LITTAFIN FIQHU (KASHI NA ƊAYA) :




BABIN TSARKI TSARKI ƁANGARE NA FARKO: 

Abubuwan da babin tsarki ya ƙunsa sun haɗa da babban tsarki (wato wanka) da ƙaramin tsarki (alwala da taimama wacce ake yi idan an rasa ruwa ko an kasa amfani da shi saboda larura). Abin da tsarki ya ƙunsa ya haɗa da wankewa da gogewa da kuma yayyafa ruwa. Akwai tsarkin najasa da tsarkin dauɗa da tsarkin kari kamar alwala da wankan janaba da na ɗaukewar jinin haila da nifasi. 

1. Kashe-kashen ruwa.
2. Najasa da dangoginta.     
3. Sunnonin fiɗ’ra.
4. Ladubban shiga bandaki.    
5. Butar alwala.     
6. Alwala.
7. Shafa a kan huffi.  
8. Shafa a kan bandeji ko karan ɗori.
9. Wanka da hukunce-hukuncensa. 
10. Taimama.
11. Hukuncin jinin haila da jinin biƙi (haihuwa) da jinin cuta.

TSARKI ƁANGARE NA BIYU: 

Tsarkin zuciya daga dattin shirka, munafurci, hassada da makamantan su.
Tsarkin gaɓɓai daga aikata laifuffuka; su ne ido, hanci, baki, hannu, qafa da ciki. Kada mutum ya kuskura ya aikata haramun da su.
Tsarkin tufafi daga najasa, dauxa da annakiya.
Tsarkin jiki daga najasa, dauɗa da annakiya.
Tsarkin muhalli daga najasa da ƙazanta.
Waɗannan su ne wurare biyar da ake so mutum ya tsarkake domin samun tsarki da tsafta. Manzon Allah ﷺ Ya ce:
    ((الطهور شطر الإيمان))  
Ma’ana, “Tsarki shi ne rabin imani.” 
KASHE-KASHEN RUWA
Ruwa ya kasu kashi shida (6). Kashi na farko shi ne:
Asalin ruwa mai tsarki ne, kamar yadda Allah ﷻ Ya halicce shi. Misali, ruwan sama, ruwan ƙanƙara, ruwan raɓa, ruwan teku, ruwan rijiya, ruwan Zamzam, ruwan da yake fitowa daga cikin duwatsu haɗa da duk wani ruwa da aka same shi yadda Allah ﷻ Ya halicce shi ba a zuba komai a cikinsa ba. Akwai dalilai da dama daga Al-qur`ani da hadisan Annabi ﷺ kamar haka:
Ruwan sama mai tsarki ne saboda fadin Allah ﷻ:
﴿ وَأَنْزَلْنَا مِنَ السَّمَاءِ مَاءً طَهُورًا. ﴾ 
Ma’ana, “Mun saukar muku da ruwa mai tsarki daga sama.”
Ruwan ƙanƙara da raɓa mai tsarki ne. Kamar yadda Annabi ﷺ ya fada. 
Ruwan teku mai tsarki ne. Kamar yadda ya zo a hadisin Abu Huraira (رضي الله عنه) wani mutum ya tambayi Annabi ﷺ dangane da ruwan teku, sai ya ce:    
((هوالطهور ماؤه الحلّ ميتته))     
Ma’ana, “Ruwansa mai tsarki ne, mushensa halal ne.” 
Ruwan Zamzam mai tsarki ne. Hujja Manzon Allah ﷺ ya yi alwala da ruwan Zamzam kuma ya sha, kamar yadda ya zo a hadisin da Sayyidina Aliyyu (رضي الله عنه) ya ruwaito kuma Albani ya inganta shi cikin Tamamul Minna. ()
Ruwan da ya daɗe a wani wuri har ya yi tsatsa ko gansakuka ko kainuwa, shi ma za a iya ibada da shi, saboda ruwa ne mai tsarki.

KASHI NA BIYU :

Shi ne ruwan da wani abu ya shiga cikin sa ya jirkita shi. Shi ma ya kasu kashi huɗu:
Ruwan da najasa ta shiga cikinsa ta sauya launinsa, ɗanɗanonsa da shaƙarsa. Wannan ba za a yi ibada da shi ba, ko abinci ko abin sha kuma ba za a yi wanka ko wanki da shi ba. Dalilin haka shi ne malamai duka sun haɗu a kan ba za a yi ibada da shi ba. 
Idan najasa ta shiga cikin ruwa amma ba ta ɓata shi ba, za a iya amfani da shi idan ba a sami wani ba. Manzon Allah ﷺ Ya ce:
((الماء طهور لاينجسه شيء))  
Ma’ana, “Ruwa mai tsarki ne babu abin da yake mayar da shi najasa.”
Ruwan da wani abu mai tsarki ya shiga cikinsa, ya sauya kalarsa, ɗanɗanonsa ko shaƙarsa, kamar maiƙo, miya, kunu, zoɓo, ruwan lemo da makamantansu.Wannan mai tsarki ne, amma ba za a yi ibada da shi ba sai dai kawai a ci ko a sha.
Ruwan da wani abu mai tsarki ya shiga cikinsa amma bai jirkita shiba, saboda abin da ya shiga kaɗan ne kuma ruwan yana da yawa.
Za a iya yin amfani da shi idan ba a sami wani ruwa garai-garai ba. Hujja, Manzon Allah ﷺ Ya yi wanka a cikin wata ƙwarya da a cikin ta akwai ragowar ƙulli a lokacin da aka yi Fathu Makkah.

KASHI NA UKU:

Ruwan da wani ya yi amfani da shi wajen wanka ko alwala ko ya sha ya rage. Irin wannan ruwa shi ake kira ‘Mus’ta'amal’ wanda aka yi amfani da shi aka rage, ko wani ya tsoma baki a ciki. Shi ma ya kasu kashi-kashi. Misali:
Ruwa mai tsarki da aka yi amfani da shi, aka wanke najasa a cikinsa. Idan ya sauya daga asalinsa, ya zama najasa, amma idan bai sauya daga halittarsa ba, za a iya sake amfani da shi idan ba a sami wani ba.
Ruwan da aka yi amfani da shi wajan tsarki, kamar kama ruwa, shi ma za a iya sake amfani da shi idan yana nan a kan halittarsa.
Ruwan da aka yi alwala ko wanka da shi amma bai jirkita ba, za a iya sake amfani da shi.
Ruwan da aka tsoma baki a ciki aka sha, babu laifi a yi ibada da shi. Hujja ita ce hadisin Nana Ai’shah (رضي الله عنها) ta ce, “Na kasance ina shan ruwa alhalin ina jinin al'ada, na bai wa Manzon Allah ﷺ ruwan ya sha, ya sa bakinsa a inda na sa bakina. 
Ruwan da wata dabba da ake cin namanta ta tsoma baki a ciki, shi ma yana da tsarki matuƙar babu najasa a bakinta a lokacin da ta saka bakin nata a cikin ruwan. Malam Ibn Munzir ya ce, “Malamai sun haɗu a kan cewa ruwan da dabbobin da ake cin namansu suka tsoma baki a cikinsa, yana da tsarki, za a iya sha kuma a yi alwala da shi.
Ruwan da jaki ko alfadari ko tsuntsayen da ba a cin namansu suka tsoma baki a ciki. Wannan ruwan idan yana da yawa yadda ba za a ga wata alama ta najasa a cikinsa ba, ko wata ƙazanta, za a iya yin aikin ibada da wannan ruwan a bisa magana ta malamai mai ƙarfi, kamar yadda fatawar manya-manyan malaman Saudiyya ta tabbatar (5/380).
Ruwan da kare ko alhanzir (alade) ya tsoma baki a ciki. Wannan ruwan najasa ne, ba za a yi aikin ibada da shi ba, ko a ci ko a sha. Saboda hadisin Abu Hurairah (رضي الله عنه) cewa Manzon Allah ﷺ Ya ce:
((إذا شرب الكلب في إناء أحدكم فليغسلْه سبعًا، ولمسلم: أولاهن بالتراب)) 
Ma’ana: “Idan kare ya sha a cikin ƙwaryar daya daga cikinku ya wanke ta sau bakwai na farko ya sa qasa.” A wata ruwayar, a hadisin Abdullahi Bn Mugaffal, (رضي الله عنه) Annabi ﷺ Ya ce: “Idan kare ya yi lallage a cikin kwarya to ku wanke ta sau bakwai, cikon na takwas ku dirje da qasa.” 
Ruwan da mage ta tsoma baki a ciki,wannan ruwa mai tsarki ne matuƙar ba a ga najasa a tare da ita ba, saboda hadisin da Manzon Allah ﷺ Ya ce: “Ita mage ba najasa ba ce, tana cikin masu zirga-zirga a cikin gidajenku.” 
Ruwan da ya yi maƙotaka da najasa har aka ji warin najasar a cikinsa, irin wannan ruwan babu laifi a yi ibada da shi, duk da ana jin warin mushe a cikinsa, amma maƙotaka ta jawo ba haɗuwa suka yi a waje ɗaya ba.
 Ruwan da mutum ya tsoma hannunsa a ciki bayan ya farka daga bacci, shi ma ruwa ne mai tsarki duk da Annabi ﷺ ya hana mutum ya tsoma hannunsa a cikin ruwa bayan ya farka daga bacci, domin bai san a wanne hali hannunsa ya kwana ba.
 Ruwan da mace ta yi wanka da shi ta rage ko namiji ya yi wanka ya rage, shin wani zai iya zuwa shi ma ya yi amfani da wannan ruwan ko a'a ? Magana mafi rinjaye ita ce, shi wanda ya yi amfani da ruwan zai iya sake amfani da shi, amma ba wani dabam ba, sai idan babu wani ruwan, kuma babu alamun ruwan ya jirkita. Sharhin Bulugul Muram: Subululs Salam.
 Idan mutum yana kokwanto a kan tsarkin ruwa, sai ya yi gini a kan asali, cewa asalin ruwa mai tsarki ne, ba za a yi hukunci da najasa ba a kansa har sai an sami dalili. 

KASHI NA HUƊU:

Shi ne ruwan da ake kokwanto a kan tsarkinsa. Irin wannan ruwa idan za a yi amfani da wata alama ko zato mai ƙarfi wajen tantance tsarkinsa sai a yi amfani da shi.

Sai kuma ruwa mai najasa da aka yi amfani da wani sanadari aka cire najasar. Irin wannan ruwa ana iya amfani da shi wajen aikin ibada matuqar wannan najasar babu ita, a ɗanɗanonsa ko shaƙarsa ko kalarsa.

Sai kuma ruwan da aka samo shi a cikin ‘ya‘yan itace. Irin wannan ruwa sai dai a yi amfani da shi a wajen al'ada amma ban da aikin ibada.

KASHI NA BIYAR:

Ruwan da aka ɗumama shi da zafin rana. Irin wannan ruwa mai tsarki ne kuma za a yi aikin ibada da shi.

KASHI NA SHIDA:

Ruwan sata ko kwace. Duk wanda ya sato ruwa ya yi wanka da shi ko alwala, ibada ta yi, amma za a tilasta shi ya biya ruwan. (Al-Mulakkas Al-Fiqhi)

Post a Comment

0 Comments