🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Abune me mahimmanci da yanzu iyaye da yawa sun farga sun fahimci amfaninsa duk da abaya da yawa kanga kamar akwai cutarwa ace anhana jariri ruwa ko abinci na tsawon kwanaki 180 saide zallar nono...
Saide sam ba haka abun yake ba. Babu cutarwa game da jariri koda kuwa a lokacin zafi ne... domin duk abunda yake bukata tsawon watanni shida din nan akwaisa acikin nono.
Nonon uwa ya kunshi:
■ Ruwa,
■ Lafiyayyen kitse,
■ Vitamin,
■ Abinci me gina jiki (Carbohydrates),
■ Abinci me sanya kuzari (proteins),
■ kayan marmari,
■ Minerals gami da;
■ Duk abubuwan da jiki ke bukata domin samun inganci wanda bature ke kira da Six Classes of food.
Hasali ma shayarwa game da baiwa yaro ruwa shike cutar da jaririn. Domin ruwan na hanasa shan nono wadatacce wanda agaba akanga galibi yara sun rame, kai in akai rashin sa'a ma aka bashi ruwa me karancin tsafta daga nan jariri ya dinga fesa gudawa kenan saboda infection wanda akarshe hankalin kowa sai ya tashi, ga rashin samun isashshen bacci da za'aita fuskanta....
Amma shayar da nonon na kwanaki 180 zallah hakan nasa jariri ya sami duk abunda yake bukata, kuma zaike yawan bacci lafiya kalau ba rigima, kuma kema mahaifiyar hakan zaisa ki sami sukunin aikace-aikace kuma ki samu wadataccen ruwan nono... domin yawan shayarwa da kike na taka rawa sosai wajen sauri da kuma yawan tsatsafowar nonon.... yawan shayarwa baya zubar da nono.
Inkikaga kina shayarwa amma nononki na shrinking toh akwai wata larurar aboye tattare dake amma ba'a shayarwa abun yake ba.
Sannan shayarwan kema kamar hutu ne gareki domin yakan hana saurin kara daukar ciki. Kuma zakiga jaririnki cikin koshin lafiya, yai kiba ya aje kumatu, zakiga arana akalla yana jiqe pampers sau 8 zuwa 11 saboda yawan fitsari....
Yawan fitsari a jariri alamace ta kyakkyawar shayarwa! Hakan na nuna yana samun abinci wadatacce. Amma ganin jariri na yawan zub da kwalla koda baya kuka alamace ta yunwa... nono baya isarsa.
Sannan yi masa Exclusive zai karama garkuwar jikinsa karfi, zai karesa daga cuttukan cancer, da karama masa kaifin kwakwalwa.....
Sannan inwata shida sun cika kada ake basa purewater, ruwan famfo ko ruwan rijiya har sai antafasa ruwan anbarsa ya huce... sai adura a flask ake bashi har zuwa sanda zai cika watanni 12 wato shekara 1 domin taimakawa jikinsa...
Daga shekara 1 shikenan a iya bashi ruwa batare da antafasa ba. Saboda alokacin garkuwar jikinsa tai karfi. Kuma in ankiyayye wannan da wuya asami jariri na gudawa ballantana ciwon yunwa wato malnutrition......
Atakaice de shayar da yaro nono zallah batare da ruwa ko abincin ba tsawon kwanaki 180 wata 6 yana da matukar mahimmanci ga jariri, mahaifiya, iyali, da kuma duk unguwa ko garinku baki daya domin za'a sami lafiyayyun ya'ya.
0 Comments