Mace dai ta kasance tamkar wata furen fulawa wanda idanun mutum suke sha’awar kallo a koda yaushe, ita fulawa ta kasance aba ce mai kamshi. Haka bayan kyawun kallo, tana da bukatar kasancewa a cikin inuwa, domin idan aka sanya ta a rana za ta yi yaushi. To tamkar haka mace kan kasance a wajen sanyaya zuciya da sanya farin ciki a zuciyar abokin rayuwarta.
Wannan kuma tun ran gini tun ran zane, domin kuwa mace tun tana ‘yar karamar yarinya ta kasance mai kokarin son yin hidima ga wani, domin hadda wasanta na yarinya ba ya wuce na kula da jaririyarta (‘yar baby), ta kara ce ko ta roba ce. Tare da son taya mahaifiyarta aikin gida.
Kuma a gaba haka za ta kasance har bayan ta girma ta yi aure inda take zama rumfa da kuma zama garkuwa ga dukkan mutanen gida ta hanyar sadaukar da rayuwarta domin ta faranta masu da haskaka masu hanyar rayuwa. Wannan ya ta’allaka ne tun daga mijinta da ‘ya’yanta da dangin mijinta da makwabtansu. Za ta kasance cikin hidimarsu ta yadda takan kasance tamkar wata baiwa wadda ita ba ta ma san wani abu jin dadi ba. Haka za ta rika gudanar da hidima ga iyalinta, kowa ya riga ta kwantawa domin yin barci kuma ta riga kowa tashi don ta share masu fagen fara rayuwa a wannan sabuwar rana.
Da irin haka kuruciyarta za ta tafi cikin hidimar gyaran al’ummarta, kyawunta da kuruciyarta da karfinta da komi nata a hankali haka za su gushe amma ba ta damu ba, manufarta daya ce rak wato sanya wa kowa farin cikin rayuwa da mika su zuwa ga ingantacciyar rayuwa har su kai ga burinsu.
Mace duk a cikin wannan tashi-fadin da take yi abu daya kawai take nema wato shi ne a nuna mata kauna da soyayya ta gaskiya ba tare da an ci amanarta ba ta kowace fuska. Sai dai hakan yana gagara a wajen da yawanmu maza. Yayin da wasunmu suka dauke ta wata abu kawai ta biyan bukata wacce ba ta da wani gata da daraja illa kawai ta biya wa mutane bukatunsu ta gusar musu da sha’awarsu. Wannan ya yi kama da yadda aka dauki mace a zamanin jahiliya. Yayin da su kuma Turawan yanzu suka dauki mace a matsayin wacce za ta kure kyawun fuskarta ta bude adonta da wasu daga cikin ni’momin da Allah ya yi a gareta, kawai domin jama’a su gani su yi dariya, sannan su ji dadi a kan haka suka mai da ita ‘yar aikin banki ko kuma ‘yar aikin shaguna ko ‘yar fim. Koma mai watsa shirye-shirye a cikin tashoshin talabijin ko ta watsa daddadar muryarta a cikin rediyo jama’a suna saurara. Ko ma ta koma wacce za a saka hotunanta a cikin abubuwan sayarwa ta rika kwaye tsiraicinta tana fitinar al’umma da kyawun surarta, tana sayen fushin Allah ga kanta da sauran mutanen duniya.
Su manufarsu kawai ita ce, domin ta janyo musu kasuwa ga abin da suke sayarwa, ita kuma ta nemarwa kanta mummunan karshe tun a nan duniya. Wacce za ta hadu da azabar Allah a gobe kiyama, ta kasance daga cikin makamashin wuta.
Yayin da shi kuma addinin gaskiya na Musulunci tun farkon zuwansa ya karrama ta, ya ‘yantar da ita, ya ba ta hakkinta tamkar namiji wajen samun sakamako a kan wahalhalunta tun ma a nan duniya.
Mata ku gode wa Allah a kan zuwan addinin Musulunci kuma ku gode wa Allah idan har ya hallicce ku Musulmai, ku bi Allah, ku bi sunnar Annabinsa, ku yi koyi da iyayen muminai domin ku shimfida rayuwa ingantacciya. Kuma ku samar da ‘ya’ya na gari, ku ba su tarbiya ta gari, a karshe su zama jama’a ta gari, a samu shuwagabbani na gari da ma’aikata na gari ko ‘yan kasuwa na gari ko malamai na gari. Kun ga dalilinku sai a samu al’umma ta gari. Mace ta gari ta sa duniya duk ta zama ta gari.
Mu kuma maza mu lura da yadda addininmu ya karamma mace, ya ba ta girma da daraja wanda shi ne dalilin da ya sanya muka dauke ta da daraja. Mu yi nazarin rayuwar Annabawa da salihan bayin Allah, yadda suka yi zamantakewarsu da matansu suka yi hakuri da su suka faranta musu rayuwa, suka nuna musu soyayya ta gaskiya ta tsakani da Allah. Idan muka yi nazarin a kan wadannan abubuwan za mu sauke nauyin da Allah ya dora mana a kan mata.
Kuma idan aka tambaye mu a kan abubuwan kiwonmu wadanda mata suna cikinsu, to a nan za mu bayar da amsa muna masu farin ciki da jin dadi.
Lallai magabatanmu sun yi adalci wajen nuna girman ‘ya mace, kuma sun nuna matsayinta da sadaukarwarta. A karshe, Allah ya sa mu kasance masu riko da gaskiya ba son ranmu ba.
0 Comments