Ga Dalilin Da Yasa Namiji Sabon Aure Bai Jimawa Akan Matarsa Bai Kawo Ba. Mace Kuma Bata Kawowa A Farkon Soma Jima'i:




Maza musamman sabbin aure suna yawan kokawa akan saurin yin inzali akan matansu. Haka suma mata sabbin aure suna kokawa akan rashin samun gamsuwa irin na Jima'i a lokacinda suke amare.
Namiji sabon aure kuma wanda baya zina, a lokacin da yayi aure zai rika saurin zuwan Kai. Hakan na faruwa ne saboda rashin sabo, zumudi da kuma yawan maniyi daya tara a ma'ajiyar adana miniyinsa.
Daga lokacin da ya ci gaba da saduwa da matarsa, zai ga yana kara lokaci kamin yayi zuwan kai har daga karshe zai dawo daidai da yadda halittar sa na Jima'i yake.

Ga angon daya samu kansa a irin wannan hali kada ya daga hankalinsa ko ya dauka yana dauke da wata cuta ne, abun ba haka yake ba. Kawai abunda ya kamata yayi shine ya kasance yana yawan gudanar da Jima'i akalla kullum sau biyu ko uku cikin karamin lokaci zai ga ya soma Jimawa.

Masu irin wannan matsalar idan suka lura zasu ga cewa, Jima'insu na farko suna saurin zuwan kai, amma kuma idan suka koma na biyu suna daukan lokaci kamin su yi zuwan kai, da zasu kara na uku zasu jima fiye dana biyu. To haka abun yake. Yawan gudanar da Jima'i yana hana saurin zuwan kai.

Haka nan kuma sabbin angwayen da suke da wannan matsalar kada su jewa iyalansu a lokacin da suka zaku, suka kamu da sha'awar Jima'i, idan har sun tinkari matansu a irin wannan yanayin suna ma iya kawowa kamin ma su shiga.

Don haka kada su yi doguwar wasannin motsa sha'awa. Haka nan kuma idan matansu masu ni'ima ne sosai nan ma suna iya zuwan kai da wuri a saduwan farko, hakan ma ba matsala bane sai dai ga namijin da sai ya huta yake sake mikewa yana iya cutar da matarsa kamin ya sake komawa ganin a lokacin data soma daukar zafi a lokacin shi kuma yayi sanyi.

Don haka maza sabbin aure masu matsalar saurin zuwan kai su gane cewa hakan ba matsala bane har sai idan mutum ya haura watanni 6 da yin aure kuma yana yawaita yin Jima'i amma hakan ya ci gaba da faruwa. Idan ango ya samu kansa a hakan, to yana bukatar magani. 
Wannan maza kenan

Ita mace sabuwar amaryar da bata taba zina ba yana da matukar wuya ta iya yin zuwan kai a farkon watannin aurenta. Bama zancen zuwan kai ba. Mata sabbin aure ba kasafai suke ma jin dadin Jima'i ba a farkon watannin da suka yi aure ko suka soma Jima'i. Sai an dauki lokaci mai tsawo ana gurzanta kamin ta soma jin dadin sa harma ta soma zuwan kai.
Akwai matan da sai ma suyi haihuwar farko sannan suke soma yin zuwan kai. Shi yasa za aji wasu matan suna kokawa akan sudai basa jin dadin Jima'i.

Ita mace kamar injin mota take. A lokacinda yake shan wuta a lokacin yake kara lafiya da kuma dadin inji.

Wasannin motsa sha'awa mai tsawo yana iya sa mace ta soma jin dadin Jima'i har ma ta soma zuwan kai cikin karamin lokaci. Sai dai ya zama dole a irin wannan yanayin na wasannin ma'aurata su rika amfani da sadarwa na Jima'i domin fahimtar inda mace tafi so a taba mata da kuma yadda take so ayi mata.

Muddin mace ta dau lokaci mai tsawo bata soma jin dadin Jima'i ba ko zuwan kai. Yana da kyau ta tuntubi likita domin samun taimako. 

Ko kunsan akwai maza da matan da kwatakwata basa zuwan Kai? A darasi na gaba zamu yi bayaninsu, abunda ke haifar da hakan, da hanyoyin magance matsalar.

Post a Comment

0 Comments