya daga cikin wadannan alamomin a garzaya asibiti dan Neman shawar wari
Allah yakara mana lfy ameen
Kabir Yusuf Danwurin Dutsi

Post a Comment

0 Comments