🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
Kamar yadda hotunan kasa inkun nazari da kyau, za kuga akwai irin wadannan mutanen musamman cikin mata da zakuga fatar idanunsu tayi duhu... tai wani circles, ko kuma iya fatar kasa wajen munjiryar idon ce tai duhun..... wanda kila wasu zasu rika tunanin ko saboda kwalliya da shafa su powder afuska ne da sauransu ke jawo musu hakan. Toh ba hakan bane.
Koda yake wasu sukan gani ma amma tunda ba ciwo suke ji ba bama sa ta6a maida hankali akai....
ABUNDA KAN JAWO HAKAN SHINE:
■Yawan bacci mutum ya zamto yana shafe sama da awa 8 ko yaushe yana bacci
■ Karancin bacci, mutum yake shiga har yankin dare sama da 12 amma baiyi bacci ba
■ Yawan kallon Tv kullum kullum har abun ya zamewa mutum jiki..
■ Yawan amfani da na'urar computer.... ana kallon screen
■ Yawan amfani da wayar salula, walau yanayin game, ko chatting ko kallo ko kuma dukkan wani abu... ko yaushe ace idon mutum nakan screen
■ Sai kuma girma wato alamun shekaru a wanda yabaiwa shekaru 50 baya. Amma irin wannan su zakuga fatar idon kamar ta dan kwakkwa6o tai kamar ta kumbura haka...
■ Kasala; wato ya zamto mutum baida garkuwar jiki me karfi kusan akai akai ko yaushe cikin ciwo yake. Ko kuma yana dauke da wani ciwo me raunana garkuwar jikin kamarsu (ciwon suga, HIV, cancer) da sauransu
■ Karancin ruwa ajika wato DEHYDRATION
■ Yawan aiki arana... wato kai komo acikin rana
■ Sai kuma kaso kalilan dakan zamto gado sukai. Musamman in cikin mahaifansu akwai mai su.
Don haka dukkan wadancan abubuwan dana lissafo idan kasan ko kikasan kina dashi... toh na tabbata zuwa yanzu kingano ta inda matsalarki ta faro. Don haka nasarar dakatar da duhun tana rataye da kokarunku na kiyaye abunda kuke.
Imba haka ba tohfa duhun cigaba da qaruwa zai wanda akarshe zai zamto yana karyata shekarunku domin za'a rika yiwa mutum kallon tsoho alhalin da sauran kuruciyarsa. Yar shekara 20 za'a ke ganinki a yar 40yrs...
MATAKAN KARIYA
1. Me raunin garkuwar jiki ya maida hankali yaci abinci me gini jiki tare da kiyaye magani
2. Me yawan chat, ko yin video game, ko kallo shima ya takaita zarar ya fara ganin alamun
3. Me yawon kallon tv ko aiki da computer atakaita.
4. Me shafe dare yaki kwanciya bacci ya dena ya rika kwanciya yana samun baccin awa 7 zuwa 8 kullum
5. Amfani da tea bag wato lipton... idan aka tsoma jakar aruwan sanyi sai adorata agefen idon gurin da duhun yake.... daga baya in anjima tai laushi sai acire awanke fuskar.... yin Hakan ahankali-ahankali ka iya ragen duhun koma ya fitar dashi.
0 Comments