Buɗewar Murfin Ciki Bayan Haihuwa: Sababi, alamu da maganinsa.

Buɗewar murfin ciki yayin goyon ciki da bayan haihuwa na daga cikin matsalolin da mata ke fuskanta sau da yawa. Masu juna biyu na fuskantar matsalar buɗewar tsokokin murfin ciki wanda kuma matsalar ke zarcewa har bayan haihuwa.

Tsokokin murfin ciki wasu jerin tsokoki ne layi biyu, hagu da dama, da ke gaban ciki waɗanda suka taso daga haƙarƙari zuwa ƙugu. Tsakanin waɗannan tsokoki wani tantani ne da ya haɗe ɓangarori biyu na tsokokin.

Buɗewar murfin ciki shi ne buɗewar bangarorin tsokokin biyu sakamakon talewar tantanin da ke tsakaninsu. Faɗin talewar tantanin shi ne faɗin rabewa ko nisantar ɓangarorin tsokokin biyu.

A yayin da aka tabbatar da buɗewar murfin ciki, za a ga bayyanar kwarmi ko rami daga murfin haƙarƙari zuwa cibiya, sannan daga cibiya zuwa ƙasa. Haka nan, za a ji wannan kwarmi ko rami a tsakiyar tsokokin idan aka danna yatsan hannu ciki. Adadin yatsun da suka shige cikin kwarmin shi ne tsanani ko girman buɗewar murfin cikin.

Sabuban buɗewar murfin ciki

Ga masu goyon ciki, talewar tantanin da ke tsakanin waɗannan tsokoki na faruwa saboda ƙaruwar sinadaran goyon ciki waɗanda suke lausasa tsokoki da tantanan jiki domin shirya jikin uwa gabanin haihuwa. Bugu da ƙari, bayan ƙaruwar sinadaran goyon ciki, bunƙurowar tayi da ke ƙara girma kullum a cikin uwa na daga cikin dalilan talewar tantanin.

La'akari da talewar tantanin, kayan ciki za su riƙa bullowa ta tsakanin tsokokin. Za a fi lura da bullowar kayan cikin musamman yayin tasowa daga rigingine zuwa zaune ko kuma yayin tsugunawa.

Kamar yadda muka ambata, buɗewar murfin ciki na afkuwa ne yayin gayon ciki, musamman tsakanin zango na biyu (wata 4 – 6) zuwa zango na uku (wata 7 – 9) na goyon ciki. Kuma wannan buɗewar ce ke zarcewa har bayan haihuwa.

Matsalolin buɗewar murfin ciki sun haɗa da: raunin tsokokin murfin ciki, sakin fatar ciki da tsokokin ciki da kuma bayyanar munin sifar ciki. 

Saboda haka, idan kin haihu kuma kina fuskantar wannan matsala, tuntuɓi likitan fisiyo domin magance matsalar tun da wuri.

#DRA
#LineaAlba
#DiastasisRectiAbdominis

Post a Comment

0 Comments