1.RIKO:
Riko shine idan an aikata maka wani laifi kabar abin a ranka batare da kayarwa ba.
Uwargida kada ki zamo mai riko domin hakan ba karamin ja maki matsala zaiyi ba musamman idan mijinki nada saurin fushi . Saboda haka idan abu ya faru ki dinga hakuri domin mata an sanku da hakuri da juriya idan akai abu to da zaran ya wuce to a maida komi ba komi bane domin aljananku tana karkashin Maza yake sai sun daga zaku samu mata Ku dinga hakuri a duk lamuranku sai kuga kun dace.
2. YAWON MITA:
Yar'uwa karki zamanto cikin mata masu yawan mita a gurin mijinki.
3. FUSHI:
Uwargida karki zamanto mai yawan fushi ko nuna wa miji Yawan fushi
Karki manta Allah da kansa "yace yana tare da masu hakuri" shin bakya son Allah ya zamto yana tare dake kowane lokaci
Yar'uwa ki sama ranki hakuri fushi banaki bane domin karkashin wani kike kowa yace zo mu zauna zomu saba ne Hakuri shine ribarki.
4.RASHIN IYA GIRKI:
Da anxo maganar girki sai naji tsoro tare da jin kunya Haba yar'uwa ya kamata ace iyayen mu na koya muku girki tun kuna 'yan shekaru 7 Wlh wallahi wlh samun yar aiki ba gata bane
Ina gatan yake kina can kwance yar aiki na saye zuciyar mijinki da dadan abinci yar'uwa/uwargida Ku tashi tsaye Ku koyi girki kodan saye zuciyar miji Domin namiji nason matar da ta iya girki sosai Zaki ga namiji na gayyato abokanai zuwa gidan shi don suci abinci saboda yasan bazata bashi kunya ba amma idan baki iyaba fa zai fara tunanin kara aure wato yayi maki KISHIYA Hmmm mata ku gyara.
5.KAZANTA:
Uwargida ayi tsafta kodon lfyr jikinkin karki manta tsafta nadaga cikin addini Yar'uwa idan ba tsaftar ya zakiyi ibada Sanan kisani tsafta nasa miji ya soki sanan yaji baya da kamarki zaki ga kowane lokaci yana manne dake yana shakar kamshinki
Idan kuwa bakida safta da ya baki kudin cefanen bazaki kara ganin shi ba sai dare domin ko ya dawo ba abinda zai gani sai bacin rai, har ki dinga cewa ya daina sonki Sanan ki sani kazanta mabudin kara aure ce wato yayi miki kishiya.
6.KULA DA SHINFIDAR MIJI:
Mata kuna sakaci wajen bawa miji hakkinsa ki naso amma ki tsaya ki kauyanci wai jan aji ina ajin yake bayan yagama saninki lungu lungu ba inda bai saniba ajikinki Allah ya kara tabbatar da Zaman lafiya tare da mazajenku
Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: ☏+2348037538596
0 Comments