Hukumar bada shawara akan bunkasa aiyukkan noma na Najeriya NIFAAS ta yi kira ga mutane da suyawaita shan nonon akuya saboda kara lafiyar jiki da yake yi.
Nonon Akuya ya fi na saniya amfani a jiki.
Amfanin da nonon akuya ke yi a jikin dan Adam:
1. Nonon akuya na dauke da sinadarin ‘Protein’ da ya fi na nonon Saniya. Yana taimaka wa jiki girma yadda ya kamata musammam ga yara masu tasowa.
2. Yana dauke da sinadarin ‘Amino Acids’ da ke kara garkuwan jikin mutum.
3. Yana dauke da ‘Vitamin A’ da ke kara karfin ido.
4. Yana dauke da ‘Potassium’ da ke kare mutum daga kamuwa da cutar shanyewar gefen jiki, kara karfin kashi, kare mutum daga kamuwa da cutar hawan jini da makamantan su.
5. Yana dauke da ‘Phosphorous’ wanda ke taimakawa wajen fitar da ababen da jiki ba ya bukata kamar zufa, fitsari da bayan gida.
6. Nonon akuya na da saurin nika abinci a cikin mutum.
7. Yana dauke da ‘Magnesium’ da ke taimakawa mutane dake fama da rashin barci.
8. Yana dauke da sinadarin ‘Manganese’ da ke kara karfin kashi.
0 Comments