๐‡๐€๐๐˜๐Ž๐˜๐ˆ๐ ๐ƒ๐€ ๐™๐€๐Œ๐” ๐“๐€๐Š๐€๐ˆ๐“๐€ ๐˜๐€๐–๐€๐ˆ๐“๐€๐‘ ๐Œ๐€๐‚๐„-๐Œ๐€๐‚๐„ ๐ƒ๐€๐‹๐ˆ๐‹๐ˆ๐ ๐‡๐€๐“๐’๐€๐‘๐ˆ๐ ๐€๐๐€๐๐„๐ ๐‡๐€๐–๐€:


________________________________________

Hatsarin ababen Hawa "๐•๐ž๐ก๐ข๐œ๐ฎ๐ฅ๐š๐ซ ๐‚๐ซ๐š๐ฌ๐ก" na daga cikin manyan iftila'oin sahun gaba-gaba na 1 zuwa 10 da sukai shura wajen kashe al'umma a Nigeria [Vehicular crash is amongst the top 10 cause of death in Nigeria].

A fadin duniya duk shekara muna rasa sama mutum milyan 1 da rabi dalilin hatsari, wanda munsan sunfi haka don wasu ko labarin faruwarsu baji ake ba, kuma galibi sunfi faruwa ne a irin kasashen mu masu tasowa, wanda wasu daga cikin wadannan mace-macen sau tari abune da zamu iya kauce musu domin kurakuran mu ke jawosu. 

Munsan idan kwana ya kare baka da dabara to amma akwai sababi, domin wasu mace-macen sakaci da ganganci kan jawosu kusa, kafin lokacin da ya kamata su auku ba.

________________________________________

Haka kuma koda bama tsoron mutuwa toh ai wahala abar tsoro ce, ga azabar fitar rai ga kuma ta buguwa ai masifar taima jiki yawa tunda shi jikin dan Adam akwai iya adadin abunda zai iya karfa na karfi wato Force wanda inya karbi fiye da haka sakamakon shine samun nakasa ko mutuwa.

Ganganci ba naka bane matsayinka na wanda ke kan karfe atsakiyar iska, kai ba'a sama ba, kai ba'a kasa ba, kuma kasan milyoyi sun mutu ta wannan hanya akan me zaka sa rayuwarka cikin garari data wadanda kake dauke dasu don nrman suna ko burga? 

Shiyasa Allah ya horema dan adam hankali, ilimi, hikima da basira domin rarrabe abubuwa tare da kaucema wadanda yasan zasu cutar da rayuwarsa.

Wajibi sai mun hada hannu da karfe kafin muga raguwar Mace-macen nan inba haka ba tohfa somawa akai wahala da jimami nagaba... 

Haka dole muji cewa muna da rawar takawa kada kurum don kana cikin mota matsayin fasinja ko aboki ka lamince cewa direbane keda ikon yin komi, A'ah kaima kana da hakkin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna wato abunda yake alkhairi in anbisa an kuma kiyaye.

--------------------------------------------‐----------------------

Saboda hatsari ba kurum a Mutuwa bane tashin hankalinsa yake, Yana da wani karin Negative effect din acikin mu.... domin ko ahaka kuka duba adadin popilation na รฝaya Mata ya ninka na รฝaรฝa Maza...., Matan nan ko duk wacce ta girma ta zama baliga tana da bukatar namiji a rayuwarta, toh gashi kuma Mazaje ne kaso 84% cikin dari na wanda ke mutuwa dalilin hatsari, Sannan Matayen auren na gaba da Mazajensu su qaro aure koda kuwa sunsan mazajen nasu adalai ne... 

Toh kunga ta wani bangaren hatsarurruka na taimakawa karuwar zinace-zinace cikin al'umma ta dalilin samar da karancin Maza.

Haka zalika masu auren cikin Maza dakan mutu a hatsari; shin mukanyi tunanin ko ya rayuwar iyalansu zata kasance bayan mutuwarsu? Ya ilimin รฝaรฝansu da tarbiyarsu? Inma ba masu aure bane wasu suke tallafawa iyayensu wadanda karfinsu ko lafiyar jikinsu tai rauni.... Kunga nan masifa ce babba ashe mamamtan da yawa. Don haka wajibi ne mui kokari mu shawo kan hakan mu dena mutuwa kamar kaji.

--------------------------------------------‐----------------------

๐Š๐š๐ข ๐ญ๐ฌ๐š๐ฒ๐ž ๐ก๐š๐ง๐ฒ๐จ๐ฒ๐ข๐ง ๐๐š ๐ณ๐š๐ฆ๐ฎ ๐›๐ข ๐ฌ๐ฎ๐ง ๐ก๐š๐๐š ๐๐š;

1. ๐‘๐€๐’๐‡๐ˆ๐ ๐Š๐˜๐€๐–๐”๐ ๐“๐ˆ๐“๐”๐๐€

Wannan abune da dayawa cikin mutane ke bad uzuri dashi; Hakika rashin kyawun hanya babbar matsalace, toh saide mun tsinci kanmu a kasar da koken mutane baida wani tasiri sosai ta wannan fuskar don haka mune ya kamata mu nemi mafita. 

Mafitar ko itace; kowacce irin hanya da yadda ya kamata abita, don haka kafin ka zari tafiya koda baka ta6a bin hanya ba ya kamata ka nemi wadanda suka san hanyar suima bayanin abubuwan data kunsa. Idan kuma kasan hanyar toh wajibi kai hakuri ka bita da halinta shine kurum karshen gatan da zakaima kanka, iyalinka, abokanka da kuma fasinjojinka. 

Banda daka ta sauran direbobi kuna tsere kuskure ne... sannan idan kana gudu kaga rami kada kace zaka kauce nan da nan ko ka taka birki kurum tunda ka kure mmasaka bari ka fada ka wuce, inba haka ba kana iya kada motar kuma ka kada me biye dakai.

Muna kuma fatan shugabannin da nauyin ke kansu zasuji tsoron Allah su dubi rasa rayukan da ake su kawo dauki.

--------------------------------------------‐----------------------

2. ๐˜๐€๐–๐€๐ˆ๐“๐€๐‘ ๐Š๐€๐๐€๐๐”๐ ๐Œ๐Ž๐“๐Ž๐‚๐ˆ ๐Œ๐€๐‹๐‹๐€๐Š๐ˆ๐ ๐Š๐€๐ˆ 

Yawaitar ๐ฉ๐ซ๐ข๐ฏ๐š๐ญ๐ž ๐œ๐š๐ซ'๐ฌ shine abu na biyu wajen tasirin yawaitar hatsarurruka akan hanya. A iya cewa arziki ne, kuma cigaba toh amma akwai tashi matsalar, domin bamu da tsari a irin tamu kasar, An iya tanadin mota amma babu tanadin gurin parking dinta me kyau, sannan da yawa sun dauketa showman ship kurum don burga bama don biyan bukatar kai ba shyasa kowanne shirme kana iya gani kan titi, in gwamnati tasa doka ace antsanantawa al'umma ana kame ammafa akwai abunda dole mu kalli amfaninsa komi kinka da gwamnati.

Domin kasashen da akaci gaba babban matakin da suka dauka shine assasa MASS TRANSIT, da wannan suka kere kowa wajen karancin yawan hatsarurruka, domin hatta cikin gari unguwa zuwa unguwa akwai motocin Mass transit da kowacce ada inda ta dosa arubuce gabanta, in inda zaka zatai ka tsayar ka shiga baruwan wani dakai, babu wanda ma ya damu dame kudine kai ko talaka, zaka shiga in anje inda zaka sauka ka sauka, cikin farashi me sauki. Babu bukatar cushe tituna da kananun motoci private cars, kuma LINES ne kowanne ga layinsa, me babbar mota layinsu daban, masu taxi daban, ma'aikata masu private layinsu daban cikin tsari, babu wanda don yaga space a layin da banasa ba zaice zai sauya hannu kamar yadda muke yi a Nigeria.

Wannan na daga tsarin da yasa ake ganin shugaban kasar koriya ta Arewa kamar zallan zalunci ya iya amma kuma ba haka bane wajen transport kowaye kai baka isa ka mallaki motar hawa ba ka tukata duk yadda kakeso sai wanda yakai ya kawo a kasar wanda suke da manyan harkokin kasuwanci da kkasake amfana dasu, majority duk public transport suke amfani dashi.

Kai kadai ko a Nigeria ka tara motocin hawa 5 ko 10 naka dana yayanka da matarka. Ba dole gur6atar yanayi ya yawaita ba. Mass transit bus daya๐Ÿš tana dibar mutanen da in a private cars ne sai ansami motoci 70 jere... kunga ai cunkoso da yawaitar hatsari dole ne Ko. 

Don haka da ace muna kasa wacce gwamnatoci suka damu da inganta rayuwar mu toh da mafita shine ayi doka da tsari ta yadda zamu riki manyan motocin mass transit musamman acikin gari dama tafiyar nesa bisa farshin da hatta mai motar kansa sai yai kwadayin saukin ya bar motarsa... domin zaka samu motace harda na'urar sanyaya daki ciki ba gumi ba hayaniya, tafiya bisa kyakkyawan yanayi, ga kuma jiragen kasa na zamani, suma farashi me sauki duk zasu taimaka.

Amma de duk da haka tunda bamu da irin wancan tsarin hanyoyin da masu private cars zasu bi su taimaka wajen takaita yawaitar hatsarurruka shine; Sanyawa zuciya hakuri, da dena son nuna mota ta taci taka ahanya, gami da koyon parking me kyau, da dena shiga overtaking kurum don kanaji da lafiyayyar mota. 

Haka zalika dena sakarwa yara masu karancin hankali motoci koda kuwa sunkai ko sun wuce shekaru 18, domin kaiwa shekarun tukin basu bane; Kaifin hankalin sarrafa karfen shine, domin maganar gaskiya namiji dan shekara 21 ma Mace me shekaru 18 tafisa hankali galibi, don haka sai Namiji yai shekaru 21 aduniya yake hada hankali da Mace yar 18 ke dashi, kunga sakarwa mutum mota don yai 18years gaskiya inbai da nutsuwa matsalane, amma inda nutsuwa dan 17 ma yafi wani me shekara 30 din tuki me kyau. Hatta hukumomi masu bada shedar tuki ya kamata suke binkicen lafiyar mutane kafin basu lasisin. Inde mukai haka muka kiyaye zamuga canji.

Domin galibi matasa ne zaka samu marasa hakurin da in anwuce a titi suma suce sai sun rama, shiyasa yan shekara 15 zuwa 39 ne suka fi mutuwa a hatsari.

--------------------------------------------‐----------------------

3- ๐Š๐€๐‘๐€๐๐‚๐ˆ๐ ๐๐€๐‚๐‚๐ˆ ๐ƒ๐€ ๐’๐‡๐€๐ ๐Œ๐€๐†๐”๐๐†๐”๐๐€

Ya dace duk direba yake tuna cewa haฤama batasa kasami rabon da banaka ba, musamman direbobi masu tafiyar nesa. Akwai ganganci mutum yake hawa karfe alhalin yasan yana cike da karancin bacci. Ita kwakwalwa tana bukatar hutu, inkuwa kace bazaka barta ta huta ba toh karshen abun shine kaika ga halaka. 

Wajibi aguji shan jike-jike ko magungunan asibitin nan domin kasancewa a farke don tuki, domin akwai tashin hankali ace kuna mota atafe amma direba na gyangyadi, kafin ka ankara sai kaji kwaram kurum. Shiyasa zaka direba ya baro jihohin kudanci lafiya amma saida yazo arewa ana ganin yazo gida kurum sai kaji accident saboda rashin bacci, yazo ya kashe muna mutanen mu na arewa da basuji basu gani ba da mota dalilin sakacinsa.

--------------------------------------------‐----------------------

4- ๐…๐€๐’๐ˆ๐๐‰๐€ ๐˜๐€ ๐…๐ˆ๐…๐ˆ๐“๐€ ๐’๐€๐”๐Š๐€ ๐‹๐€๐…๐ˆ๐˜๐€ ๐€๐Š๐€๐ ๐†๐€๐†๐†๐€๐–๐€

Yana daga rawar da zamu taka dena ingiza direbobi suna tukin ganganci, taya kai da hankalinka kasani cewa wannan direban har zancensa ake yafiye tukin ganganci da gudu amma ka zabi motarsa saboda kurum kanaso kaje gida akan kari ko wani uzuri. 

Hakika ya kamata mui hankali mu lura da yanayin direba dakyau, kana ganin idanun me shaye-shaye kasani, domin shaye-shaye baya buya, wani direban ma rangaji zakaga yanayi kuma ya shiga mota, wai kuma ahakan kana gani ka yadda ka zauna kace Allah zai kiyaye bayan ya baja hankali kaga matsala da idonka.... Aiko baza abiyani kudina ba na fita. 

Haka intafiyace ta daurin aure idan kaga motar da dattawa ke shiga inda guri shiga, kyale samarin nan inde kasan direban baijin magana, aje lafiya adawo lafiya shine tafiya. Inko tsautsayi yasa duk sai cikin matasa toh inkaga ana tafiyar ganganci ka tsawatar, in anki ji kace atsaya ka sauka... karka ta6ajin kunya! Rai guda dayane inkuma ka rasa toh ka rasa.

--------------------------------------------‐----------------------

5- ๐€๐Œ๐…๐€๐๐ˆ ๐ƒ๐€ ๐–๐€๐˜๐€ ๐Š๐Ž ๐Š๐”๐๐๐€ ๐‘๐€๐ƒ๐ˆ๐Ž

Amfani da wayar salula a halin tuki na daga sahun gaba na abunda ke jawo hatsari shima wato daga waya tsaka da tuki. Direba ka sani magana kwata-kwata bataka bace inka riki sitiyari. Anaso ka nutsu ka rika kallon titi tare da scanning din inda motar zata isa adukkan sekonni 10 zuwa 12, wato ka rika hangen nesa walau rami ko wata alama don gudun hatsari. Ba'ason raba hankali

Inma ta kama dole saika amsa wayar saboda mahimmancinta yayin tuki toh kaima Allah, kaima Annabi ka dawo shelder ka tsaya kai parking agefen hanya inka gama saika cigaba da tafiya. Kada ka kuskura ka raina tsayin maganar da zakui yayin tuki.

Haka zalika sanya waya a HANDS-FREE wannan ma ba mafita bane, domin kara raba hankali da nutsuwarka yake, cikar hankali da basira shine ka tsaya kai parking. Inda hali ma rufe wayarka inzakai tuki har sai kaje ka tsaya a inda zaka.

Haka zalika kunna radio da canjin waka alura sosai, yayin da zakayi ka dawo hannun gefen titi sannan ka rage gudu kuma ya zamto hannunka daya na rike da sitiyari sosai kuma kana kallon titi.

--------------------------------------------‐----------------------

6- ๐ˆ๐‹๐Œ๐€๐๐“๐€๐‘ ๐ƒ๐€ ๐ƒ๐ˆ๐‘๐„๐๐Ž๐๐ˆ

Wajibin hukuma ta tsaya ta lura da cewa lallai kwararun masana tuki akeba lasisi, cin hanci masifa ne, rashin kiyaye wannan ka'idar ke saka rayukan bayin Alkah cikin hatsari.... domin yana daga matakin nasarar rage hatsura ya zamto dukkan direbobi sunsan alamomin titi da hakkin rai acikin kowanne addini da direba yai imani dashi.

Haka na. sanya manhajjar ilimin tuki cikin syllabus din koyar da tuki da ka'idojin titi tun daga matakin karatun firamare ko karamar sakandire abune da dace, hakan zai taimaka yasa yara su taso da ilimin abun hawa sosai tun suna kanana, musamman aguraren da alamomi ke nuni da alamar hatsari, ketarowar dabbobi wato animal crossing sign, ko alamar dake nuna kwai kwana agaba, ko akwai makaranta, ko hanya ta karkace da sauransu.

--------------------------------------------‐----------------------

7- ๐‹๐”๐‘๐€ ๐ƒ๐€ ๐‹๐€๐…๐ˆ๐˜๐€๐‘ ๐“๐€๐˜๐Ž๐˜๐ˆ ๐ƒ๐€ ๐Š๐”๐™๐€๐‘๐ˆ๐ ๐Œ๐Ž๐“๐€

Ya kamata akewa mota service akai akai, Hakanan inda akece enjin oil ake sawa karka nuna son kudi kaqi sa me kyau, wannan ba dabara bace kashe kaine, Sannan wajen birki/giyar mota mai makon man AZ't da ake sawa wasu ance Omo suke kadawa da ruwa suke zubawa agurin fisabillillahi ai wannan ba adalci bane, shyasa galibi masu irin wannan zakaga direbobin motocin cikin gari ne da masu Tifa... 

Shiyasa suke distracting tare da kashe mutane baji bagani idan birki yaki ci, ko kuma su zo su gwabzama kana tsaye haka kurum, don haka ya kamata hukumomi kada su sassautawa duk wanda aka samu da irin wannan laifin, domin tausaya masa jefa rayuka cin hatsari ne, muji tsoron Allah mu kauda ha'inci mui abunda ya dace, Motarka batakai ran mutum ba.

Sannan ka sani direba kowacce mota akwai iya adadin gudun da zata iyayi, kuma hakan ya danganta da lafiyarta, kasani kamar yadda a mutane wani yafi wani kaima dole ne akwai wanda sai ya wuceka a titi, kuma kaima saika wuce wani saboda kirar motocin ba daya bane. Sani da yarda da wannan zaisa mu dena cusa kanmu ahalaka.

Hakanan dukkan tayar mota na expiring bayan shekara hudu (Every tyres expires after 4 years of manufacturing). Ita ko wannan expire na faruwane walau anyi amfani da tayar ajikin mota koda kuma ba aiba. Kaga idan kasan tayoyinka sun tsufa haramun nema kai gudun wuce sa'a da jama'a koda daidai da yadda wannan motar taka zata iyane ballantana tsere da wacce tafita. 

Karka rudu da sabuwar taya kasaka wani lokacin sabuwar expire ce ko dab da expire, saboda andade da yinta saida ta kusa expire akai cinikinta. 

Duk tayar Mota akwai expiring date dinta saide ba 6aro-6aro ake rubutashi ba cikin hikima ne da kana bukatar masaniya kafin ka iya ganewa: 

MISALI: Duk taya akwai lambobi kamar kanana kamar haka 2024, 3005, 5122, 1002 da sauransu. 

Abunda hakan ke nuni shine manufacturing date ne na tayar walau ta mota ko ta mashin, don haka lisaafin iri biyu ne; wasu nasa manufacturing date kurum wasu kuma Expiring amma duk zaka iya tantancewa, kaide kurum ka rike taya na expire duk bayan shekara 4:

๐Œ๐ข๐ฌ๐š๐ฅ๐ข; inkaga ansa 1017, wannan "10" din sunan wata da ranar da akayita ne, kunga watan goma ya kama OCTOBER (Anyita 10 ga watan october), yayin da "17" yake matsayin shekarar wato 2017 kenan. To kaga kenan dole zai zamto wannan tayar daga November abunda yai sama zuwa 2018 ds za'a sameta tunda a october ne. Kaga daga 2017 zuwa yau JUNE 2021 kaga kusan 4 years kenan. Idan kaje ka kwaso wannan tayar ayanzu JUNE, JULY, AUGUST, SEPT, OCT Kaga saura wata 4 tai expire don haka ka kwaso gwari.

To da kuma numbar 4425 kagani to anan kuma kaga ai ba wata me "44" toh anan hakan na nuna ba manufacturing date suka sa ba, Expiring date ne. Lamba 44 na nufin sati na 44 acikin shekara, yayin da 25 ske nufin 2025. Toh kaga tunda sati 52 ke shekara guda kaga akalla ana nunama karshen SEPTEMBER 2025 wannan tayar zatai expire.

Don haka mu lura sanin hakan da kiyayewa zai takaita yawaitar hatsari dalilin fashewar taya.

Sannan intaya ta fashe ka rike sitiyarin gam ayadda yake, kada ka taka birki ko kadan kada kuma kace zaka kashe motar kai tsaye ta hanyar cire makullin, ko kuwa kace zaka juya sitiyarin zuwa gefe kul dinka wannan ne ke kashe mutane saboda babu balance, don haka kurum ka nustu sosai ka kankame sitiyarin ahankali zakaji motar na rage gudu karka taka birki.

--------------------------------------------‐----------------------

8- ๐‹๐”๐‘๐€ ๐ƒ๐€ ๐‡๐€๐–๐€๐ ๐‰๐ˆ๐๐ˆ ๐ƒ๐€ ๐’๐”๐†๐€๐‘

Sau tari wani hatsarin kan afkune badon wata mota ko dabba ta gitta ba, Stroke kan sami direbobi tsaka da tuki musamman a mutane masu hawan jinin da basa kulawa. Wanda shayewar barin jikin kansa su rasa control wanda shine galibi kesa aga mota ta bar hannunta har ta ketara ta fadi awani hannun idan 2 way ne titin ko kuwa tai cikin gonaki. 

Wani kuma hawan jini dama ya hadu da ciwon sugar wato diabetes dukkan wadannan idan stress level yai high komi na iya faruwa inba abasu kulawa, shyasa nasha fada sau tari don kana da wannan larurar baka sani, saboda ba ajin wasu alamu tsawon lokaci sai abu ya baci. 

Ko kuma ma kasan kana da ciwon sugar amma kurum shan magani kake babu lissafi, idan sugar din tai low toh nan ma kana iyayin accidents. Dole yayin neman kudi muke kula da lafiyar mu muma, kada mu shagala. Yara kanana yanzu ana samunsu da wadannan larurori don haka shekaru basune ba, walau iyayenka nada su ko babu duk kana iya haduwa dasu ba gadonsu kurum ake ba.

Kana iya sayen abun awon jini hatta ahanya kai parking ka rika dubawa, ko agida kafin kanfita. Lallai mui hankali da hawan jini matasa Mata da Maza ba wasa bane.

--------------------------------------------‐----------------------

10- ๐Œ๐€๐’๐” ๐‹๐€๐‘๐”๐‘๐€๐‘ ๐ˆ๐ƒ๐€๐๐” ๐Š๐”๐†๐€ ๐‹๐ˆ๐Š๐ˆ๐“๐€

Akwai masu larurar makantar dare wato Xeropthalmia da zarar magariba tayi basa gani sosai, gaskiya bai kamata mai irin wannan matsalar yai tukin dare ba matukar yana da tsoron Allah, kada kudi ko yaushe su zamo abun hange ga direba maimakon lafiya, ya kuma zama wajibi mutum yaje yaga likita tunda ana iya maganceta.

Wata matsalar ganin kuma ciwon suga ne har ya fara ta6a idanu wanda inba ai komi ba mutum ma zai makance baki daya. Haka zalika wanda yake da larurar karfin gani hatta da rana ya kamata ko yaushe ya kasance sanye da gilashinsa na qara karfin gani hakan shine abunda ya dace. Hakanan asan irin adon da za'akewa cikin mota domin wani design din na daukar ido ko kashe ido da jawo hatsari.

--------------------------------------------‐----------------------

12- ๐Œ๐Ž๐“๐’๐€ ๐‰๐ˆ๐Š๐ˆ ๐“๐€๐‘๐„ ๐ƒ๐€ ๐€๐Œ๐…๐€๐๐ˆ ๐ƒ๐€ ๐’๐ˆ๐“ ๐๐„๐‹๐“

Motsa yana da tarin amfani, zai taimakawa guiwoyinmu su zamo flexible tare da samun sauki yayin mummunan hatsari, domin mafi yawan sashin da yafi samun matsala shine; Daga kugu zuwa kafa wato karayar kafafuwa da kuma buguwar kai wato taruwar jini a kwakwalwa sune ke kashe mutane ahatsari. 

Bawai kirji bane kamar yadda mukanyi tunanin zuciya! Domin wani karayarsa ta ciki ce, wani kkumaya karye hadda jini wato compound fracture hakan ya huda jijiyar jini yayin da 6argo yabi cikin jijiyar ya tafi zuciya ya shiga huhu ya sarqe numfashinsa ya kashesa (pulmonary embolism).

Wani kuma kai tsaye kansa ya bugu ba asani ba, ya sami abunda ake kira epidural hematoma, ko subarchnoid hemorrhage jini ya wanke kwakwalwarsa, ko ya taru agefe ta ciki yai sanadiyyar kashesa... Amma kuma ta waje kila ku gansa garau babu ko kujewa amma ya mutu. Wannan tasa wanda aka samesa da rai kukaji yana kukan kansa na ciwo bayan hatsari inde bai sami kulawa ba cikin minti 60 shima zai iya mutuwa, dole abude kokan kansa a zuqe jinin, shyasa wasu sai a asibiti sukk karasa mutuwa, kila ga asibitin anzo amma ba kayan aiki.

Sanya sit belt hakan na taimakawa hatta ga gadon bayan mutum, domin wasu sukan zamo araye amma lakarsu ta sami matsala su da takawa har abada kullum saide ajuyasu, don haka wajibi mu lura da kanmu.

--------------------------------------------‐----------------------

13- ๐‹๐”๐‘๐€ ๐˜๐€๐˜๐ˆ๐ ๐๐€๐ƒ๐€ ๐‡๐€๐๐๐” ๐€ ๐ƒ๐€๐๐†๐„๐‘

Mu sani bawani wanda yake titi nasa ne shi kadai, don haka ake hakurin bada hannu, sannan in anbada hannu karkai saurin tashi, ka kirga 1-2-3 ana hudu saika daga. Karka damu da hayaniyar na bayanka in agaba kake, iya abunda zasu iya kenan haushi. Akuma rika duba mirror kafin bude kofa in mota ta mutu cikin traffic saboda masu babur kada ka kayar da wasu kasa rayuwarsu a hatsari sakamakon bude kofa daka.

--------------------------------------------‐----------------------

14- ๐’๐€๐Œ๐”๐ ๐“๐‘๐€๐ˆ๐๐ˆ๐๐† ๐†๐€๐Œ๐„ ๐ƒ๐€ ๐€๐†๐€๐‰๐ˆ๐ ๐†๐€๐†๐†๐€๐–๐€

Yawanci mutane basusan ya ake bada agajin gaggawa ba inhatsari ya faru, babu lokaci mafi mahimmimci wajen samun taimako kamar mintuna sittin na farko bayan faruwar hatsari daga nan in aka rasa dauki mutuwa ke yawaita.

Galibi ba danna kirji ko hura numfashi wato resuscitation bane, dole saika koya kasan adadin yadda zakai tsakanin babba da yaro, da kuma gurin da ya dace ka danna din, Ya dace Matasa suje kungiyoyi na hukumar RED CROSS domin su sami training saboda bada agaji koda wataran kana tafiya kun riski hatsari ahanya ta yadda zaki iya rescuing succesfully. Saboda hatta wa ya dace afara ceto atsare abun yake, sannan yyadd ake zaqulo mutum acikin mota shima a ilmance yake, bawai kurum a fitar dashi bba a'a a tabbatar ya fita babu mummunar illa domin wajen cirowar nan akan tsinkawa mutane laka. 

Hakama bada fifiko wajen bada agaji kwai tsari

--------------------------------------------‐----------------------

๐Œ๐ˆ๐’๐€๐‹๐ˆ; Kazo ka riski anyi hatsari can ga yaro ko yarinya karama da ciwo ahannu amma ko numfashi bata yi, Can kuma ga mace me juna biyu maqale tsakanin kujera itama ba alamun numfashi duk da tana da rai, daya bangaren kuma ga namiji da rauni ahannu amma shi yana numfashi saide sama-sama ne! WA ZAKA FARA CETA CIKINSU....?

Hmm, da yawa kila suce me juna biyu, ko yarinya karama da bata iya numfashi... Amma azahiri wannan namijin me numfashi sama-sama shine ya dace ka fara ceta, su saura already a critical stage suke ba abunda zaka iya musu domin inka kuskura ka kyale mai numfashi sama-sama kana ganin kamar lafiya ne kafin ka gamo da sauran shima ya galabaita ya mace! Kaga anyi 3:0 wato biyu-biyu kenan, sakin na hannu kamun naguje. 

Don haka ko yaushe me dama-dama ake fara baiwa agajin gaggawa, sannan me bimasa atsanani, sannan mafi tsanani. Wancan da baya numfashi koda kaji alamun pulse cewa da ransa karka 6ata lokaci kansa ka fara ceto mai numfashi tukun shine guarantee. Haka in akwai mai zubda jini toh shi ya kamata afara taimaka atsaida jinin kafin kowa.

Dama de sauran abubuwan koyo... don haka adaure asami training din nan basai ma'aikacin lafiya ba, kowa na iya zuwa yai rejista ya sami training din cikin kwanaki 3 zuwa 4 ko sati 1.

15. ๐€๐ƒ๐ƒ๐”'๐€

Bayan dukkan matakai toh kuna sai afita gida da addu'a. Idan anfara ansawo kafar dama waje sai ace; Allahumma bil-kalimatullahi tammat wamin sharril makalaq.

Allah ya kara mana lafiya, yasa agama lafiya... Hatsarin abun hawa tun daga kan takalmi salifas har izuwa jirgin sama Allah ka tsaremu.
________________________________________

✍๐Ÿผ
[Ibrahim Y. Yusuf]

Post a Comment

0 Comments