Ita ya mace a kullum Babu abunda yake jawo mata daraja irin kamun kanta.
Namiji ko Dan iska ne mace Mai kamun kai yake so idan ya tashi yin aure. Haka suma al'uma sunfi daure wa namiji gindin yin iskanci son ransa tunda yasan idan yazo neman aure za a bashi ba kamar mace da tana yin kuskure ko sakaci kadan zai shafi rayuwarta har abada.
Kamun kai zai yiwa mace wahala muddin tanada kwadayi.
Abunda zai hana mace kwadayi kuwa shine idan ta guji dogon buri da gasa na sai nayi abunda wacce tayi ko take da shi.
'Ya mace data fito daga gidan da babu wadata dole ne ta kiyaye mutuncinta ta hanyar kokarin neman na kanta da kuma kauracewa kawaye marasa daraja.
Ba mazan aure bane babu. Ba kuma mazan basa son yin auren bane. Rashin samun mace ta gari mai natsuwar da zasu aura a wasu lokutan sune abu mai wahala.
Da zaki kula da kyau, zaki ga wani gidan matansu har ribibin aurensu ake yi saboda irin natsuwa da tarbiyan da aka sheda gidan nasu da shi.
Don haka ki guji kwadayin abun hannun maza. Ki guji mu'amala da kawayen banza. Ki samu abun yi dai-dai gwargwado. Ki Kuma zauna da kowa lafiya zaki kasance cikin daraja da mutunci har lokacin da Allah Zai yi hukuncinSa akan ki.
#tsangayarnalam
#sirrinrikemiji
Share
0 Comments