ALWALA
Kafin mu yi bayani a kan alwala akwai abubuwa da za mu gabatar a matsayin sharar fage, kamar:
Falalar yin alwala.
Sharuɗɗan alwala.
Farillan alwala.
Sunnonin Alwala.
Butar alwala.
Abubuwan da wajibi ne a yi alwala kafin a yi su.
Abubuwan da an so a yi alwala kafin a yi su.
Abubuwan da suke warware alwala.
Yadda ake yin alwala.
Farillai da sunnonin alwala da abin qi a cikinta.
FALALAR ALWALA
Manzon Allah ﷺ ya ce, “Al'ummata za a kira ta a ranar Alqiyamah masu fararen qafafuwa da hannaye da adon goshi, saboda alwala.” Wanda ya sami iko daga cikinku, ya tsawaita gurrarsa (haske) to ya aikata.
Manzon Allah ﷺ ya ce, “Wanda ya yi alwala, ya kyautata to dukkan laifin da ya aikata, zai fita daga jikinsa har sai ya fice ta qarqarshin farcensa.”
Manzon Allah ﷺ ya ce, “Ku yi cak a kan daidai, amma ba za ku iya ba, ku sani mafi alherin ayyukanku shi ne sallah. Babu mai kiyaye alwala sai mumini.”
SHARAƊIN INGANCIN ALWALA
Alwala ba ta inganta har sai ta cika waɗannan sharuɗɗa:
Na daya: Niyya.
Na biyu jerantawa, misali ba a fara alwala ta ƙasa ko ta tsakiya dole a fara alwala yadda Annabi ﷺ ya koyar.
Na uku, yin Basmala (fadin Bismillahi) saboda hadisin da ya ce, “Babu alwala ga wanda bai fara da sunan Allah ba.” ()
* * * *
FARILLAN ALWALA
Abin da ake nufi da farilla shi ne, duk wani aiki da Shari'a ta wajabta ko ta tilasta yin sa. Idan an yi za a sami lada, idan ba a yi ba akwai zargi da alhaki.
Alwala ta zama farilla ga musulmi mai hankali kuma baligi, wato wanda alƙalamin Shari'a ya hau kansa.
Farillan alwala guda tara ne, dole a yi su a cikin alwala kafin ta zama ingatacciya.
1. Wanke fuska: Faɗinta ya fara daga kunne zuwa kunne, tsawonta daga goshi zuwa haɓa. Wajibi ne a wanke duk abin da yake tsakanin wannan wuri don kada a bar lam'a, a tabbatar ko`ina ya sami ruwa.
2. Kurkurar baki da shaƙa ruwa da facewa. Wasu malamai suna saka su a cikin sunnonin alwala, amma a gaskiya suna cikin farillai domin a cikin fuska suke wacce aka wajabta wanke ta, da kuma umarni da aka samu daga Annabi ﷺ cewa lallai ne a kula da aikata su. Ya ce, “Idan ɗayanku zai yi alwala lallai ya shaqa ruwa a hancinsa.”
A wani hadisin kuma ya ce, “Idan ɗayanku zai yi alwala ya tabbatar ya shaƙa ruwa a hancinsa.”
Wannan umarnin shi ne wasu malamai suka ɗauke shi a matsayin sunnah, wasu kuma daga cikin malaman suka ɗauke shi a matsayin wajibi.
3.Wanke hannaye zuwa gwiwar hannu, cikin hannu da wajensa. A kula sosai wajen wanke hannu kada abar lam'a domin hannu yana da ɓangarori da dama: tafin hannu, sangalalin hannu, gwiwar hannu, wanda a nan aka fi samun lam'a, ga kuma gaban hannu da bayansa. A wanke da kyau, a cuɗa, a tabbatar ko’ina ya sami ruwa.
4. Shafar kai: A wajen shafar kai a tabbatar da abubuwa guda huɗu:
Sanin farkon inda ake fara shafawa da ƙarshen inda ake tsayawa.
Sannan ya zama an sanya hannaye biyu.
Sai an tsoma hannu a cikin ruwa kafin a shafa a ka.
Shafa tana farawa daga farkon matsirar gashi zuwa ƙarshen ƙeya.
Idan akwai hula ko rawani a kan mutum, ko ɗan kwali ko hijab a kan mace, sai an cire shi sannan za a yi shafa, amma wanda akwai rawani a kansa kuma yana so zai yi shafa a kansa to yana da hali uku:
1.Yin shafa a kan rawani gaba daya.
2.Fara yin shafar a rabin kai a qarasa a kan rawani.
3.A cire rawanin a yi shafar a kai.
Duk wannan kalolin shafar, an ruwaito su daga Manzon Allah ﷺ.
5. Wanke qafa: Ita ƙafa tafi kowacce gaɓa wuyar sha'ani a wajen alwala, domin a nan aka fi samun kurakurai da kuma lam'a. Saboda akwai tafin ƙafa da ‘yanyatsun ƙafa da tudun ƙafa da idon ƙafa da dunduniya da agara da ƙarƙashin ‘yanyatsu. Ga shi kuma wani yana da kaushi, wani ko yana da faso a kafarsa. Don haka wanda zai wanke ƙafa duk sai ya lura da waɗannan ɓangarori, domin kada a bar wani wuri ba a wanke ba, ko a sami lam'a.
Manzon Allah ﷺ ya ce “Azaba ta tabbata ga wanda yake barin wuri a dunduniyar qafarsa wanda bai sami ruwa ba.”
Wannan yana faruwa ne idan mutum yana gaggawa ya gama alwala, ko kuma ya ƙi tara hankali da nutsuwa da kulawa a lokacin da yake gabatar da alwala.
6.Tsefe ‘yanyatsun ƙafa da na hannu a lokacin alwala domin kada a sami inda ruwa bai shiga ba.
A wajen wanke fuska idan mutum yana da gemu, mai kauri ko mai shara-shara, wajibi ya ɗebi ruwa da hannunsa ya tsoma wannan gemun nasa a ciki ya tsefe shi sosai har sai ya tabbatar cewa ruwa ya ratsa wannan gemun ya tarar da fatarsa.
Anas Ɗan Malik ya ruwaito hadisi ya ce, Manzon Allah ﷺ ya yi alwala sai ya ɗebo ruwa da tafin hannu ɗaya ya zuba ruwan a haɓarsa, ya cuɗanya gemunsa sai ya ce, “Yadda na yi haka Allah Ya umarce ni.”
7. Jerantawa tsakanin farillai: Abin da ake nufi a nan shi ne a yi alwala yadda aka koyar a jere kada a fara alwala ta ƙasa ko ta tsakiya, ko kuma a sami jinkiri tsakanin wata gaɓa da wata gaɓa. Idan an gama wani sai an dauki lokaci mai tsawo kafin a yi na gabansa. Misali, mutum ya fara wanke ƙafa kafin hannu, ko wanke hannu kafin fuska, ko ya fara alwala da shafar kai. Duk wanda ya yi haka da gangan ya saba, kuma alwala ba ta inganta ba.
Za muci gaba insha Allah.
Allah ya bamu ilmi mai amfani.
0 Comments