SAMUN KUZARI DA KARSASHI GAME DA SALLAR DARE DARASI NA 13




Akwai wasu ladubba da ake so mutum ya kula da su waɗanda za su ƙara masa karsashi da nishadi idan yana son ya yi ƙiyamul laili. Su ne kamar haka:

Mutum ya shirya cewa shi yana son ya yi tsayuwar dare ne ta hanyar yin barci ɗan kaɗan irin wanda ake yi da rana wanda ake cewa ƙailula ta yadda zai rage masa nauyin barci da daddare, sannan ya daina zaman hira har dare ya tsala, ko kalle-kallen talabijin, ko danne-dannen wayar hannu, wanda wannan zai iya sawa jiki ya yi nauyi idan an zo an kwanta ba za a iya tashi ba. 

Mutum ya yi niyyar yana so ya tashi ya yi sallar dare don neman kusanci ga Allah ﷻ domin hadisi ya zo daga Abud Darda'i رضي الله عنه daga Ma’aiki ﷺ inda yake cewa,”Wanda ya zo shimfiɗarsa ya kwanta a zuciyarsa, yana so ya tashi ya yi nafilfili da daddare sai idonsa ya rinjaye shi bai farka ba har ya wayi gari, to za a rubuta masa abin da ya yi niyya, wannan barcin kuma zai zama sadaƙa a gare shi.” ()

Mutum ya yi barci da alwala domin yin barci da alwala yakan hana mutum ya yi barci mai nauyi ƙwarai.

Mutum ya yi barci a kan ɓangarensa na dama, saboda hadisin Ummina Hafsat رضي الله عنها inda take cewa, Manzon Allah ﷺ ya kasance idan ya zo kwanciya yakan sanya hannunsa na dama a ƙarƙashin kumatunsa na dama.” ()

Idan mutum ya ji tsoron ba zai farka da daddare ba, to sai ya fara yin wutiri kafin ya kwanta.

Mutum ya ambaci Allah ﷻ idan zai kwanta barci, saboda shi ambaton Allah ﷻ idan za a yi barci yakan tsare mutum daga sharrin Sheɗan, kamar yadda Nana A’isha رضي الله عنها ta tuwaito cewa, idan Ma’aiki ﷺ ya zo makwancinsa a kowane dare yakan haɗa hannayensa guda biyu sai ya tofa ƙulhuwAllahu da falaƙi da naasi a cikinsu sai ya shashshafe iya inda hannunsa zai kai, kuma yana farawa daga kansa da fuskarsa sannan gaban jikinsa, yana yin haka sau uku. ()

Idan mutum ya tashi daga barci ya goggege alamar kwantsa a idanunsa da fuskarsa ko yawun barci idan ya zuba, sannan ya ambaci Allah ﷻ ya yi alwala, kamar​ yadda ya zo a cikin hadisin Bukhari da Muslim. 

Mutum ya yi amfani da asuwaki, saboda hadisin Huzaifatu Bn Yaman رضي الله عنهما da yake cewa, idan Ma’aiki ﷺ ya tashi da daddare zai yi tahajjudi yakan fara goge bakinsa da asuwaki. ()

Mutum ya fara buɗe ƙiyamullailinsa da raka’o’i biyu gajeru kafin ya shiga dogaye, kamar yadda Ummina A’ishah رضي الله عنها ta ke cewa, Manzon Allah ﷺ ya kasance idan zai yi sallar dare yakan farawa da gajerun raka'o'i guda biyu kafin dogaye. Imamu Ahmad da imamu Muslim ne suka ruwaito shi. 

Mutum ya buɗe sallar dare da irin addu'o'in da Ma’aiki ﷺ ya koyar bayan ya yi kabbara, kamar yadda ya zo a hadisi, daga cikin irin addu’o’in akwai:
((اللَّهُمَّ لَكَ الْحَمْدُ، أَنْتَ نُورُ السَّمَوَاتِ وَالأَرْضِ وَمَنْ فِيهِنَّ، وَلَكَ الْحَمْدُ أَنْتَ قَيِّمُ السَّمَوَاتِ وَالأَرْضِ وَمَنْ فِيهِنَّ، [وَلَكَ الْحَمْدُ أَنْتَ رَبُّ السَّمَواتِ وَالأَرْضِ وَمَنْ فِيهِنَّ] [وَلَكَ الْحَمْدُ لَكَ مُلْكُ السَّمَوَاتِ وَالأَرْضِ وَمَنْ فِيهِنَّ] [وَلَكَ الْحَمْدُ أَنْتَ مَلِكُ السَّمَوَاتِ وَالأَرْضِ] [وَلَكَ الْحَمْدُ] [أَنْتَ الْحَقُّ، وَوَعْدُكَ الْحَقُّ، وَقَوْلُكَ الْحَقُّ، وَلِقاؤُكَ الْحَقُّ، وَالْجَنَّةُ حَقٌّ، وَالنَّارُ حَقٌّ، وَالنَّبِيُّونَ حَقٌّ، وَمحَمَّدٌ - صلى الله عليه وسلم - حَقٌّ، وَالسّاعَةُ حَقٌّ] [اللَّهُمَّ لَكَ أَسْلَمتُ، وَعَلَيْكَ تَوَكَّلْتُ، وَبِكَ آمَنْتُ، وَإِلَيْكَ أَنَبْتُ، وَبِكَ خاصَمْتُ، وَإِلَيْكَ حاكَمْتُ. فَاغْفِرْ لِي مَا قَدَّمْتُ، وَمَا أَخَّرْتُ، وَمَا أَسْرَرْتُ، وَمَا أَعْلَنْتُ] [أَنْتَ المُقَدِّمُ، وَأَنْتَ المُؤَخِّرُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ] [أَنْتَ إِلَهِي لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ)). ()
Mutum ya tsawaita raka'o'in tsayuwar dare, sai dai kada ya yi abin da zai takurawa kansa har ya rasa nishaɗinsa da samun ɗanɗanon ganawa da wanda yake yin sallar don shi. ()

Mutum zai iya yin sallar nafila a tsaye, kuma zai iya yi a zaune idan ya gaji domin Ma’aiki ﷺ ya yi sallar dare kashi uku: 

 Ya yi sallah a tsaye gaba ɗayanta daga farko har ƙarshe. 

 Ya yi sallah a zaune daga farko har ƙarshe, wato ya yi ruku'u a zaune. 

 Ya yi sallah rabi a zaune, rabi kuma a tsaye, wato ya fara sallar a zaune sai ya rage wasu ayoyi kaɗan kamar aya (30) zuwa (40) sai ya miƙe ya ƙarasa sallar a tsaye. 

Sannan kuma idan mutum yana sAllah sai ya gaji ko ya fara jin barci, to ya kwanta ya ɗan rintsa domin barcin ya tafi, shi kuma ya sami nutsuwar da zai iya ci gaba da sallar, saboda hadisin da Ma’aiki ﷺ ya shigo masallaci sai ya samu an ɗaura igiya daga wannan al'amudin zuwa wancan, sai ya ce menene wannan? Sai aka ce igiyar Zainab ce da take yin sallah idan ta gaji sai ta jingina da ita, sai Ma’aiki ﷺ ya ce, “Ku kwance ta, sannan ya ce, mutum ya riƙa yin sAllah da nishaɗinsa shi ya fi idan ya ji kasala ko gajiya sai ya kwanta ya yi barci. Imamul Bukhari da Muslim suka ruwaito shi. 

Mutum ya yi karatun Alqur’ani ya rera shi da kyakkyawar murya kuma ya yi shi da bin ƙa'idojin karatu, saboda ayar Alqur'ani tana cewa:
﴿وَرَتِّلِ الْقُرْآنَ تَرْتِيلًا۝﴾ ()

Ma’ana: “Ka karanta Alqur’ani ka rangaɗa shi rangaɗawa mai ban sha'awa.” 

Mutum ya riƙa bin ma'anonin fassarar Alqur’ani a yayin karanta shi, ya kuma riƙa yin ƙoƙari wajen halarto abin da Alqur’anin yake faɗa na umarni ko hani domin samun damar yin kuka a inda ya kamata a yi kukan, ko shiga jazaba domin firgici da tsoro a inda ya kamata aji tsoron, ko nishaɗantuwa a inda nishaɗin ya zo a cikinsa. 

Saboda hadisin Huzaifah رضي الله عنه da ya ce, Ma’aiki ﷺ yana yin karatu ne daki-daki, idan ya wuce wata aya wadda akwai tasbihi a cikinta sai ya tsaya ya yi tasbihin, idan kuma ya wuce ayar da ake neman tsari a cikinta, sai ya tsaya ya nemi tsarin Allah ﷻ a wurin, idan kuma ya wuce ta ayar da take akwai roƙo a cikinta, sai ya tsaya ya yi roƙon. 

Mutum ya yawaita addu'a a lokacin karatun Alqur’anin a lokacin sahur da ƙarshen dare a cikin sallah da wajen sallah , saboda hadisin Jabir Bn Abdullahi رضي الله عنه da ya ce, a cikin dare akwai wata sa'a mutum ba zai dace da wannan sa'ar yana roƙon Allah ﷻ wani abu na alkhairin duniya ko na lahira ba, face sai Allah ﷻ ya ba shi abin, wannan kuma yana faruwa ne a kowane dare.” () 

An so mutum ya tashi iyalansa su yi tare, kamar yadda hadisi ya zo cewa, “Wanda ya tashi iyalinsa suka yi sallah a cikin dare za a rubuta shi a cikin masu yin zikirin Allah ﷻ da yawa maza, da masu yawaita zikirin Allah ﷻ da yawa mata.”

Mutum ya ɗan kwanta ya huta bayan ya gama ƙiyamullaili ko sallar dare kafin Alfijir ya fito.

Ba a son wanda ya saba yin sallar dare kuma ya daina, saboda hadisin Abdullahi Ɗan Amru رضي الله عنه ya ce, Ma’aikin Allah ﷺ ya ce da shi, “Ya kai Abdullahi kada ka zama kamar wane mana, ya kasance da dare yana yin tsayuwar dare kuma daga baya sai ya daina.” Kamar yadda ya zo a ruwayar Bukhari da Muslim​​.
* * * *

Post a Comment

0 Comments