Za a ga mace takai mace amma da zaran maza sun zo aurenta ana kwana biyu sai a nemesu a rasa. Hakan kuwa baya rasa nasaba da irin waɗansu munanan halaye da ɗabi'u ne da masu nemansu suka lura da su, ko kuma suka yi kokarin ta gyara taƙi.
Ga wasu halayen da cikin sauƙi suna iya korar duk namiji mai hankali da yake son mace da aure.
1: KARYA: duk inda namiji ya fahimcj ke mace mai son yin karya a zahiri ko ta alfahari kina iya koraras cikin sauƙi.
Akwai wasu 'yan matan a gaban samarinsu suke yiwa wani saurayin karya ta waya da tunanin su masu wayo ne. Hakan nasa idan namiji mai hankali ne zai soma tunanin shima abunda kike masa kenan. Muddin kika ci gaba da yin irin waɗannan halayen na karya a gabansa, tofa kina iya rasa shi.
YAUDARA: 'yan mata da dama suna da hali na son yaudarar maza ciki har waɗanda suka fito suka nuna suna sonsu da aure.
Inda zata rika nuna tamkar dagaake take son shi bayan amincewa data yi da shi. Amma tana fakewa da hakan ne domin cimma wani buri nata. Irin wannan da zaran mazan sun gano suna iya hakura.
Akwai kuma wasu matan da suke ɓoye yawan shekarunsu ko karancin shekarunsu ga mazan da suka zo nemansu da aure, hakan shima na iya zamemiki matsala. Haka matan da suka taɓa aure ko haihuwa da suke ɓoyewa, zai iya koran miki manemi.
3: CIN AMANA: wasu 'yan mata sunada mai sonsu da aure kuma sunda wanda suke soyayya da shi.
Shi wanda ake soyayyan da shi ita ke zuwa nemansa ba shi yake zuwa ba. Akwana a tashi duk ranar da mai nemanta da aure ya gano daga nan bai zai sake kulata ba.
4 KAWAYE: akwai 'yan mata masu tara kawaye birjim kuma kowasu iri. Ba duk namijin da yake son mace da aure bane yake son ganinta da tarin ƙawaye musamman marasa tarbiya.
Da zaran namiji mai sonki da aure ya fahimci bazai iya rabaki da irin waɗannan ƙawayen naki ba, tuni zai cikawa wandonsa iska.
5: ROƘO: yawan roƙon namiji musamman mai son aurenki na iya zama sanadiyar rabuwarku. Akwai wasu matan suna neman abu ana musu ko kamin ma amusu sun sake bukatan wani. Hakan na jefe zullumi da tsoro a zuciyar duk namiji mai hankali daya zo aurenki ganin zai wahala bayan auren naki da yawan buƙatunki.
Waɗannan dama wasu da bamu ambato suna cikin mugayen halayen da suke korar maza da wasu matan basu ɗaukesu matsala ba.
Dafatan za a kiyaye.
0 Comments