CIWON YA'TSA [KARKARE]




🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉🎉

Ciwon karkare wanda da turanci akan Kira da (whitlow) yana daya daga cikin cututtukan dakan shafi fata (skin) da kwayoyin cutar birus (herpes simplex virus) ke kawowa, Kuma yana daya daga cikin wadanda ke addabar mutane da dama a cikin al’umma. 

Wasu da Kän hadu da ciwon sukan kwatanta shi da ciwo irin wanda basu ta6a ji ba a rayuwarsu sabda azabar zogi, zafi, hana sukuni, tare da hana bacci musamman in dare yayi, awasu ma da abun yai tsanani zaka samesu suna sumbatu su kadai suna surutai batare da sun San sunayi ba. Kai a wasu ma cikin dare sukan bude kofa su fita batare da sun San ina zasu ba. Hakika ciwon hannu, kunne, da hakori wadannan larurori mizaninsu daban ne acikin ma'aunin zogi na likita (pain scale).
       
Kamar yadda na fada kwayoyin cutane na herpes simplex virus ke shiga tsakankanin "FATA da FARCE" a dan yatsa sai a samu ciwo da kumburi awajen. Inda daga bisani sai aga gurin nacigaba da Mamaya yana kara girma domin virus yana da wuyar sha'ani cikin kankanin lokaci yakan hayayyafa.

Akan samu wanda BACTERIA kan kawo, akan kuma samu wanda kwayar FUNGUS kan kawo, Amma wanda kwayar VIRUS kan Jawo yafi yawa ya kuma Fi wahalar sha'ani domin duk abunda yake virus bai cika Jin magani ba, sai andage! Babban misali Kwayar HIV dakan zama AIDS kunga duk da magungunan amma basa iya kashe Kwayar baki daya. 

Saide wani mahimmin abu shine yawanci mutanen da wannan Kän kama sukan kasance suna da matsala ta wannan kwayoyin virus daga farjin su walau mata ko Maza wato (Genital herpes) da akan ga kurji mai ruwa agefen farji ko azzakrin mutum, toh a yayin matse irin wannan kurjin ne in ruwan ya taba Yatsa kuma ba'a lura anyi gaggawar wankewa ba aka kai hannun baki sai asami kuma dayan da ake Kira (Oral herpes) aga kurji ajikin le6e mai ciwon gaske har yake hana cin abinci cikin dadin rai, ana haka nan ma sai ruwan ciwon ya samu shiga tsakanin fata da farce shikenan sai afara Jin kai kayi sai ai developing karkare.

Wasu kanyi kunshi susa lalle da taki ahannun da ciwon ya kama AMMA a likitance banda cikakkiyar masaniya ko shafa lallen yana kashe wata kwayar cutar a cikin kwayoyin dana lissafa a sama, saide duba da yadda lalle Kän tattare fata ya rage saurin Jin ta6i, kila ace ko zafi yake ragewa da sanya rurucewar da wajan yayi tai saurin warkewa.

Haka sauran nau'in ma dana ce kwayoyin bacteria dana fungus Kän jawo; Yafi kama mutanen da basu da yawan tsabtace hannunsu ta hanyar wankewa da sabulu a kai-a kai, da kuma mutane masu yawan cin yatsa, ko cire farce da hakori domin kwayoyin cutar bakinsu suke sawa a wurin na daga ragowar irin abincin da ya mammakale a hakori basui brush ba yakan sa su hayayyafa su kawo karkare.     
                      

ALAMOMIN CIWON

1- Dan yatsan da abin ya faru kan fara kaikayi, sannan ya d'ad'e ya kuma duri ruwa ya kumbura ya fara zafi ko zogi sosai. 

2- Akan samu kaluluwa a hammatar hannun da abin ya faru. 

3- Wani lokaci kuma ciwon na zuwa da zazzabi.
           
4- Sannan ciwon yakan hana samun nutsuwa tare da isashshen bacci.

HANYOYIN KARIYA

1- Ga masu fama da kurajen gaba ya kamata namiji ko mace sui kokari su nemi magani don Kare afkuwar wannan ciwon.

2- Haka ba iya masu kuraje ba har masu fuskantar matsalar fitar ruwa (discharge) daga farjin su; Maza da matan suma su nemi magani domin irin wannan infection din na farji ba karkare ba har haihuwa yakan iya hanawa, kaga kenan wajibi ne anemi magani.

3- idan ansami yanka ahannu akula da shi aje chemist ko pharmacy ba lallai sai asibiti a wanke wajen da sinadaran kashe kwayoyin cuta domin in iska mai Qura ta bude hannun ana iya samun wannan ciwon

4- Masu yawan cin yatsa ko farce dole ne su daina saboda suna cikin hadarin kamuwa da wannan ciwo.

5- Sai kuma jaddada yawan wanke hannaye da sabulu a kowanne lokaci.

6- Da ciwon ya fara ya kamata mutum yaje asibiti inda za'a duba agane kowacce kwayar cuta ce ake ganin ta kawo shi, sa’annan a bada maganin kashe zogi dana kashe kwayoyin cutar da suka kawo ciwon. 

7- Idan kuma wurin ya riga da ya kumbura ya duri ruwa, dole aje acire ruwan da ya taru kafin abada magunguna. Idan ba'a cire ruwan ba yakan dau lokaci yana zogi. 

8- Idan abun ya faru ba matsala bane ake dund'uma ruwan dumi asa gishiri ciki ake tsoma yatsan sau 3 zuwa 4 a rana, shima yana taimakawa wajan saurin waraka.

Idan koh aka fidda ruwan, nan da nan yake bushewa.
MU YINI LAFIYA

[Ibrahim Y. Yusuf]

Post a Comment

0 Comments