YADDA ZAKI HADA ( DAMBUN SHINKAFA ) DAMBUN KWAI:


Danbum Shinkafa

Kayan hadi

Shinkafa
Zogale
Mai
Tattasai
Albasa
Nama ko kifi
Maggi
Gishiri
Yadda Zaki Hada

Ki bada a barzo shinkafa saiki sa rariya tankaden gari ki fidda gari Dan kar dambun ya hade. Saiki wanke shinkafar da aka barza ki yanka nama kanana cikin ta saiki zuja su hade ki zuba ga abunyin dambu, Saiki yanka tarugu albasa da tattasai ki hada da zogale ki wanke. Saiki kwashe danbun da kika Dora a wuri mai fadi ki zuba su zogale da maggi da gishiri kiyayyafa ruwa ki juya suhade ki mayar ya qara turara idan yayi ki sauke kiss mai shikenan. Amma idan da steamer zakiyi komai zaki zuba a shinkafar ki zuba. Amma idan da abun yi na gargajiya zakiyi yafi kyau ayi bugu 2 yadda nayi bayani. Kuma idan kinaso zaki iya sa su karas,nidai da kifi nayi amfani aci lyf.

Yadda ake funkaso

Kayan Hadi

Alkama (gwangwani hudu
Filawarki (gwangwani daya)
Ruwan tsamiya (kamar Rabin gwangwani)
Yeast (cokalin shayi karyayi tsiri)
Sikari (cokali daya)
Ruwan kanwa (cokali daya) 
Mansuya (kwalba daya)
yadda zaki hada

Kisami robarki mai murfi ki zuba sikariki da da yeast da ruwan tsamiya da kanwa kamar yadda na auna miki filawarki ki hadata da garin alkamarki idan yeast ya narke kijuye filawarki ki kwaba sosai ki tabbatar ba gudaji kuma kar kwabin yayi ruwa karkuma yayi tauri tikiki saiki rufe ya samu kamar awa daya zakiga ya tashi ki dora manki yayi zafi sosai ki sami kwabin ki kara juyashi sosai zakiga ya koma ya kwanta kuma zakiga ayayin da kika dada juyashi kwabin ya dada sakin jikinsa saiki sani dan farantinki ki shafe da ruwa kirika gutsurar kullin kina sawa akan dan farantin ki huda tsakiya saiki saka acikin mai zakiga yana dagowa yana fadawa cikin mai a hankali da kulawa abin

 Lura shine funkaso bayason yawan juyawa idan kinga kasan ya soyu saiki juya saman shima ya soyu kuma funkaso bayason mai kadan wajan suya yafison mai wada tacce ya sakata ya wala amfanin tsamiya a funkaso shine bazai taba sha miki maiba kuma zai miki suya tai ja tayi kyau wannan shine iya awon danayi idan da yawa zakiyishi to haka zakirika aunawa kina kara yawan abinda na lissafo miki uwargida ko amarya dafatan zaki nutsu wajan gwaji.

Dambun Kwai

 *Ingredients:_

Kwai
Nama
Curry
Maggi
Gishiri
Albsa
Tarugu
 

*procedure*

Zaki tafasa namanki da citta da albasa magggi gishiri inyatafasu saiki sauke kizuba shi aturmi kidakashi yayi kamar zakiyi dambun nama saiki juyeshi awurimaifadi saiki zuba jajjage aciki saiki fasa kwai biyar

Kiyanka albasa kixuba curry saiki zuba maggi da gishiri kadan saiki jujjuyashi saiki. Daura mai inyayizafi saikizuba naman dakikahada inyasoyu zakiji kamshi saiki sauke

Butter yam

Ingredients

Doya
Butter cokali8
Albasa1
Kwai:3
Curry cokali 1
Gishiri
Mai na suya.
METHOD

Ki fere doya ki yanka ki dauraye ki dafa ta sai ki marmasata sosai ki zuba butter ki sa maggi gishiri curry sai ki lailayata dogaye kamar girman spring rols ki sata a furji ko gurin mai sanyi tayi awa daya sai ki kada kwai ki dora mai a wuta yayi safi saiki dinga tsoma doyarki. Acikin ruwan kwai kina sawa a mai kina soyawa idanyayi ruwan kasa sai a tsame.

Alalen Doya

Kayan Hadi:

Kwai
Doya
Curry
Hanta
Maggi
Attaruhu
Za a wanke doyar sai a yanka ta daidai yadda hannu zai iya rikewa, sannan a goge ta a jikin greater, sai a yi blanding dinta da attaruhu da albasa! yayi kauri kamar yanda ake kullun wake, sannan akawo maggi asaka, asaka curry kadan ba’aso yafito, se’akawo yankakkiyar dafaffen hanta asaka aciki, akawo yankakken dafaffen kwai asaka aciki! Amma kananan yanka da’ayi musu, idan ba’a bukatar dafaffen kwai da’a iya saka danye bayan ankadashi, da’a kulla kamar yanda akeyin Alalen wake, sai adafashi, ana iya cinshi haka nan, kuma da’a za’a iya cinsa da miya

Alalen fulawa:

Kayan Hadi:

Fulawa
Kwai
Nama
Kifi danye
Markadadden kayan miya
Albasa
Attarugu
Curry
Gishiri
Maggi
Ki tafasa kifi, ki bare ki fidda tsokar, ki kwaba fulawa da kauri kamar kwabin Alale, fulawa gwangwani hudu, sai ki fasa kwai hudu akai, ki zuba kifin da kika murmusa ki yanka nama kanana ki zuba, ki zuba markadadden kayan miya ludayi daya ki yanka albasa da attarugu, kisa curry, gishiri da maggi. Ki zuba mai gwangwani daya ki juya sosai, ki shafa mai a gwangwanaye ki zuzzuba ko ki kulla a leda ki dafa.

Alalen kabeji

Kayan Hadi

Kabeji
Wake
Hanta
Kwai
Kifi
Attarugu da Albasa
Maggi, Curry da Gishiri
Manja ko Man gyada
Ki surfa Wake gwamgwani hudu ki zuba attarugu da albasa ki kai a markada miki, ki yanka kabejinki kanana mai dan yawa ki zuba akai, ki yanka dafaffen kwai kizuba akai, kisa maggi, curry, gishiri ki juya sosai, kisa mai gwangwani daya, ki kara juyawa ki zuba a gwangwani ko leda ki dafa

Alalen dankali:

Kayan Hadi

Dankali
Nama
Kwai
Attarugu
Albasa
Curry
Maggi
Gishiri
Mai
Ki dafa dankalinki ki marmasa ko ki daka, ki tafasa nama ki daka kizuba akai, ki jajjaga attarugu da albasa kizuba akai, kisa maggi, curry, gishiri da mai, ki fasa kwai kizuba akai ki juya sosai, ki zuba a leda ko gwangwani ki dafa.

Alalen Plantain

 

Kayan Hadi:

Plantain
Garin plantain
Cray fish
Dry fish
Attarugu da Albasa
Curry
Manja
Ki bare plantain guda uku ko hudu, ki yanka kanana ki mutsittsike ko ki markada a blender, ki zuba garin plantain kofi daya da rabi akan plantain din dakika nika, ki gyara busasshen kifinki da dakakken cray fish akai, kisa maggi, gishiri, attarugu, albasa da mai akai ki juya, idan yayi kauri ki kara ruwa yazama kamar kullin Alale, ki zuba a gwangwani ko leda ki dafa.

Alalen Kwai, Nama Da Hanta

Kayan Hadi:

Kwai
Nama
Hanta
Albasa
Attarugu
Maggi da gishiri
Curry
Mai
Ki tafasa nama da hantarki da tafarnuwa da thyme da maggi da gishiri, ki yanka namar kanana, hantar kuma ki daka ta ki hada su guri daya, ki jajjaga albasa da attarugu ki zuba a kai ki fasa danyen kwai ki zuba akai, kisa maggi, gishiri, curry da mai ki juya sosai, ki zuba a leda ko gwangwani, ki dafa wannan Alale yana gina jiki sosai.

Post a Comment

0 Comments