BAYANI A KAN NAJASA
Abin da ake kira najasa shi ne duk wani abu da Shari'a ta yi hukunci a kansa cewa najasa ne. Irin wannan abun wajibi ne a kawar da shi daga jiki, tufafi da wurin da za a yi sallah da duk wata ibada da aka sharɗanta tsarki daga najasa a lokacin yin ta.
Asalin komai mai tsarki ne sai wanda Shari'a ta yi hukunci a kan cewa kaza da kaza najasa ne, su ne kamar:
1. Fitsarin mutum najasa ne. Wajibi a wanke shi daga tufafi, jiki, wurin mai sallah, amma an yi sassauci a kan fitsarin yaro wanda bai fara cin abinci ba. Idan aka yayyafa ruwa a kai, ya isa.
2. Kashin mutum najasa ne. Wajibi a wanke shi kafin a yi sallah daga tufafi da jiki da wuri.
3. Maziyyi najasa ne. Shi maziyyi wani ruwa ne mara kauri da yake fita a lokacin sha'awa ko tunanin jima'i ko shafar mace da makamantan su. Wajibi a wanke duk inda ya taɓa kafin a yi sallah, saboda hadisin da Manzon Allah ﷺ ya yi fatawa ga Sayyadina Aliyyu ya wanke gabansa sannan ya yi alwala.
عن علي - رضي الله عنه - قال: كنت رجلا مذّاءً ، فاستحييت أن أسأل رسول الله ﷺ لمكان ابنته منّي ، فأمرت المقداد ابن الأسود فسأله ، فقال: ((يغسل ذكره ويتوضّأ)) () وللبخاري: ((توضّأ واغسل ذكرك)) ولمسلم: ((توضّأ وانضح فرجك))
Ma’ana: “Ka wanke gabanka (tsarki) sai ka yi alwala.”
4. Wadiyyyi: Shi ma najasa ne. Kuma ruwa ne mai kauri yana fita a ƙarshen fitsari. Wajibi a wanke shi kafin a shiga sallah.
5. Jinin al'ada: Shi ma jinin al'ada najasa ne. Wajibi a wanke duk inda ya taɓa kafin a shiga sallah, saboda hadisin da ya zo cewa wata mata ta zo ta yiwa Manzon Allah ﷺ tambaya a kan jinin al’ada, sai ya ce:
((تحته ، ثمّ تقرصه بالماء ، ثمّ تنضحه ، ثمّ تصلي فيه)) ()
Ma’ana, “Ta kankare shi, sannan ta wanke shi da ruwa ta ɗauraye, sannan ta yi sallah da shi.”
6. Yawun bakin kare najasa ne. Idan ya taba jikin mutum ko tufansa ko wurin da zai yi sallah wajibi ne ya wanke kafin ya yi sallah, saboda hadisin Abu Huraira (رضي الله عنه) cewa:
((إذا شرب الكلب في إناء أحدكم فليغسلْه سبعًا، ولمسلم: أولاهن بالتراب)) ()
Ma’ana, “Idan kare ya yi lallage a cikin kwanon dayanku, ya wanke sau bakwai na farko ya sa qasa.”
7. Naman alade. Shi ma najansa ne. Wajibi a nisanta shi daga wuri da jiki da tufafin wanda zai yi sallah.
8. Mushe. Duk wani mushe najasa ne. Wajibi ne a nisanta mushe daga wajen sallah da jiki da tufafi sai kawai gawar mutum da kifi da fara da abin da ba shi da jini a jikinsa kamar tururuwa da sauro da tsutsa da sauran kwari; irin waɗannan an yi sauqi a kan su.
9. Abin da aka yanko daga jikin wata dabba mai rai, da ranta kafin a yanka. Wannan abin ko nama ko fata duka najasa ne, wajibi a nisance shi a lokacin sallah. Manzon Allah ﷺ Ya ce:
((ما قُطِع من البهيمة وهي حية فهو ميت)) ()
Ma’ana: “Duk abin da aka ciro daga jikin dabba alhalin tana da rai wannan abin najasa ne.”
10. Duk naman dabbar da aka haramta cin namanta, najasa ne. Wajibi a nisanci wannan naman, saboda hadisin Abu Ɗalha (رضي الله عنه) cewa Manzon Allah ﷺ ya umarce shi ya yi shela a lokacin Yaqin Khaibar cewa haƙiƙa Allah ﷻ da Manzonsa ﷺ sun hana cin naman jakin gida domin najasa ne.
11. Fitsari da kashin dabbar da aka hana cin namanta. Duk wata dabba da aka hana cin namanta a Shari'a wajibi a nisanci kashinta da fitsarinta a lokacin sallah domin najasa ne, amma duk dabbar da aka halatta cin namanta, kashinta ba najansa ba ne. (Mugniy na Ibn Qudamah da Majmu’u na Imamun Nawawiy.)
12. Maniyyi. Malamai sun yi saɓani a kan maniyyi najasa ne ko ba najasa ba ne, saboda an sami inda ake kankare shi daga jikin tufafi, da kuma inda aka wanke shi. Amma babu wata magana ta fili qarara da take tabbatar da cewa maniyyi najansa ne. Saboda abubuwa guda uku muka zabi maganar malaman da suka tafi a kan cewa ba najasa ba ne:
Dalili na ɗaya shi ne daga maniyyi aka yi mutum, shi kuwa mutum yana da daraja a wajan Allah. ﷻ Don haka bai halicce shi daga najasa ba.
Rashin dalili qarara daga Manzon Allah ﷺ da yake nuna najasar maniyyi kamar yadda aka samu a kan maziyyi.
Saɓanin da malamai suka yi a kan hukuncinsa, ya nuna tsarkinsa.
Allah ﷻ ne mafi sani.
13. Giya. Giya haramun ce shanta da amfani da ita ta kowacce hanya. Amma idan ta zuba a jikin mutum, zai wanke kafin ya yi sallah ko kuma a’a? Malamai sun yi saɓani a kan haka, amma maganar da ta fi qarfi da rinjaye shi ne giya najasa ce.
Mazhabobin Hanafiyyah, Malikiyyah, Shafi’iyyah, Hambaliyyah da Zahiriyyah su Ibn Haz’min sun tafi a kan cewa giya najasa ce.
Malam Dawud Azzahiri, Malam Rabeeatu, Malam Laisu, Imam Shaukani, Albani da Ibn Usaimeen duk sun tafi a kan cewa giya ba najasa ba ce, amma shan ta shi ne aka yi ittafaƙi a kan haramun ne.
14. Jini: Mun yi bayani a baya cewa jinin al'ada najasa ne, amma sauran jinanai kuwa akwai saɓani. Magana mafi rinjaye ba najasa ba ne, saboda dalilai masu yawa daga ciki akwai sahabin da aka harba yana sallah, ya ci gaba da sallah ga jini yana zuba daga jikinsa.
15. Kumallo wanda ya fara wari, ya jirkita daga abinci. Irin wannan kumallo ya zama najasa wajibi a wanke shi daga jiki ko tufafi ko wurin da za a yi sallah.
16. Wani ruwa da yake fitowa mata daga gabansu wanda suke kira (ruwan ni’ima). Irin wannan ruwa kazanta ne kawai amma ba najasa ba ne. Don haka idan ya fitowa mace za ta wanke shi domin tsafta kawai.
17. Ruwan kwatami wanda yake kwantawa ya dade har yana wari. Irin wannan ruwa najasa ne.
A cikin waɗannan bayanai za mu ga daga ciki a kwai abin da aka sami haɗuwar kan malamai cewa najasa ne da kuma abin da suka yi saɓani a kan cewa najasa ne ko ba najasa ba ne? Allah ﷻ Ya sa mu dace. Amin.
YADDA AKE GUSAR DA NAJASA.
Akwai hanyoyi da ake bi wajen kawar da najasa wanda Shari'a ta tanadar. Wata najasar wanke ta ake yi, wata kuwa goge ta ake yi, wata kuma yayyafa mata ruwa ake yi gwargwadon yadda najasar take. Wata najasar sai an wanke ta da ruwa sannan take fita, kamar kashi da fitsari idan suka taɓa jikin mutum ko tufafinsa, kamar yadda aka yi umarni a wanke tufar da jinin al'ada ya taɓa.
Fitsarin yaro idan ya taɓa tufafi sai a yayyafa ruwa a ɗauraye shi kenan ya isar. Kamar yadda ya zo a hadisin Abus Samhi (رضي الله عنه) ya ce:
((كنت أخدم النبي ﷺ فكان إذا أراد أن يغتسل قال: ((ولّني قفاك)) فأولّيه قفاي فأستره به، فأتي بحسن أوالحسين - رضي الله عنهما - فبال على صدره، فجئت أغسله ، فقال: ((يُغسَل من بول الجارية ، ويُرشّ من بول الغلام)) ()
Ma’ana: “Ana wanke fitsarin qaramar yarinya, sannan ana yayyafa ruwa a fitsarin qaramin yaro.”
Idan maziyyi ya taɓa tufafi sai a ɗebo ruwa a jiqa inda ya taɓa, ba sai an wanke shi ba kamar yadda ya zo a hadisin Sah’lu Bn Hunaif (رضي الله عنه) ya ce na tambayi Manzon Allah ﷺ a kan maziyyi sai ya ce:
((أنما يكفيك من ذلك الوضوء)) قلت: يارسول الله ، فكيف بما يصيب ثوبي منه؟ قال: ((يكفيك بأن تأخذ كفًّا من ماء فتنضحه بها من ثوبك حيث ترى أنه أصابه)) ()
Ma’ana: “Alwala kawai za ka yi.” Sai na ce, ya zan yi da bangaren da ya taba a jikin tufafina? Sai ya ce: “Ka ɗebi tafin hannu ɗaya na ruwa sai ka yayyafa a wuraren da ka ga alamunsa.”
Yadda ake tsarkake tufafin da suke jan ƙasa kamar hijab da zane. Idan aka ja zanen a wuri mai tsafta zai iya goge shi, idan najasar ba ɗanya ba ce. Kamar yadda ya zo a hadisi daga Ummus Salamah (رضي الله عنه) cewa wata mata ta tambaye ta game da jan tufafi a ƙasa (amma ga mata) sai ta ce Manzon Allah ﷺ Ya ce:
((يُطهِّره ما بعده)) ()
Ma’ana: “Abin da ke bayansa zai tsarkake shi.”
Idan mutum ya taka najasa da takalmi, sai ya goge a kan ƙasa ko yashi ko dukkan wuri mai tsarki, kamar yadda ya tabbata a hadisin Abu Hurairah (رضي الله عنه) ya ce: Manzon Allah ﷺ ya ce:
((إذا وطئ أحدكم بنعله الأذى ، فإن التراب له طهور)) ()
Ma’ana, “Idan dayanku ya taka ƙazanta da takalminsa, to ƙasa ce mai tsarkakewa a gare shi.”
Idan aka yi fitsari a kan ƙasa ko yashi da zarar an kwarara ruwa a wurin ya tsarkaka kamar yadda yazo a hadisin wanda ya yi fitsari a cikin masallaci, aka yi umarni a zuba ruwa a wurin.
Rijiyar da wata dabba ta mutu a ciki ko ɓera ya faɗa cikin jarkar mai ya mutu a ciki. Yadda za a yi shi ne a yashe iya inda ya faɗa idan man a daskare yake amma idan narkakke ne sai a zubar, saboda ya gauraye ko'ina. Ita kuwa rijiyar sai a yashe ta bayan an ɗauke abin da ya mutu a ciki.
Yadda ake tsarkake abin da kare ya saka baki ya zuba yawun bakinsa a ciki, sai a wanke sau bakwai na farko a zuba ƙasa a cuccuɗa.
Yadda ake tsarkake fatar mushe. An yarda a yi amfani da fatar mushe amma bayan an jeme ta da ruwa da bagaruwar jima kamar yadda ya tabbata.
Allah ya bamu ilmi mai amfani.
0 Comments