๐๐๐๐๐๐๐๐๐
๐
๐
๐๐
Anyi aure-aure musamman tun daga wajen November 2020 zuwa watan May dinnan wato kusan watanni 6 zuwa 7 kenan, wanda ahalin yanzu wasu har rabo ya samu atsakani.
Tunda nakan samu, shyasa gara na qara wayarmuna dakai mu mazan. Wasu kance lafiya kalau suka fita gida amma haka kurum inya dawo sai yaga matar ta hade fuska, rai a6ace, ko suna zaune ana hira yaga ta canza, ya rasa gane kanta, nan da nan sai fushi, ko akwai wata larura ne dana sani a likitance dake jawo hakan?
A karshe tambaya daya nakan musu ko tana da juna biyu? Sai kaji ance eh amma de ai yan satuttuka ne, kurum de ni inaga wulakanci ne... wato ran maza ya 6aci๐
★★★★
Sam ba larura gareta ba, ba kuma wulakanci bane... Mood swings muke kiransa, caccanzawar dabi'u, abune dake faruwa kai tsaye game juna biyu tun ma ba cikin fari ba, saboda canje-canjen da jikinta kan samu, ita kanta bata da ikon hana kanta 6acin ran, saide in anyi muwafaka mutum ce mai yawan barkwanci kuma kaima mijin ya zamto kana da barkwancin.
Yaron ciki ne kuma farin shiga ce, don haka baya ga yawan cin magani da bata rai, zakaga tana fama da laulayi na yawan amai da tashin zuciya musamman a watanni uku na farko. Don haka nuna tausayawa kurum take bukata, kai akaima laifin amma dole kaine mai bada hakurin.
๐ญ๐ฎ๐ป๐๐ผ ๐ธ๐ ๐ธ๐ถ๐๐ฎ๐๐ฒ ๐ธ๐๐บ๐ฎ ๐ธ๐๐ถ ๐ฟ๐๐ธ๐ผ ๐ฑ๐ฎ ๐ฎ๐ฏ๐๐ฏ๐๐๐ฎ ๐ธ๐ฎ๐บ๐ฎ๐ฟ ๐ต๐ฎ๐ธ๐ฎ;
1-■ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐
Kamar yadda na fada abaya ciki nasa yanayinsu ya canza, zaka iya fita ka barta lfy amma ka dawo kaga ta daure fuska kamar me, koma ta rika ma wasu abubuwa na 6acin rai, agaskiya maigida sai kai hakuri tare da kai zuciya nesa, inba haka ba kunta rigima kenan kuma ba denawa zatai ba, har gara kai rarrashi yafi sauki.
2-■ ๐๐๐๐ ๐๐๐ ๐๐๐ ๐๐๐๐๐
๐๐๐๐๐๐
Kana iya nemanta a shimfidarka taki, saboda kurum bata cikin yanayi me kyau sakamakon hormonal fluctuation, karka matsa dolen dole, don za'a iya samun matsala... karika hakuri tare da bin ta cikin hikima da dabaru (ka iya sayo kayan kwalama kila a saito ta), Saboda inka tilasta ko kace zaka sa karfi ko iko toh in bakin ciki da takaicinka ya rika shiga ranta saboda turasasata abu da kake kwai babbar matsala gami da barazana ga juna biyun.
3-■ ๐๐ ๐๐๐๐
๐๐
๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐๐
Akan basu sinadaran multivitamins, folic acids, calcium da iron... domin abubuwa ne masu mahimmanci ga kowacce irin Mace mai juna biyu, saide wasu kan wasa dashi koma suqi sha kwata-kwata wanda wannan ba karamin kuskure bane shyasa ake haifo wasu yaran da tawayar halitta.
Wadannan sindare ayanzu sune akan amfani dasu ga mai juna biyu musamman wadanda jininsu ke hawa wato hawan jini yayin goyon ciki (๐๐ฆ๐ด๐ต๐ข๐ต๐ช๐ฐ๐ฏ๐ข๐ญ ๐ฉ๐บ๐ฑ๐ฆ๐ณ๐ต๐ฆ๐ฏ๐ด๐ช๐ฐ๐ฏ)... supplements kadai sun isa sui control na Bp din nata daga wata 1 har zuwa 5 ko 6 na ciki batare da bukatar amfani da magungunan hawan jini ba galibi.
Sinadarai ne da zasu taimaka jariri yai cikakken girman da akeso, yai lafiya, yai kyau, tare da ba jaririn kariya daga samun nakasa irin wacce akan haifi jirajirai da ita.
4-■ ๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐
Ana bukatar mai juna biyu ta rika samun isashshen bacci akalla na awa 7 zuwa 9 arana, duk da idan ciki ya gabato watan haihuwa wato watanni 9 na karshe yawan zulumi, tunani, fargaba, da kuma canzawar sinadaran halitta (Hormones) na hana samun isashshen bacci.
5-■ ๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐
Ka tsaya kaida kanka kuyi tare da hankali kake sata tana motsa jiki inkaga bata da kuzarin yi, Babu girman kai, sai 6ata kudi kuke kuna kallon film din fararen fata amma bakwa koyar komi wajen irin wannan... ๐ฉ๐'๐ ๐๐๐ ๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐๐ ace koya abu yake saide kisa yara, haka zaike sa miki tsamin jiki, yawan gajiya da kasala. In takaice miki motsa jiki da yin ayyuka zaisa ki yaki abubuwa da yawa ciki hadda yawan tunani da damuwa, ciwon jiki, yawan fushi, karancin bacci da kuma hanaki yin nauyin da zai cutar dake.
6-■ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐'๐ ๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐
Bamu hana ai jima'i ba lokacin goyon ciki, babu matsala in har an tabbatar Mace bata cikin hatsarin komi wato ko ina mahaifarta lafiya take, babu barazanar zubewar ciki, kuma bakin mahaifarta antabbatar mai zurfi ne wato (๐ณ๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐).
Domin kwai mata masu yawan bari (miscarriage) adalilin kurararre ko gajeren bakin mahaifa wato (๐ฌ๐ก๐จ๐ซ๐ญ ๐๐๐ซ๐ฏ๐ข๐ฑ) wanda da ya wargaje ciki ke fita kunga irin wannan jima'i dasu hatsari ne batare da tuntu6ar likita ba.
Amma inde antabbatar babu wani hatsari, lafiya kalau Mace take toh shikenan, saide duk da haka kada a tsananta jima'i fiye da sau 2 zuwa 3 asati yayin da ciki yake sabo wato satin farko zuwa sati 12 (watanni ukun farko), daga nan shikenan
Haka zalik nasha fada abaya salon jima'i wato (poses) lokacin goyon ciki ba daya bane da sanda babu ciki, domin akwai pose din da bamaso saboda hatsarinsa. Banda ruf da ciki adoramata nauyi amara sosai.
Sannan bama son ake gwadawa mai juna biyu karfi. Sannan bamaso take kwanciya rigingine ta gadon bayanta. Domin hakan nasa nauyin ciki danne jijiyar jinin dake maida jini zuciya wanda hakan zai iya sa numfashinta ya dauke ta shiga mawuyacin hali tunda jima'i kansa EXERCISE ne yasa hatta Blood pressure ya karu, shyasa wasu har zufa suke.
Inya kama dole saita kwanta rigine to a tabbatar ansa matashi wajen kanta ya zamto de kamar a 90⁰ take... sannan akesa hannu adogare gefe da gefe ba adoramata duk nauyi ajika ba ksmat yadda nace, haka zaku iya jaraba ta hanyar yin goho, ko juya ya zamo kaine ka kwanta ita a samanka.
7-■ ๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐
A matsayinka na maigida munso ka rika rako mace zuwa awo asibiti, koda ba ko yaushe ba amma de ace akalla ko sau 1 ko 2 ka ta6a hakan, domin yin hakan na bamu karfin guiwar yima bayani wanda zai sa ahaifa lafiyayyen yaro musamman idan ka kasance miji nagari, wanda ya damu da lafiyar iyalinsa.
8-■ ๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐
๐๐
๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐
Munso ta Rika sanya kaya masu saukin nauyi, musamman lokutan zafi, kada kike yawan hada zufa, kuma take zama a muhalli mai ventilation koda babu fanka. Ki kuma rika zama aguri mai karancin hayaniya ko karar abubuwa. Haka banda sanya matsatsun tufafi masu kama jiki.
9-■ ๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐
๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐
Kula da tsafta, munason Mace mai tsafta ko wajen awo zakuga ma'aikatan mu sunfi jansu ajika, domin hakan na karawa mace lafiya, itama bazatake shayin shiga ko ina ba, kuma galibi baka samun mata masu tsafta da infection.. itako mai juna biyu farjinta saida tsafta gaskiya domin yafi ko ina datti jikinta, kwarai kuwa ko dubura batakai gabanta hatsarin cuttuka ba shiyasa mukeson tsafta. In mukaga matsala shyasa bama bari wasu matan su haihu da kansu saide muce ai aiki acire... hakan shine masalahar inba haka ba wasu jaririn abunda ke sa su mutu kenan takaitaccen lokaci ko kwanaki bayan haihuwa, wanda kuma suka rayu suita fama da ciwon ido. Wannan yasa tsafta duniya ce.
10-■ ๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐๐
A Matsayinka na maigida duk da munce ta rika motsa jiki amma muna so arika taimakawa wajen rage mata dawainiya, musamaman inba cikin fari ban4 dama akwai yara... saboda ta yiwu kakesata wasu ayyuka da ada bata gazawa amma yanzu ya zamto ta kasa har ta rika cewa saide ma kai kanka kai mata kaza da kaza, kota rika nuna kasala inkace tai wani abun... karka dauka wulakanci ne ko rashin jin magana ne, har ka rika fushi kana daga murya dole sai kai hakuri.
11-■ ๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐
๐๐๐๐๐๐
Ka sani suna da yawan fitsari musamman inciki ya fara girma sosai saboda danne mafitsara da mahaifa kanyi hakan nasa koya fitsari ya taru sai sun tashi sunyi... don haka kar kuna hira kaga duk minti 30 ta atashi da sauri ta nufi bandaki ka rika mata hayaniya. Bamason haka.
12-■ ๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐๐
Ka rika debe mata kewa, Eh mana! Kaima ka rika kwaikwayonta inkuna zaune irin kaima kana da ciki. Koma ka debo zannuwa ka cusa aciki kaima. Ko kuma de wasu abubuwa da zasuke sata yawan dariya da murmushi hakan na taimakawa wajen aborting din yawan fushinta ko yawan canzawar yanayi ko fuskarta.
Ko ka rika cewa wannan ne? Kana nuna cikin, kace dauko sukundireba kurum ahudashi ki huta, ai nima likita ne๐ Hakan zaike yaye damuwa da fushi, domin idan Mace mai ciki na fushi tohfa jaririn ma fushi yake...., karka yadda a haifoma jaririn da zaizo yana daure fuska yana jin haushin kowa.
13-■ ๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐
Masu juna biyu kan tsargu in suna kallon madubi, musamman inkai dace da mace yar kwalliya me tsafta, suna kallon fuskarsu su kasance cikin rashin jin dadi saboda duhun da sukanyi na fata, ga stretch marks, ga jikinsu ya bude sunyi kiba, dade sauransu
Don haka matsayinka na maigida, munso ka daure ka rika tunasar da ita ko yaushe cewa nifa ras nake kallonki tamkar randa aka kawonke, Gaskiya ke kyakkyawa ce, ke benu ce bakya tsufa, Gaskiya na mori mace.... haka de ka rika dan wasata hakan zai hanata zamowa depressed domin tabbas juna biyu ba'a rasa da damuwa. dashi da damuwa hannu da hannu suke tafiya amma inka tsaya mata toh zata haihu lafiya, zata sami kuzari ta yadda da wuya tazo haihuwa ace sai anmata aiki da ikon Allah inde komi ya tafi lafiya.
14-■ ๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐
๐๐
๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐
Ka rika taimakonta yayin laulayi abunda muke kira morning sickness... yawan amai, tashin zuciya, kasala, rashin son kamshi, da saka wahalhalu sayo kaza da kaza (yalo, goriba, magarya, ice cream, agwaluma,) da sauransu.
Banda kyararta cewa ke wlh kazamiya ce, sai tofe-tofen miyau, ga wanke-wanke duk kinqi yi, da sauransu. Kuma inda hali ataimaketa da abunda ta roka saboda sukanji bukatar cin abubuwa barkatai abunda muke kira capricious appetite.
Haka arika samo mata fruits, kayan marmari irinsu; lemon 6awo, kankana, ayaba, cucumber, da sauransu. Saide banda barinta tana ciye-ciyen kayan zaki irinsu bournvita, ovaltine, chocolates, shan sugar, sweets da sauransu ko yaushe.
15-■ ๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐
A matsayinka na maigida ka sakar mata fuska, ka kuma buda mata kofar komi akan take tambayarka, Banda wulakanci ko azabtar da mace da yunwa Allah ma bqzai barka ba, ka sani bukatuwarsu ga abinci kan karu musamman in sun shiga watanni ukun karshe na goyon ciki, Ka tuna fa bacci take amma Allah yake halittar mutum acikinta ai abuj tausayi ce. Gashi nan kai atini kake kashi mai tauri amma kaita nishi kana zare ido abandaki kaji wuya..
Ka kuma rika bata tabbacin komi lafiya, musamman masu juna biyu akaron farko tunda basanin abubuwa sukai ba sukan firgita koya abu yake, sukan yi kokonto ko yaya jaririn, sukan rika zullumin ko zan iya haihuwa dakaina oho, ko kuwa aiki za aimun oho, ko mutuwa ma zan oho... Haka de, ko yaushe ka rika ce mata lafiya zaki haihu da ikon Allah.
★★★
Wadannan sune ababe 15 da zaku taimaka dasu angwaye ko kuwa masu gidaje ga matanku yayin goyon ciki. Allah kuma ya raba lafiya. ๐จ๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐ ๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐, ๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐ ๐
๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐ ๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐จ๐๐๐
[๐๐๐ซ๐๐ก๐ข๐ฆ ๐. ๐๐ฎ๐ฌ๐ฎ๐]
0 Comments