Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: ☏+2348037538596
Sirrin rike miji
Sirrinrikemiji@gmail.com
Sirinrikemiji@gmail.com
☏+2348037538596
wannan karonma zanyi bayanin wani sirrin dafa kaza wanda idan har mace tayi zataga amfaninsa musamman amarya anaso kisamu bushashen ganyen magarya da kanunfari da idon zakara duk ki hadasu waje daya ki dakasu ki tankade su zama gari to idan kika samu:
budurwar kazar kika gyarata saiki zuba wannan garin acikin tukunyar sannan zaki iya zuba kayan miya yanda kikeso bayan ta dafu saiki cinye gaba daya yana saka gaban mace ya kumbura ya ciko da ni ima kuma yana karawa mace dandano sannan kowacce mace zata iyayi koda batada aure.
Halawa mai gyara fata...
Halawa wata aba ce da ake amfani da ita wurin gyaran fatar jiki ce. Wannan halawar an fi samunta a Jihar Barno. Akan hada ta musamman ga amare. Akan hada ta ne ta hanyar amfani da siga da lemun tsami da ruwa kadan. Wannan halawar na amfani wurin debe gashin fata domin ta yi sulbi da laushi.
Abubuwan da ake bukata:
· Cokali 3 na siga ko zuma
· Lemon tsami 3
· Ruwa cokali daya
Yadda ake hadawa:
A dora tukunya a murhu idan ta yi zafi sai a zuba siga ko zuma, idan siga ko zuma ta fara narkewa sai a zuba lemon tsami da ruwa kadan. Idan a murhun itace ne ake hada halawar to kada a bari wutar ta kama sosai, haka idan ma da risho ne ko na’urar gas cooker da sauransu. Domin kada ta kone. A yi ta gaurayawa zuwa minti 45 har sai hadin ya koma ruwan kasa, sannan a sauke. A jira ta huce. Za a ga ta yi danko. Sai a samu cokalin katako ko na roba a shafa a kan fata inda akwai gashin jiki. Bayan ya bushe, sai a sami tsumma a danna a kan fata sai a rika ciro ta. Yin hakan na fitar da gashin fata kuma za a ga fatar ta yi sulbi da santsi.
Sirrinrikemiji@gmail.com
Sirinrikemiji@gmail.com
☏+2348037538596
0 Comments