LADUBBAN SHIGA BANƊAKI:




Idan mutum yana da buƙatar shiga banɗaki, domin yin bawali, ko bayan gida, ya kula da sunnoni da ladubba da Shari'a ta koyar kamar haka:

1. Kada ya shiga banɗaki da wani abu mai ɗauke da sunan Allah ﷻ, sai idan yana gudun kada ya rasa abin, to sai ya nemi wani abu kamar jaka ya saka a ciki ya shiga da shi, domin abin da ake gudu shi ne kada wannan abin da yake ɗauke da sunan Allah ﷻ ya faɗa cikin najasa ko ya shafi najasa. Wajibi ne kuwa a girmama sunan Allah ﷻ.

2. Ya yi nisa ko ya shiga wani wuri mai nisa yadda ba za a jiyo wari ko ƙarar turosonsa ba. 

3. Ya yi bas’mala, ya yi addu'a lokacin shiga banɗaki a fili yadda zai ji a kunnansa. Sai ya ce: 
((بِسْمِ اللَّهِ، اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْخُبْثِ وَالْخَبائِث)) ()  
Ma’ana: “Ya Allah ina neman tsari daga sheɗanu maza da sheɗanu mata.” Kada ya bari najasa ta ɓata masa tufafinsa.

4. Kada ya kalli gabas ko ya bata baya, a lokacin yin fitsari ko bahaya , kamar yadda aka hana. Wasu malamai sun ce idan ba a fili ba ne ko sarari babu laifi, amma an fi so kada a kalli gabas ko a bata baya a ko'ina mutum yake, don girmama alƙiblar sallah.

5. Ya nisanci wurin da mutane suke zama, kan hanya ko wajen ruwa, domin an hana yin bahaya ko fitsari, a irin wannan wurin, kuma mutane suna la`antar wanda yake yin haka a waɗannan wurare.

6. Ya nemi wuri mai taushi yadda fitsari ba zai ɓata masa jiki ko tufafinsa ba.

7. Kada mutum yana yin bayan gida kuma yana magana, sai idan da wata buƙata ta yin maganar.

8. Ya shiga banɗaki da ƙafar hagu, kamar yadda yake shiga masallaci da ƙafar dama.

 9. Kada ya dinga yin fitsarin a cikin bahon da yake wanka domin yana jawo yawan waswasi da yaɗuwar cuta da ƙazanta. Ya fara yin fitsari a wajen yin fitsarin kafin ya fara wanka.

10. Kada ya goge bayan gida da kashin dabba ko ƙashi. Domin ba a yin tsarki da su, kuma bayan Shari'a ta hana akwai yiyuwar wataƙila hatsarin kamuwa da gubar da take jikin kashin ko ƙashin.

 11. Kada ya yi tsarki da hannun dama, domin duk wani abu mai daraja da dama ake yi.

12. Ya yi amfani da ruwa a wajen tsarki ya fi yin amfani da hoge ko (tissue) ko (toilet paper).

 13. Idan zai yi amfani da tissue ya goge sau uku.
 14. Kada ya dinga yin bawali a cikin ruwa da baya gudu.
 15. Idan an yi tusa ba a yi mata tsarki da ruwa, sai idan kashi ko zawayi ya biyo bayanta wanda ya zama wajibi a wanke.
 16. Yin tsarki wajibi ne: Idan mutum ya gama bayan gida amma ya ƙi yin tsarki ya yi saɓo kuma sallarsa tana cikin garari domin ya yi sallah da najasa a jikinsa kuma da ganganci.
 17. Idan yana da matsalar yawan kokwanto sai ya dinga yayyafa ruwa a gabansa, domin ya kore kokwanton cewa idan ya ji danshi ya san ruwan da ya zuba ne.
18. Ya wanke hannunsa da sabulu ko ƙasa idan ya gama tsarki kafin ya fito daga banɗakin.
19, Ya guji yin bawali a ruwa da baya gudana, da rami, da guri mai tiles, saboda tartsatsi ya fallatsa a jikin sa.
Yanzu zamani yazo har ana yin banɗaki mai TV, da radio, 
 . Ya yi addu'ar fitowa daga banɗaki ya ce: ((غُفْرَانَكَ)).” wato ina neman gafararKa ya Allah.
Allah shine masani.
Zamu ci gaba Insha Allah.

Post a Comment

0 Comments