๐–๐€๐๐๐€๐ ๐‘๐€๐˜๐”๐–๐€๐‘ ๐“๐€๐Œ๐” ๐€ ๐˜๐€๐”:


Malama da bakinta matsayinta na Mace a lecture dinta take cewa; Wajibi mu fadwa kanmu gaskiya, kwai hadisi ingantacce da Annabi (SAW) ke cewa sauti biyu Allah ya la'ancesu inji annabi; 
- Tace daya daga ciki shine; duk wanda Allah yai masa ni'ima kuma yabi ni'imar nan da kida, ko ya sami wani cigaba arayuwa, ko cin jarabawa, ko kammala karatu, ko uwa uba aure! Hanyar da ake samun รฝaรฝana na sunnah.

Malama tace; Yau aurarrakin mu zaku ga duk sun koma na yahudu, babu dandanon addini, mu Matan ai kauyawa day, ai fulani day, ai mothers night, aiko wanne shirme da shirita.... abubuwa de gasunan na shirme da rashin hankali.

Shyasa matsalolin aure gasunan birjik, agama duk abunda za'ai karshe afara zaman aure kuita zagi da zargin juna tun ba'aje ko ina ba. Duk me hankali inya duba zaiga yayyen mu Mata wadanda akai aurensu daga 2005 abunda yai baya zuwa su 90's da 80's har yau kusan 80% dinsu suna gidan miji inbanda wadanda mazajen suka rasu. 

Amma daga yan 2009 zuwa yau zaka samu wadanda suka rage gidan auren basufi 32% ba, sake-sake na tsiya sun auku, kunga jawa kai mukai, domin me? Domin wadancan yayyen namu galibi duk da ba duk ba amma ankiyaye Allah, amma yau fito na fito ake a aurarrakin mu da ubangiji. Gashi abun babu alamun zaizo karshe nan kusa.

๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ

Malama ta qara da cewa Matsalar aurarrakin mu ayau Mata nada kaso 50 zuwa 60% na lalacewarta, tace su Matan ne matsalar ba Maza ba. domin addu'ar Mata kar6a66iya ce. Ke kuma duk sanda kika budi baki saide ki la'anci Mijinki, ko ki furta gazawarsa fiye da abunda zai taimaki auren, Bawai akan baya cutarki ba... eh mun kwai Maza azzalumai kuma shiyasa ma Allah yake kar6ar addu'ar taki ai. 

A lokacin da kike wannan muguwar addu'ar da addu'ar shiriya kike masa da rokon Allah yai masa budi wallahi da kaso 70 na matsalolin aure ayau an maganinsu.

๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ

Malama ta cigaba cewa; Hakika wasu matan an jarabacesu, suna auren Mazan da basusan menene aure ba, amma kuma cikin duk sunonin annabi wanda namiji yafiso shine auren. 

Duk mace nason namijin da inta dafa abinci xai ci yace ya gode, amma wanda bai san aure ba bazai ta6a cewa mace ya gode ba. Macen nason namijin da intai abu zaice Allah yai mata albarka, amma wanda baisan aure ba bazaita ta6a cewa matarsa Allah yai mata albarka ba, wallahi wani kila bai ta6a godewa matarsa ba, baya ado domin iyalinsa duk da Matan ma yanzu hakan muke kuma bakwa adon sai zaku fita unguwa mafi yawa. 

Haka wanda baisan aure ba shine zaka samu bazai ta6a cewa mace ta tashi tai addini ba ballantana รฝaรฝansa, harkokin gabansa kurum sune gabansa.

๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ๐Ÿ’ฎ

Tace in matsalolin sun taso kokari zaki ki zamo mai ibadah, kike tashi cikin dare ki sallolin nafila kikai kukanki gun Allah, shine ya halicci soyayya, shi ya nufeki da son wanda kika aura, kuma shi zai yaye miki kukanki, kai kara garesa. 

Sannan ki ฤamarar bin duk wata hanyar da zaki bi ki jawo hankalin mijinki gareki ta hanyar amfani da turare, tsafta, sanya irin kayan da yafiso, lura da inda yafi so ajikinki, kyauta da kuma yin irin dan abin ci da lashelashe. 

Musamman akwai irin mazan da agaban matansu ma chat da danne dannen waya suke ba ruwansu saboda yasan ba yadda kika iya dashi. 
Malama tace toh a irin wannan hali ba fada, kuka ko 6acin rai zaki koma kinayi ba, shiga zaki me kyau ki fesa turare sai ki dauko kwanon gullisuwarki ko tuwon madara kice a'ahh hira ake shane haka? Toh ga wannan..... ki bude masa murfin kwanon ya dauka, alokacin kamshin turaren kurum dazai bugesa... tuni zai sauya tunaninsa, karshenta daga nan zai rikoki ki zauna kusa dashi abunda da baya bari. 

Domin wani ko abinci saide yai nuni da asa yara su kawo masa ko kuwa in macen ta aje yace to jeki-jeki inna gama kyazo ki dau kwanon.

Wani namijin yanason kwalliya amma bazai ta6a iya saya matarsa ba. Gashi duk inda yaji ana wa'azi mace mai tsafta kaza da kaza yaita zagin tasa, amma zai iya saya budurwarsa can awaje kona nawa ne.

๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ

Son Mata da Maza keyi halittar mu ce haka, kuma sunnar mu ce, bazaki ta6a iya raba mijinki da Mata ba, bazai yiwu ba, gara ma ku kwantar da hankalinku kunji... Namiji ko mahaukaci ne abola cikin datti wallahi in mace ta wuce sai ya waiwaya... 

Jarabtace bazai yiwu ayanzu ka sami Maza 100% suna kula da Matansu ba bazai yiwu ba, kuma ba abune da yanzu aka soma ba tunda zamanin annabi dama kafin zamaninsa haka ake. 

๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ

Karki ce bazaki hidimtawa miji da kudinki ba... A'ah inda ta kama ki amfani da kudinki kinji domin ki ceto aurenki, mutuwar aure ba dadi sai dole, kidena jin waike bazaki iya kashewa mijinki kudinki ba. Kinkai Nana Khadija dukiya ne? Amma haka tai amfani da arzikinta taiwa Annabi hidima, ta taimakesa, wanda yasa ta dasawa annabi soyayyar da shi kansa saida yace Allah bai azurtashi da Mace kamarta ba. 

Ta taimaki musulunci da arzikinta, ta tsare mutuncin annabi, ta bashi gudunmawa, shyasa har kawayenta bai gushe ba yana karramasu ko bayan mutuwarta. 

Wannan ke nuna miki Mace na neman matsayine a gurin namiji da dukkan abunda take dashi, domin Aljanna ba'a nemanta da wasa, bazai yiwu ki sameta daga kwance ba, akwai kuma wadanda rashin hankalinsu cikin Mata shine komi saide yayansu suiwa mijinsu, saide tace wance kai masa kaza, yi kaza wannan koda namiji baya korafi ya kamata kisan aurenki yake, arziki ko samun sake ba hauka bane.

Ku dena gane-ganen gidan mutane, kowa da irin jarabawarsa. Zaki samu tuwo yake baki amma saiki shekara baki rashin lfy ba, amma wasu ga komi amma ba lafiyar ci.

๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ

Malama ta qara da cewa karya na daga abunda ke 6ata mana aure!
Mu dena karya: kin ari kayan sawa kinzoma saurayi, shima ya aro kaya sannan ya nemi aboki me mota ya rakosa... karshe duk anje anshiga wahala.

Wasu kuma su suka 6ata wayonsu. Taya zaku kafa aure da sabon Allah ku dauka zai qarko? Ba wani Namiji da zai soki da sa6o in yana kaunarki sabi da Allah. Tace

Duk namijin da ya gwadaki da zina billahil azim ko shi kadaine namiji ki rabu dashi. Domin ya gwadamiki kansa shi mazinaci ne, inkika kuskura kika auresa koda bai zinar dake sai kinyi kuka da idonki game da halayen da zaike gwada miki. Ke da kike mace akeson ki zamo uwar al'umma, ai alfahari dake yaushe arayuwa zaki zauna wani yazo ya 6ata rayuwarki ya cuceki, wallahi karki yadda da wannan. 

Koda ya biya sadakinki ina tabbatar miki bafa aurenki yakeson yi ba tuntuni domin baya ganinki a matsayin macen data cancanta dashi.... duk karyace. Karki bari ko ta6aki yake yi, ko yake cewa juya nagani.

Malama tace; Bazan manta ba akwai wanda ya gwada wata yarinya da haka... aiko tai masa kaca-kaca! Da ya tafi bayan kwana biyu sai gashi ya dawo da abokinsa wai abunda yai mata yayine ya gwadata dama ance masa tana da tarbiya, tayi hakuri. A hakan ya aureta, bayan sun tafi honeymoon, a hotel din da suka sauka bayan ta farko ta fito sai ma'aikatan suke cewa wanda suke tare ya bar sako cewa ta daga pillow... bayan ta koma ta duba taga takardar saki da kudi milyan 1 wai shi yayi gaba, ashe sunan da tasansa dashi ma ba nasa bane, wanda ya kawo ma matsayin iyayema hayarsu yai, sannan abun haushi ya barta da ciki, kuma da akaje binkice yai binkice aka gano Matansa 4 ita ata biyar ma ya aureta. 

Don haka sai anlura, binkice dole ne kan halin mutum in akace baza aiba aure bazai ta6a zama lafiya ba. Kunga sha'awarta kurum yake, da yaga bai samu hadin kai ba sai ya nemeta da auren, karshe bukata ta biya yai gaba. Shyasa duk wanda ya nuna miki kui zina yace wai ki hakuri shikenan... kai ki barshi kinji.

Zina hali ce, wanda bayayi ko wanda bata bashi sha'awa bazai ta6a gwadaki da ita ba. Inko kika kuskura soyayya ta rudeki ko wata ta zugaki wai ai yanzu ba'a samun miji saida hakan to you are in trouble wallahi zaki sha kuka kuma kukan da bashi da magani. Kuna iya auren yake bijiromiki da wasu abubuwan ma da Allah ya hana...  

Ba yadda za'ai inde namiji nada mutunci ya budi baki ya nufaceki da zina, inde har neman na Allah da annabi ne.

Akwai wanda inbaki yadda ba zai rarrasheki har ai auren amma bukatarsa na biya zai sallameki, shyasa yanzu har masu tarbiyar ma cikin mata basu tsira ba, domin mazan ma na faking din halayensu su nuna nagarta su sami aurensu.

Don haka duk munsan matsalolin mu, tashi zamui mui yaki da son zuciya sannan mu nemi taimakon Allah sai kuga Allah ya taimakemu.

Allah ka gyara muna auratayyar mu.

Post a Comment

0 Comments