🐐🐐🐐🐐🐐🐐🐐🐐🐐🐐🐐🐐🐐🐐🐐🐐🐐🐐🐐🐐🐐🐐🐐🐐
Akuya wacce muka sani a kasar Hausa, ana kiranta da Goat a harshen Ingilishi. Ta kasance daya daga cikin dabbobin da ake kiwo a sassa daban-daban a fadin duniya kama daga kasashen Afirka, kasashen Turai da na Larabawa.
Amfanin naman Akuya zai iya kasancewa daidai da na sauran dabbobin da ake ci, amma kuma amfanin nononsu ya bambanta.
Akwai dabbobin da ya kasance ana cin namansu amma kuma ba a shan nononsu, misali tunkiya. Ana cin naman tunkiya sai dai kuma ba a shan nononta.
Nonon tunkiya ba ya kasha wa ko da an sha sai dai kuma akwai wasu illoli na daban da yake haifarwa. Yana haddasa zafin ciki da taurin rai da kekashewar zuciya wanda ko kashe mutum za a yi to ba zai gudu ba kuma ba zai koka ba. Wannan ba ya rasa nasaba da dabi’un tunkiyar domin yana da wahala ka ga inda za a yanka tunkiya ka ji tana kuka, kuma komai wahalar da tasha ba za ka ji tana kara ba asali idan ba ka gani ba sai dai ka iske ta yi motsa a kan igiyarta.
Haka kuma kimiyya ba ta gano wani alfanun da ke tattare da shan nonon tunkiya ba, amma kuma ta zayyano dimbin amfanin nonon shanu dana awaki.
A lokacin manzon Allah (S.A.W) an ruwaito cewa fiyayyen halitta ya sha nonon akuya. Wannan nuni na musamman ga Musulmai cewa shan nonon akuya halal ne kuma baya cutarwa.
kofi daya na nonon Akuya na dauke da calories guda 168, Saturated fat kusan grms 6.5, grm 11 na carbohydrates, grm 10 na protein, milligrams 27 na good cholesterol, grams 11 na sugar, milligrams 12 na sodium.
Sai minerals din dake kumshe da nonon Akuya kamar haka : milligrams 327 na calcium, millilligrams 271 na phosphorus, milliligrams 342 na maganesium, sauran sun hada da copper da zinc da fluoride da niacin.
Sai bitamin A, bitamin B,bit B1,B2, bit.D, bit.B6, Folate, bit B12 Betaine.
Da wadannan sinadiran dake kumshe da nonon Akuya a fili yake, nonon Akuya ya dara na shanu amfani, duk da yake kitsen dake a cikin nonon Akuya ya dara na nonon saniya yawa, sai dai shi na nonon Akuya nan take yake narkewa ya bi jiki baya dakarewa sabanin na saniya dake daukar lokaci mai tsawo. Kuma na Akuya good cholesterol ne amma na saniya idan ya yi yawa to yana da illa.
Haka kuma ga masu fama da matsalar nan ta lactose intolerance wadanda shan madara kan kumberawa ciki to nonon Akuya baya da wannan matsalar. Asali shan nonon Akuya yana sacce kumburin ciki.
Nonon Akuya na kumshe da sinadiran dake busa garkuwan jiki wadanda sune ke da alhakin yaki da kwayoyin cuta wadanda idan su ka yi rauni to cuta za ta fi karfin jiki.
-Nonon Akuya na maganin cututtukan ciki kamar su kumburin ciki, ciwon ciki, kukan ciki, murdawarsa da kuma yawan tashin zuciya.
-Nonon Akuya na gyara fatar jiki, shi ya sa kuke ganin fararen buzayen dake shan nonon awaki kamar Turawa.
-Idan kitse ya yi maka katutu a jiki to ka lazimci shan nonon Akuya zai narke maka da kitse mara kyau.
-Idan kana son rage nauyin jiki ko kiba to ka nemi nonon Akuya lafiyayya ka dunga sha.
-Mai fama da karamcin jini ko karamcin sinadiran iron to ka dunga shan nonon Akuya bayan shekara daya sai ka yi mamaki.
-Domin samun karfin kashin jiki kamar buzayen nan dake kokowa a Tawa dake a Nijar sai a dunga shan nonon Akuya.
-Nonon Akuya na kare zuciya daga wasu cututtukan da bamu da masaniya a kan su.
-Yana rage damuwa da yawan bugun zuciyar sinadirai masu yawa a cikinsa.
-Nonon Akuya na wujuwuju da ciwon suga amma kuma akwai yanda za a sarrafa shi.
-Nonon Akuya yana kara kaifin basira kuma yana maganin shawara. kai hartama da ciwon tarin tibi da kuma ciwon hanta.
-Sai dai kuma idan za a shayarda jinjiri to kada a bashi nonon Akuya, abu mafi kyau shi ne a bashi nonan saniya.
SHARE 🐐
0 Comments