🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍
TIPS NA FARKO
Jarirai mutane ne masu rauni wato basu da garkuwar jiki mai karfi da zata iya yakar cuttukan daka iya kamasu Saboda haka basu cikakkiyar kulawa wajibi ne Akan mu, wani abun su zamui wa wato kamar sanya musu kayan sanyi, share hancin su yayin da yake toshewa, karesu daga iskar fanka Kota Äç daka iya dauko kwayoyin cuta zuwa garesu daka iya shafar hanyoyin numfashi su koma sui developing din pneumonia, ko kuma ta hanyar ku iyaye matan kuke ci musu nau'in abinci mai inganci da zai amfani jikinsu ta hanyar shan nono.
🎑TIPS NA BIYU
Wajibi ne a irin wannan zamani da muke ciki kai yara alluran rigakafi domin kula da lafiyar su musamman Wadanda ake ma yara daga zarar haihuwa na (BCG da HBV) domin karesu daga hatsarin kamuwa da kwayar cutar tarin TB. (Tuberculosis) da ciwon hanta rukunin B.
Hikimar yin hakan aranar da aka haifi yaro shine, ana samun mutane Yan barka dake tururuwar zuwa ganin jariri musamman yankunan mu na karkara da kowacce burinta abata dan ta dauka, wata ajikin tufafinta ba'a san me ta debo ahanya ba Saboda kura ko iska, haka wata ita kanta kila tana fama da ciwo irinsu tari da sauransu kunga sanda ta rungumi jaririn nan komi na iya faruwa wanda ka iya cutar da yaron, Amma karshe sai kaji uwa na ai baki ne ya kamashi kowa sai Yace kai wannan yaro katoto haka. Amma azahiri bawani baki sakaci ne kurum dan haka koda anyo irin wannan alluran ki samu net din saka jarirai ki tura danki ciki duk wacce ta shigo an haihu! Eh an haihu ga yaro can yana bacci! To Allah raya amin. Hakan ya wadatar gara aleka aganshi yafi kowacce tazo ace sai an Mika mata duk Abu agaji da yaro. Ba ruwanki da surutun da za'ai gara surutun kin hana dan da abarku da ciwo kuna kwana ba bacci.
TIPS NA UKU🎑
Haka kuma kamar yadda Nasha fada abaya iyaye mata ya kamata su kara kulawa bayan farkowar jariri daga bacci ko yana Kuka ko bayayi ba ruwa ya kamata ake dura masa ba, Nono yake bukata, adena basu ruwa kai tsaye sai bayan sun sha nono.
Ruwan da ake basu shike sa da yawa Basa girman da kuke so saide ku rika hangen ya'yan wasu kuna sha'awa. Kuma shikesa wasu yaran fama da gudawa suna ramewa.
🎑TIPS NA HUDU
Bayan kingama ba yaro nono karki abun nan da mata suka jima suna yi wato kurum ki ja sale6ar nono ki mayar cikin bra. Wannan kuskurene hakan Akan kwayoyin bacteria koda yaushe Akan fatar jikin mu aduk yayin da Kika gama bada nono anso ki sa ruwa ko tsuma mai lemar ruwa inda hali mai dumi ki goge Kän nonon da shacin jikin nonon Sannan ki mayar cikin bra hakan na kare jarirai daga tsotsar dattin irin wannan bacteria daka iya sa su zawo Saboda haka akula.
TIPS NA BIYAR🎑
Bayan gama shayar da jariri nono kada ki sake ki tintsirar dashi wato ki maida shi gado ki kwantar wannan kuskurene. Ana so ki dorasa akafada ne ki ke jijjigashi ahankali Kina shafa bayansa zuwa can zakiji yayi gyatsa alamar ruwan nonon ya tsirga masa hakan zaisa da kin koma kin kwantar dashi zaici gaba da baccinsa domin ya koshi Amma inkika ji bai gyatsa ba alama ce ta nono bai ishesa ba dan haka ki tashi zaune kici gaba da bashi nono.
Haka kuma kuskurene Nasha fada bayar da nono akwance shike kumbura ma jirajiranku ciki suita Kuka wani lokacin. don haka komi dare ki daure ki tashi zaune.
🎑TIPS NA SHIDA
Yawancin jira-jirai sabbin haihuwa Akan haife su da nauyin kilograms biyu da digo bakwai (2.7kg) zuwa kilo hudu (4kg), kadan ke haura hakan. Sannan yaron da ya Gaza kilo 2 wannan ya kasance malnourished wanda ba'a son ganin haka domin hakan na nuna uwa batasamu ingantacciya kulawa ba yayin goyon cikin ko kuma ambarta tai ta fama da cuttuka musamman malaria.
Saide koda an haifi yaro da cikakken nauyi bayan kwana 3 zuwa 4 da haihuwa nauyin yaron kaso 5% zuwa 10% yana raguwa komi kulawar da ake bashi wannan ba matsala bane dan anga haka. Sannan tsayin jariri inya kasance namiji yana zuwa ne tsawon centimeter 50cm yayin da mace ke zuwa a centimeter 49cm.
TIPS NA BAKWAI🎑
Daga lokacin da jariri yakai watanni 6 zuwa 12 ana tsammanin nauyinsa na haihuwa ya rubanya kansa yakai ninki uku (3x). Wato in anhaifa yana da 3kg daga sanna yakai wata 6 har zuwa cikar shekara ana tsammanin yakai 9kg.
Inba haka ba hakan na nuna baya samun cikakkiyar shayarwa da ingantaccen abinci Saboda haka sai a kiyaye.
Zaki iya sanin nauyin danki da kanki ta hanyar lissafa yawan watannin sa a duniya (Age in month) ki tara da iya adadin watannin ciki wato wata tara (+9), sai ki raba zuwa gida biyu.
Kamar haka:
Weight= No of child months +9/2.
Misali:
Idan yaron watansa 4.
W= 4+9/2
= 13/2
= 7.5kg,,
Kunga dan wata hudu zai kasance da nauyin 7.5kg idan har yana samun cikakkiyar shayarwa.
ALLAH YA BAMU IKON KIYAYEWA AMIN
[Ibrahim Y. Yusuf]
0 Comments