🗺🗺🗺🗺🗺🗺🗺🗺🗺🗺🗺🗺🗺🗺
Likita meke jawo kurji ne wato Boils musamman a hammatar mutum, ga zafi in anta6a. Wani lokacin ko ya warke sai kaga ya dawo?
✍🏼
Yawan cin hakan yafi faruwa a mutanen dake yawan zufa. Maza ko mata. A mata musamman masu kiba, a maza kuma musamman masu aikin karfi saboda matukar mutum zaiyi zufa yai sharkaf da gumi amma ya dauki lokaci bai wanka ba har ya bushe yaci gaba da harkokinsa kamar bai zufa ba toh tabbas hakan naba kwayoyin cuta na fata damar samun invading din fatar mutum su haddasa masa kurji.
Sai kuma! karancin tsafta ake barin hammata tana haura sama da sati 4 zuwa 6 batare da an aske ba alhalin mutum na aiki na kaikomo musamman arana ko dakin girki (kitchen)
Sai kuma raunin garkuwar jiki. Musamman a mutane masu cuttuka irinsu Ciwon suga, cancer, Hiv, da sauransu.
Musamman wanda ake shan magani yana 6acewa amma aga ya dawo walau a hammata ko a mazaunai... duk me ganin haka inyasan baida wata matsala toh ya daure yaje ai masa gwajin sugar ta iya yiwuwa yana da ciwon bai sani ba.
Sai kuma Abu na karshe induk bama wadannan din... shine rashin iya wanka, kamar yadda wasu basu iya tsarki ba. Ya zamto kana cuda soso ko ina ajika ba nazari. Ka kai soso ka gogo duburarka ko duburarki karshe ka dawo dashi ka cudo hammatarka... yin hakan kuskure ne.
Akwai dubunnan bacteria a dubura da ido baya iya gani kana dangwalo su a soso ka goga a hammata ko a farji shikenan infection ya samu. Don haka ko yaushe dubura itace karshe akomi.
Fatan za'a kiyaye.
0 Comments