MENENE CIWON SANYI (INFECTION) ❓
Amsa:
Ita cutar ciwon sanyi wata kwayar cuta CE ta bacteria ke haddasata, wacce turawa suke kiranta da suna (Neisseria Ghonorea), sannan ita wannan cuta tana rayuwa ne a waje me damshi a jikin dan-adam mace👩🏻 ko namiji👨🏻. Ba wai don an kirata da ciwon sanyi hakan yana nufin sanyi na yanayin duniya ke kawota ba! Ah a❌ an kirata da ciwon sanyine sbd ita cutar gun jiqa/damshi take zama a jikin DAN-ADAM. Misalin inda cutar take zama:
1. Farji=farjin mace wani kogo ne da baya rabuwa da jiqa/damshi, shiyasa da zarar cutar ta shiga ciki sai tayi wahalar fita ko warkewa.
2. Mahaifa/mafi tsara=duka wadannan wurare basa rabuwa da damshi.
HALAMOMIN CIWON SANYI (INFECTION);
Manya-manyan halamominsa sun hada da;
1. Jin ciwo ko zafi😭yayin fitsari
2. Fitar farin ruwa kamar maniyyi ga namiji👨🏻 ga mata👩🏻 me kauri kamar koko, ko kamu, me wari😷 ko me qarni🙊 ko marar ko daya daga cikin biyu. Turawa na kiransa da (GLEET).
3. Qaiqayin farji ko qurarraji, ko rajewarsa, ko jin zafinsa musamman lokacin jima'i
4. Kumburin "ya" yan marena ga maza👨🏻
5. Rashin jin cikakkiyar gamsuwa lokacin jima'i.
Saidai wasu bata nuna musu da kowacce irin alama, sannan baza a iya gane cewa tana da ita ba ko bata da ita ba, saidai in an je asibiti an yi gwaji a kan hakan. Sannan ita wannan wacce bata nuna alama tafi bada matsala sosai musamman in ta Dade a jiki ba a ankare ba.
MATSALAR DA WANNAN CUTA TAKE HAIFARWA GA MATA DA MAZA👩🏻👨🏻
1. Matsalar rashin haihuwa ta hanyar kassara kwayoyin da ke Samar da ciki, sai kaga mace👩🏻 ta qi haihuwa.
2. Tana haddasa wani ciwon ido me suna (Opthalmia Neonatorum) ga jarirai, Wanda mace me ciki kan iya gogawa yaro ta hanyar fitowarsa ta farji, tunda dama nace cutar tana zama a mafitsara da sauransu.
3. Tana sa zubar chiki/6ari.
4. Raunin qarfin mazaquta da zubar farin ruwa.
Tabbas ciwon sanyi na mata👩🏻 da maza👨🏻 babbar matsala CE ga rayuwar dan-adam, har ma takan yi barazana ta fuskar auratayya. sannan ita wannan cutar takan kamata wasu daga cikin sassan jikin mutum. Nah sha jin wasu masu tallen maganin gargajiya; suna ta yada qarya da qarerayi cewa: wai ciwon sanyi, sanyine na qorama, ko na ruwa, ko na damshi. Wai shi ke haddasa wannan ciwo na sanyi (INFECTION), Wanda kuma ba haka bane, qarya suke yi, suna fadan hakan ne kawai domin kasuwancinsu ya yi armashi ga jahilai wadanda basu sani ba, domin kai daga jin irin wannan talla kai ka San babu bincike a cikin tsarin. Suna yada jita-jita ne kawai labarin qanzon kurege, kuma Allah zai iya kamasu da laifin yada qarya a kan abinda basu yi bincike a kai ba. Ita dai wannan cuta ta sanyi (Wato Infection) akwai hanyoyin da ake daukarta kamar haka:
HANYOYIN DAUKAR CIWON SANYI (INFECTION):
1. Sex= hanyar da aka fi saurin daukarta shine yin jima'i (sex) da Wanda yake da ciwon sanyin mace👩🏻 ko namiji👨🏻 idan kai baka da ciwon in har ka yi jima'i da me ciwon sai ka/ki kamu, shiyasa ake son a dinga gwaji kafin a yi aure ko qarin aure ga maza masu auren mata sama da daya.
2. Shiga bayandakin da yake da qazanta, kokuma Wanda kowa da kowa yake shiga, misali kamar gidan wanka na kasuwa (Public Toilet).
3. Shigar baqin aljani👹 (jinnul ashiq)jikin mace👩🏻 ko shigar baqar aljanah👩🏿 jikin namiji👨🏻 musamman in suna zuwa muku a mafarki suna yin jima'i da ke/kai👨🏻👩🏻 zasu iya sa ma wannan kwayar bacteria din ta ciwon sanyi (infection) sbd suna👹👩🏿 jima'i da mutane kacha-kacha a cikin barci, zasu iya dakko wa a jikin wata/wani su sa ma/miki👩🏻👨🏻
To a taqaice dai wannan shine hanyar da aka fi saurin kamuwa da ciwon sanyi (infection).
CIWON SANYI NA MATA👩🏻 DA MAZA👨🏻
CUTAR P.I.D (PELVIC IMFLEMMATORY DISEASE) GA MATA👩🏻
to wai wace cuta ce p.I.d? Sannan ya ake kamuwa da ita? sannan wace illa take ma mata👩🏻? Kuma menene matakan kariya❓
P.I.D Cutar dake shafar mahaifar mace👩🏻, madaukan mahaifa, da kwayoyin halittar ta (ovaries).
P.I.D na nufin Pelvic imflammatory disease. Sau da yawa mata👩🏻 kanje asbt idan lalura na damunsu, sai suji likita yana ce musu suna fama da P.I.D.ko kuma sunki samun ciki ko suna ta 6ari (miscarriage), sai ace ai P.I.D garesu. To wannan ne yasa nace to bara nai karin haske akan wannan cutar kowa ma ya santa.
MECECE CUTAR P.I.D KUMA YA TAKE❓
Wato P.I.D wata nau'in cuta ce dake kama mahifar mata👩🏻 kadai, sakamakon yaduwar kwayoyin cutar bacteria na saduwa wato S.T.I (sexual transmitted infection), a hausa kwayoyin cuta da ake dauka ta hanyar saduwa, ita wannan cuta tana faruwa ne sakamakon faruwar cutar sanyi ta ghonoria, (wato cutar da ake dauka ta saduwa ba ta sanyi na yanayin gari ko na ruwan sama ba❌). Ko kuma cutar chlymidia, ko candidiasis, da sauransu, Wadanda sukan rayu ne a waje me danshi kmr mahaifa da farjin mace. to idan su wadannan cutar misali ta ghonoria mace👩🏻 na dauke da ita sannan ba'ayi maganinta ba, to takan yadu ta bar farjin mace👩🏻 sai ta gangara mahifa, sai ta illata madaukan mahaifa ko (pollofian tube) ko kuma ta illata ita kanta mahaifar ko kuma ta illata su kwayoyin haihuwar mace(ovarries). To sakamakon tashi da tayi daga farji zuwa mahifa to tabar nau'in kwayoyin cutar saduwa ta koma P.I.D. Daga nan se mace👩🏻 ta fara jin wadannan alamun
1. zafi yayin fitsari ko kuma yin fitsari dan kadan.
2. Zazzabi
3. Zafi yayin saduwa(sex)
4. yawan yin al'ada cikin wata takan iya yi sau 2-3
5. fitar farin ruwa marar dadi me wari.
6. Ciwon mara
7. Idan yayi karfi yana hifar da ciwon baya me tsanani
Sannan idan suka jima ajikin mace sukan haifar da 6arin ciki,(misschariage)rashin haihuwa (infertility) da sauransu. Sbd haka wadan nan sune alamomin cutar ta p.I.d sannan wasu matan ma bazasu ji wadannan alamun ba musamman idan cutar chlamydia ta haifar da shi P.I.D din.
Babban hanyar kariya shine
1.Da zarar anga kuraje ko anji kaikayi ko fitr farin ruwa a farji a garzya anemi magana Dan ciwo babba Ba karami
2. Mata su dena saka pant me lema sbd su kwayoyin cutar irin su candida albicans su suna alaka da damshi ne se su shigi mace👩🏻 su kawo mtslr
3.A rinka sanin yanayin da za a sadu da namiji👨🏻 ba saduwa da maza barkatai ba masu neman mata.
4. A kiyaye yin madigo (lesbin) sbd ana saka cutar ta dan yatsa wajen fingering🤘🏻 da sukeyi👩🏻👩🏻
5. A rinka tsaftace inda ake fitsari ko da garin gishiri ko isol ko da ruwa kamun ai fitsari
6.Sannan a dena saka dan yatsa a farji ba tare da an tabbatar da tsaftar yatsan ba👆🏻 dan shima yakan saka cutar D.S.S. in yatsan ba a wanke yake ba👆🏻Dan wlh ayanxu bbu abinda yapi damun Mata👩🏻 Kamar wannan ciwo😭 dolene ya sa iyayena mata👩🏻 ku tashi ku nemi magani🍵💊 a inda ya dace a kuma gun Wanda ya dace, Domin ku kare kanku Daga wannan ciwo. P.I.D.
SHAWARA A KAN CIWON SANYI NA MATA👩🏻 DA MAZA👨🏻
FITA TA UKU 3⃣
SHAWARA GAREKU MATA👩🏻 IYAYEN KOWA👏🏻
Zan yi bayani ko zan bawa mata👩🏻 iyayena wata Yar shawara game da lafiyar farjinsu.
Farjin mace👩🏻 tamkar idanu👀 yake baya buqatar kowanne irin baqo, wannan Abu yana cimin tuwo a kwarya😡 sai kaga mace har mace👩🏻 amma bata San yadda zata kiyaye lafiyar farjinta ba😭 hakan ya sa matan wannan zamanin basu da aiki sai Neman maganin mata da shiga bokaye👺. Rashin tsaftar farji ko kiyaye lafiyar farji kadai ma shine muhimmi wajen sanadiyyar mutuwar aure a wannan zamanin. A taqaice dai yah ke uwata kuma yayata👩🏻 INA son ki sani cewa Allah ya miki wata baiwa🎁 banda ke👩🏻 babu wata Halitta da take da irin baiwar ki ya ke uwata mace👩🏻 kar fa ki manta cewa duk sarauta👳🏻 ko mulkin namiji👨🏻 ko kudinsa💰 ke duk daukakar da Allah ya masa ke kadai kike iya sarrafashi kamar yadda kike sarrafa wayar salularki📲 amma fa ki sani hawa doki🏇🏻 iyawane, in baki koya ba wallahy fadowa zaki yi👩🏻 ki ji ciwo😭
Kowacce mace👩🏻 a duniya da dadinta Allah ya halicceta👩🏻 Namiji👨🏻 baida wani dadi 👎🏻 kece me baiwar dadi a jikinki ba namiji ba👎🏻👨🏻 ❗
Ya aka yi kika bari dadin ki ya ku6uce miki sister👩🏻 na😭❓
KURAKURANKI👩🏻 GAME DA FARJINKI
1. Ba a sa kumfar sabulu kowanne iri ne a cikin farji🚫
2. Ba a chusa kwa6a66en magani ko wani gari a cikin farji❌
3. Maganar gsky ba kowanne Abu ake son ya shiga wannan kogin me daraja ba❌
MALAM MIYE MAFITA🙎🏻❓
Mafita dai aunty na 👩🏻 itace ki kiyaye saka wadannan 👆🏻👆🏻 abubuwan da na fada a sama.
TO MALAM👳🏻 DA ME ZAN DINGA KULA DA LAFIYAR FARJINA👩🏻❓
👳🏻AMSA:
1. KULLUM baki da ruwan yin tsarki face ruwan zafi.
2. Ba sai kin ji fitsari ba zaki dinga tsarki da shi, a qalla sau uku a rana banda tsarkin fitsari ma, iya na ruwan zafi haka kawai
3. Zaki iya sa gishiri, da kaninfari, da lalle ko gishiri kadai, ko kaninfari da Ruwan zafin kadai ma x OK, in kin tsantsame sai ki nemi farin muski da man kadanya ki shafe ciki da wajen farjinki👩🏻
Sannan mafi yawan mata basu iya sa ruwan zafin ma a farjin su ba❌
Ana son ki shiga cikin ruwan zafin ki bubbude qafafunki kaman me haihuwa👩🏻 sai ki sa yatsarki👆🏻
Me tsayin nan (wato manuniya👆🏻) ki dinga kwakwalo cikin farjin kuma kina tura ruwan zafin yana shiga, ta yadda zai wanko annakiyar da ta maqale a cikin farjinki👩🏻 wannan shine tsarkin ruwan zafin da ake nufi, domin wasu don sun ji ance tsarkin ruwan zafi sai kaga sun dauki ruwan zafi a buta kawai su tsuguna su wawwatsa ruwan fat-fat a saman farjinsu su tashi tsaye to ba haka ake nufi ba mamana👩🏻 shi wanchan da ban ne.
Don Allah ki gwada ko na yini daya ne ki bani labarin yadda kika ji auntyna👏🏻👳🏻.
+2348037538596 or m+2348066627317
MATAKAI GUDA UKU DOMIN MAGANIN CIWON SANYI INFECTION GA MATA👩🏻 DA MAZA👨🏻
Ganin yadda cutar take da wahalar Magani Yasa Na Ce barin Baku hanyar da zaku bi Ku rabu da Ita gabadaya inshaaAllahu.
1. A nemi wadannan abubuwa kamar haka:
1-Khurunjal
2-Dammul-akhawaan
3-Qudnuful
4-Zanjabil
5-Ful-ful
6-ikhlilul-jabal
7-Daqiqul-Thawm
8-Habbatussaudah
9-Habbaturrashad
10-Hulbah
11-Na'ah-Na'a
12-Asalin furen Albabunaj🌻
13-Asalin itacen sazabu
14-Asalin Ganyen zaytun🍃
15-"Ya"Yan majamfari sai a soya Su a dake Su Su zama gari.
Wadannan abubuwa da Na lissafo ana son a dake Su gabadaya Su zama gari sosai sai a dinga diban tea spoon ana zubawa a Ruwa karamin cup Daya sai a dafa in ya tafasa sai a sauke a Sa Zuma daidai gwargwadon yadda zakin Zai fito yadda za a Ji dadin sha kaman shayi☕ safe da yamma, in kuma yayi Tsanani a jikin mutum toh ya dinga sha sau Uku a kowacce rana, ana son a kai tsawon sati Biyu a Jere ne ana sha, inshaaAllahu Zai kashe Na cikin yadda ya kamata.
MATAKI NA BIYU DON MAGANCE CIWON SANYI (INFECTION) WANDA YA ADDABI CIKIN FARJI GA MATA👩🏻👩🏻👩🏻:
A nemi wadannan abubuwa kamar haka:
Ganyen lalle Wanda bai zama gari sosai Ba
Yayan hulbah
Kwallayen tafarnuwa
Kaninfari
Ganyen magarya🍃
Ganyen zaytun Na Asalin🍃
Sai a hadasu GU Daya a dinga diba cikin Babban chokalin cin shinkafa biyu, Ruwa liter Biyu sai a dafa ya tafasa sai a juye a baho, in ya Dan huce yadda bazai cutar da ke Ba sai ki nemi ruwan khal tiffa, ba kowanne irin khal ake so ba, asalin khal tuffah me hoton Appke shi xaki nema, sai ki zuba chokali takwas a cikin ruwan, sannan sai ki cire wando ki shiga Ciki ki zauna tsawon mintuna 10 kina Ciki kuma ki wanke yatsanki👉🏻 ki dinga wanko ciki da ruwan maganin, amma in ke budurwa ce kar ki sa yatsa, kuma ki tabbatar kin aske Gashin Gaba Sbd ruwan Maganin ya samu damar ratsa pussy Ciki da waje sosai, Bayan kin fito sai ki nemi muski me Kyau da man zaytun me Kyau ki dangwala da auduga sai ki Yi matsi da shi, Bayan kaman awa Uku sai ki cire audugar, sannan Bayan awa Biyu da cire Audugar kina iya kara dafa wannan Maganin ki kara shiga ki kuma yin matsin again, son samu ki dinga yin wannan sit-birth din sau Uku ko Biyu a kowacce rana, inshaaAllahu dukkan matsalolin da infection ya Sa miki a farji misali kaman tsagewar farji ko kuraje, ko wari, ko zubar Farin Ruwa inshaaAllahu duk Zaki rabu da Su cikin ikon Allah, kuma Zaki Ji gun yayi Dadi kuma ya zama daidai Ba Matsalar komi.
In kuma Namiji ne👨🏻 shi Ba sit-birth Zai dinga Yi Ba, shi kawai ana son ya Hada Na sha din kuma Yana Yawan tsarki da ruwan Zafi sau Biyu a rana.
MATAKAN DA YA KAMATA A DAUKA DON KIYAYEWA KAR A KAMUWA DA CUTAR:
1. Idan Ku ma'aurata ne💑 ana son Ku dakata da yin jima'i har sai kun gama Maganin tsawon sati Biyu a jere.
2. Idan kina da Miji to dole tare zaku sha Maganin
3. In kina da Kishiyoyi Dole Ku sha Magani tare
4. Gyara bandaki da barbada Gishiri a cikinsa lokacin da za a wanke shi
5. Ki wanke pant Dinki da ruwan Gishiri Bayan kin wanke da omo ko sabulu sai ki jika ruwan Gishiri da ruwan Zafi ki tsoma duka pant Dinki a ciki su kai mintuna goma sai ki cire ki shanya su a rana, in da hali kuma kawai ki Sayi sabbi ki watsar da wadanchan.
6.kiyaye shiga toilet din da kowa da kowa ke Iya shiga ya Biya bukatarsa musamman a Gidan biki ko Kasuwa (Public toilet).
7. Yawan tsarki da ruwan Zafi akai-akai.
InshaaAllahu idai am Yi amfani da wannan hanyoyi za a rabu da Ciwon Sanyi infection kwata-kwata da yardar Allah👆🏻
MAGANIN CIWON SANYI (INFECTION NA MATA👩🏻👩🏻👩🏻 DA MAZA👨🏻👨🏻👨🏻
=====================================
======================
Bismillahirrahmanirrahim!
Idan aka Ce sanyi ba wai ana nufin sanyi Na hunturu ko sanyi Na Ruwan sanyi, ko sanyi Na yanayi shine ke sa Ciwon sanyi ba! No! Sanyi Na farji😁 ake nufi, in ance sanyi Na farji ba wai ana nufin farji yayi sanyi ba😀 No! Dalilin da yasa ake cewa Ciwon sanyi ko Sanyin gaba shine: kwayar cutar Bacteria din tafi zama a Waje me jika kamar farjin mace kenan👩🏻 kaga ai shi farjin mace a bude yake👩🏻 kuma baya rabuwa da jika kokuma damshi, saboda haka in cutar ta shiga take da wuyar warkewa/Magani.
**********************************************
RARRABUWAR CIWON SANYI
-----------------------------------------------------------------------
1. Sanyi Na yanayi, shine me sa matsalolin huhu (lungs). Kamar mura, tarin Asthma da sauransu,
2. Sanyin Qashi, shima ba Sanyin yanayi ke kawoshi, Amma shi gaigayewar tsakanin Ga6a da Ga6a ta cikin Qashi shine ake cewa Sanyin Qashi.
3. Sanyi Na farji shine: Infection kenan me zama wajen jiqa, kamar cikin bandaki inda Ruwa ke taruwa ko cikin farjin mace inda baya rabuwa da damshi.
ANA SAMUN CIWON SANYI INFECTION TA HANYOYI KAMAR HAKA
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
1. Bandakin da kowa da kowa ke shiga a Kasuwa ko wajen Sana'a ko gidan yawa (Public toilet)
2. Rashin tsaftar Bandakin kansa
3. Haramtaccen jima'i Zinace-Zinace da mata daban-daban👱🏻♀👩🏻👩🏽👧🏻
4. Luwadi Homoursexual ko madigo Lesbianism Allah ya sawwake👏🏻
5. Shigar bakin Aljani jinnul Ashiq👹 me zuwa a mafarki yana saduwa da mace👩🏻 domin kafin Ita qila Daga jikin wata aka masa ruqiyyah sannan ya dawo jikinta, ta yiyu inda ya bark matar👩🏻 nada Ciwon sanyi Dan haka kema yana iya sa miki, tunda ya zo a hadisi cikin littafin majmu'ul fatwah Na ibn taymiyyah cewa: wannan mafarkin da mace ke Yi Namiji Na saduwa da Ita ba shirmen mafarkin bane da gaske aljanine yake saduwa da ita👹👩🏻 domin in ta farka da zata kalli farjinta zata ga alama an ta6ata👩🏻 saboda haka dattin farjin bakin Aljani ba infection bama har H.I.V yana sawa mace🤔 kaga mace ba harkar BANZA take Yi ba Amma Sai ta wayi gari TANA da cutar H.I.V a rasa ya aka Yi 🤔
Kasancewar farjin mace👩🏻 a bude yake kuma baya rabuwa da damshi hakan yasa warkewarta yana da Wuya matuka indai ba wai an samu ingantaccen Magani ba, ba kamar farjin namiji👨🏻 ba a lullu6e🍌, domin bincike ya tabbatar da cewa Namiji shine ke daukar cutar ya sawa mace in ta hanyar sex ne, saidai kuma da ace Namiji zai dakata da yin jima'i Na sati daya tare da shan Magani💊 zai Warke da gaggawa fiye da mace👩🏻 saboda shi farjin sa a lullu6e yake🍌 ba a bude ha kamar Na mace👩🏻
ALAMOMIN CUTAR SANYI NA FARJI (INFECTION)
1. Fitar farin Ruwa Daga cikin farjin mace👩🏻 me kauri kamar dusar awara, ko kamar kamu, ko kamar koko, koda yana wari🙊 ko karni ko marar daya Daga Ciki.
2. Zafin farji yayin da aka Yi Yi ko ake Fitsari
3. Kaikayin farji ko fitar Kuraje masu kaikayi ko zafi da zugin farji musamman lokacin jima'i (Sex)💏
4. Kafewar farji tare da daukewar damshin farji (Flora) sannan da Ciwon Mara musamman in ana sex, da sauransu.
MAGANIN💊 KOWANNE IRIN CIWON SANYI NA FARJI MACE👩🏻 KO NAMIJI👨🏻
********************************************
Da farko dole Maganin ya zama Kashi biyu ne Na sha💊 da Na shiga Ciki (sit-birth) domin samun Samar kashe cutar Ciki da Waje.
MAGANIN💊 INFECTION NA CIKIN CIKI
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
A nemi wadannan abubuwa daidai misali
1. Danyar tafarnuwa (Garlic)
2. Kanunfari
3. Khurunjal
4. Ganyen Na'a-Na'a Busashshe
5. Zanjabil (cittah/Ginger)
6. Kajiji
7. Ganyen lalle Wanda ba a dakeshi ya zama gari sosai ba
8. Yayan Hulbah (Fenugreek)
9. Yayan habbaturrashad
10. Ganyen magarya
11. Ganyen Garahunu
Wadannan abubuwa Guda 11 sune za a nemosu a kintata adadinsu a hada GU daya a nemi Ruwa me kyau a dafa ya tafasa sosai Sai a tace a juye a flask, Sai a dinga diba A karamin kofi🍵 sai a Dan zubar Zuma kadan yadda zai Dan Yi zaqi kaman Shayi Sai a saisaita a sha safe da yamma Sau biyu a yini, in yayi tsanani Sau Uku a yini.
Wannan hadi ba Sanyin farji kadai ba har Sanyin Jiki me sa kumburin Jiki kuma yana tace jini sosai yana kuma kara lafiyar Jiki sosai.
MAGANIN CIWON SANYI NA CIKIN FARJI
Wadanchan abubuwan Guda 11 da aka lissafo don magamce Na cikin Ciki su za a nema again bambancin kawai shine Sai za a shiga Ciki sannan a dafa, kuma za a dafa ne daidai gwargwadon shiga cikin bahon, Sannan ana son a nemi Apple Veneger (Khall tiffah) Sai a dinga zubawa a cikin bahon kimanin babban chokali 6, sannan ana son a aske gashin gaba (shaving) sosai saboda lokacin da aka shiga Ruwan zagi ana son Ruwan Maganin ya shigeki sosai ya gasa naman farji Ciki da Waje, in da gashi a cunkushe kinga bazai bawa Ruwan zafin Dakar shiga farjinki yadda ya kamataba, kuma in kika shiga bahon ba zama zakiyi damasmasba kamar kin samu kujera😁 No! Tsumbuluwa ake son kiyi, ke Baki zaunaba ke Baki Fita ba, wato in kika zauna to mazaunenki zasu hana Ruwan zafin fenetrating cikin farjinki yadda ya KAMATA, saboda haka a gyara mata👩🏻. In kai Namiji ne kuma wanne bananar🍌 zaka dinga Yi da Ruwan Maganin, kar a manta Sau biyu ake tsarkin, kuma lokacin da za a Yi lokacin ake dafawa ya tafasa Sai a sauke in ya Dan huce ba gabadaya ba Sai a shiga, kullum Sau biyu, kwana Bakwai a Jere ba tsallakewa, kuma za a dakata da yin jima'i Na kwana Bakwai a Jere.
A kiyaye tsaftar bandaki, a kiyaye shiga toilet barkatai, a kiyaye zinace-zinace, a sha Magani tare da iyali👨👨👧👧 in ana da mata.
Wannan shine ingantaccen MaganiN Ciwon sanyi infection kowanne iri inshaaAllahu kuma Wanda ake warkewa gabadaya.
0 Comments