DAREN LAILATUL QADARI:



DARASI NA 14.

Allah ﷺ ya fifita wani dare a cikin watan Ramadan ya ba shi wata daraja da ɗaukaka ta musamman, kuma ya keɓance shi da wata falala ta musamman wadda bai ba wa sauran darare ba, wannan kuma zaɓi ne da ganin dama daga gare shi maɗaukakin sarki, domin yana yin abin da ya so a cikin halittarsa, da mashi'arsa.
 Wannan dare shi ne daren lailatul ƙaɗari wanda Allah ﷻ a cikin suratul ƙaɗri ya ce:

﴿إِنَّآ أَنزَلْنَٰهُ فِى لَيْلَةِ ٱلْقَدْر۝ وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا لَيْلَةُ ٱلْقَدْرِ۝ لَيْلَةُ ٱلْقَدْرِ خَيْرٌ مِّنْ أَلْفِ شَهْرٍ۝ تَنَزَّلُ ٱلْمَلَٰٓئِكَةُ وَٱلرُّوحُ فِيهَا بِإِذْنِ رَبِّهِم مِّن كُلِّ أَمْرٍ۝ سَلَٰمٌ هِىَ حَتَّىٰ مَطْلَعِ ٱلْفَجْرِ۝﴾ () 
Ma’ana: “Lallai tabbas cewa mu muka saukar da shi wannan Alƙur'anin a cikin dare mai Al-ƙaɗari da matsayi a wajen Allah ﷻ waya sanar da kai menene lailatil ƙaɗari? Wannan dare mai Al-ƙaɗari ya fi watanni dubu, Mala'iku suna sauka a cikinsa tare da ruhu (Mala'ika Jibrilu) suna sauka a cikinsa da dukkanin al'amurra, da izinin Ubangijinsu ﷻ, waɗannan Mala'iku kalmar aminci kawai suke ta faɗa har zuwa hudowar Alfijir.”
 
Lallai ko ba a faɗa ba, wannan sura ta fito da darajar wannan dare mai albarka, ta fuskoki guda shida, kamar yadda ya zo a cikin littafin At-Tafsil litawilit tanzil na Malam Musal Adawi ya ce, 
    Allah ﷻ ya saukar da wannan Alqur’ani a wannan dare kamar yadda ya faɗa a cikin Alqur’ani inda yake cewa:

﴿إِنَّا أَنْزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةٍ مُبَارَكَةٍ إِنَّا كُنَّا مُنْذِرِينَ ۝ فِيهَا يُفْرَقُ كُلُّ أَمْرٍ حَكِيمٍ۝﴾ ()
Ma’ana: “Lallai haƙiƙa mu muka saukar da shi a cikin dare mai albarka, haƙiƙa mu masu gargaɗi ne da yin azaba ga kangararru.”
Allah ﷻ ya girmama sha'anin wannan dare da ya ce, waya sanar da kai mene ne lailatul Qadari? 
Yin ibada a cikin daren ya fi yin ibada a dare dubu (1000), wato Shekara (83) da wata (2) kenan. 

Mala'iku suna sauka acikin wannan daren, kuma an ce, suna sauka ne da rahama, da albarka, da nutsuwa, kuma an ce suna sauka ne da dukkan wani al'amari da Allah ﷻ ya zartar, kuma ya ƙaddara shi a cikin wannan Shekarar. 

Aminci da sallama suna sauka a cikin wannan dare ga masu imani da kuma sallamar da Mala'iku suke yi musu. 

Abu Hurairah رضي الله عنه ya ce, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Wanda ya yi azumin watan Ramadan yana mai imani yana kuma neman lada, to za a gafarta masa abin da ya wuce na zunubinsa.” () 

Haka nan wanda ya tsaya a daren lailatul ƙaɗari yana mai imani yana mai neman lada, za a gafarta masa abin da ya wuce na daga zunubansa.”

DA YAUSHE NE AKE SAMUN DAREN LAILATUL QADARI?

Shi dai lailatil Qadari ana samunsa ne a cikin watan Ramadan, kamar yadda Allah ﷻ yake cewa:
﴿شَهْرُ رَمَضَانَ الَّذِي أُنْزِلَ فِيهِ الْقُرْءَانَ هُدًى لِلنَّاسِ﴾ ()
Ma’ana: “Watan Ramadan shi ne watan da aka saukar da Alqur’ani a cikinsa domin ya zamo shiriya ga mutane.” 
Amma a wajen iyakancewa, ko tantance a dare na nawa ne ake samunsa, Ibn Hajar Al-Asƙalani ya ce, malamai sun yi saɓani mai yawa kusan ƙauli arba'in (40) kamar yadda ya kawo a fatahul bari tare da hujjojin kowane malami. 
Sai dai mafi yawan malaman sun tafi a kan cewa ana samun wannan dare ne a goman ƙarshe na watan Ramadan, kamar yadda ya zo a hadisin Abu Sa'dil Khudri رضي الله عنه inda yake cewa, Ma’aikin Allah ﷺ ya ce, “Ku nemi daren lailatul ƙadri a goman ƙarshe.” ()
Haka nan kuma mafi yawan malaman sun tafi a kan cewa, daren yana cikin mara goman ƙarshen. 

Saboda hadisin da Ma’aiki ﷺ yake cewa, “Ku kardaji daren lailatil ƙadri a cikin mara goman ƙarshe.” Kamar a dararen 21-23-25-27-29. 
Mafi yawan malamai kuma sun tafi a kan daren (27) ne kai tsaye babu tantama, wannan kuma shi ne abin da wasu daga cikin sahabbai suka tafi a kai.

 Daga cikin su akwai Ubayyu Ɗan Ka'abu رضي الله عنه domin shi har rantsuwa ya yi a kan cewa, daren (27) tabbas shi ne daren lailatil ƙadri. 

Abin da ya fi kamata a dogara da shi shi ne, lallai shi daren lailatul Qadari yana cikin watan Ramadan, kuma ana samunsa a goman ƙarshe, sai dai kuma yana sassauyawa daga Shekara zuwa Shekara. 
Ma’ana: wani lokaci za a iya samun sa a (21), a wata Shekarar kuma a same shi a (23) a wata Shekarar kuma a same shi a (25), a wata kuma a same shi a (27), amma dai an fi dacewa da samunsa a daren (27). 
Shi ya sa a wani hadisi Ma’aiki ﷺ yake cewa, “An nuna min lailatil ƙaɗari sai aka mantar da ni shi, amma ku neme shi a cikin goman ƙarshe a cikin wutiri, domin na ganni ina sujjada a cikin ruwa da caɓalɓali.” 

Abu Sa'idil Khudri رضي الله عنه ya ce, an yi wannan ruwan ne kuma a daren (21) ga watan Ramadan, don haka wannan ya nuna kenan wata Shekarar za a iya samun sa a (21) a wani lokacin kuma a same shi a saɓanin wannan.
* * * *

HIKIMAR DA TASA AKA ƁOYE DAREN LAILATUL QADARI
HIKIMAR DA TA SA ALLAH ﷻ YA ƁOYE DAREN LAILATUL ƘADARI ITA CE:

Domin mutane su zage ɗantse da yin biyayya da ayyukan ɗa'a waɗanda za su ƙara kusantasu ga Allah ﷻ a cikin sauran dararen da suke cikin watan. 

Saboda da mutane kai tsaye za su san ainihin takamaiman daren, da kawai sai su taƙaita ibadunsu da ƙoƙarinsu da jajircewarsu ta hanyar dogara da wannan daren shi kaɗai, sai su bar sauran dararen ba za su raya su ba, ta haka za su taƙaita a ibada kenan a cikin watan da ake yabon masu jajircewa da raya shi da nau'o'in ibada, shi ya sa aka ɓoye sanin haƙiƙanin daren da zai wuce. 

Kamar yadda Ma’aiki ﷺ yake cewa, “Na fito da niyyar in bayyana muku sanda za a sami daren lailatul ƙadari kai tsaye, sai na sami wane da wane suna faɗa, sai aka mantar da ni sanin wannan daren, amma dai ina fata hakan ya zama alkhairi a gare ku, don haka sai ku tashi ku yi da gaske ku neme shi.” ()

NEMAN DAREN LAILATUL QADARI:

Shi daren lailatul Qadari dare ne mai albarka mai daraja, wanda duk aka haramta masa shi an haramta masa alkhairi mai yawa, babu wanda ake haramta wa alkhairi sai wanda ba shi da shi, don haka ya kamata ga dukkanin Musulmi mai hankali ya dage ya ci ɗamara ya yi ƙoƙarin aikata ayyukan ɗa'ar da za su ƙara kusanta shi ga Allah ﷻ ta hanyar raya waɗannan darare na Ramadan gaba ɗaya, musamman ma dararen goman ƙarshe. 

Akwai alkhairi matuƙa cikin raya su da salloli da karatun Alqur’ani da tasbihi da hailala da istigfari da salati ga Annabi ﷺ a bisa tsammanin samun kusanci ga Allah ﷻ da neman falalarsa da samun ladansa mai girma. 

Sannan kuma mutum ya yi da gaske a goman ƙarshe domin koyi da Ma’aiki ﷺ kamar yadda Ummina A’ishah رضي الله عنها take cewa, Manzon Allah ﷺ ya kasance yana yin ƙoƙari a goman ƙarshe fiye da ƙoƙarinsa a wani watan wanda ba na Ramadan ba.” ()

Duk mutumin da yake neman daren lailatul ƙadri bayan dagewarsa da sAllah da ayyukan ɗa'a, to haka nan ma an so ya tashi iyalansa, wato matansa da 'ya'yansa waɗanda za su iya yi su ma su yi iya bakin ƙoƙarinsu wajen ibadar. 

Saboda hadisin A’ishah رضي الله عنها inda take cewa, Manzon Allah ﷺ ya kasance idan goman ƙarshe ta shigo sai ya ci ɗamara ya ƙara zage ɗantsen wajen ibadarsa da daddare kuma ya tashi iyalinsa.” ()

ADDU'AR DA AKE YI A DAREN LAILATUL QADARI;

An so a yawaita addu'a a goman ƙarshe na watan Ramadan, musamman ma a dararen da ake tsammanin wucewar wannan dare na lailatul ƙadari, wato su ne dararen (21-23-25-27-29) ana so mutum ya ƙara tsanantawa a wajen nacin addu'a a dare da rana, da fatan samun karɓuwarta, don neman falalarSa, tausayinSa, rahamarSa da kuma karamcinSa a kan bayinSa. 

Sannan an so ya dage wajen maimaita irin addu'ar da aka jiyo ta daga bakin Ma’aiki ﷺ, kamar yadda Ummina A’ishah رضي الله عنها take cewa, na ce da Ma’aiki ﷺ ya Ma’aikin Allah ﷺ idan Allah ﷻ Yasa na dace da daren lailatul ƙadari mai kake ganin zan roƙa? Ma’ana wacce addu'a ya kamata in yi? Sai ya ce mata ki ce, “Ya Allah ﷻ kai mai afuwa ne kuma kana son yin afuwa ka yi min afuwa.” ()

ALAMOMIN DA AKE GANE DAREN LAILATUL QADARI:

Shi daren lailatil ƙadri yana da wasu alamomi da ake gane shi da su:
Sararin samaniyar wannan daren zai kasance shiru fayau-fayau babu wata hargowa, cikin nutsuwa, babu wata iska mai bugawa da ƙarfi gari ya yi tsit. 

Kamar yadda Abdullahi ɗan Abbas رضي الله عنه yake cewa, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Shi daren lailatul ƙadari dare ne mai sauƙi, kuma sakakke ba shi da nauyi a jikin mutane da ruhinsu, kuma shi dare ne wanda ba shi da tsananin zafi, ba shi da tsananin sanyi, wato dare ne madaidaici ga jikin ɗan’adam da kuma ruhinsa, don haka rana za ta wayi gari mai rauni mara kaifi kuma ja.” () 

Samun nutsuwa da kwanciyar hankali a jikin muminai da kuma ruhinsu, saboda saukar Mala'iku a cikin daren, sai Musulmi su riƙa jin wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali a zuciyarsu da kuma jikunnansu, ƙirjinsu ya saki ya washe babu nauyi a cikinsa, su sami ɗanɗano da nishaɗi a wajen ibada a cikin daren za su riƙa jin hakan ninkin yadda suka saba ji a wani daren wanda ba shi ba. 

Mutum zai iya ganinsa a cikin barcinsa, wato a mafarki kamar yadda hakan ya tabbata daga sashin sahabban Ma’aiki ﷺ da waninsu. 
Idan daren ya gabata washegarin safiyar daren za a ga ranar ta ɓullo wankakkiya fara tas, babu wani gurɓata a cikin ƙwallon haskenta.
 Kamar yadda hadisi ya zo daga Ubayyu Bn Ka’abu رضي الله عنه inda yake cewa, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Washe garin daren lailatul ƙadri rana za ta bayyana ne ta ɓullo babu gurɓata a cikin haskenta.” ()
Akwai wasu alamomi kuma na daban waɗanda mutane suke ambaton su waɗanda a gaskiya ba su tabbata daga Ma’aiki ﷺ ba, sai dai ko wataƙila wasu sun gansu ne, kamar a ce, idan daren ya bayyana za a ga bishiyoyi sun kwanta gine-gine sun ranƙwafa, kuma ba za a ji haushin kare ko na jaki a daren ba, da dai sauran su. 
A gaskiya dai waɗannan alamomi ba su tabbata da nassin hadisi ko a ingantattun fatawoyi malamai ba.

Allah kasa mu gama da duniya lafiya ka karɓi addu'ar mu.

Post a Comment

0 Comments