Daga Yusuf Shuaibu
Iyaye suna da matukar tasiri a zamantakewar aure da ‘ya’yansu a ko wani hali da kuma yanayi. Don haka nema a zamanin baya iyaye ne ke zaba wa ‘ya’yansu maza ko mata wadanda za su aura, hakan kuma ya yi matukar tasiri a wannan lokacin ganin yadda ake samun aure na mutu ka raba sabanin abubuwan da suke faruwa a yanzu.
Duk kuwa da wasu gidajen har yanzu iyaye ke da alhakkin nema wa ‘ya’yansu wadanda za su aura.
Rashin jituwa ko fahimta da ake samu a tsakanin iyayen miji da matarsa ya fi yawaita a tsakanin uwar miji, domin yana da matukar wuya a uban miji ne ya takura wa matar dansa ko kuma ba su zaman lafiya da juna.
Wannan dabi’ar ya fi yawaita ne a tsakanin uwar miji da kuma matar danta, wanda wasu da dama na mamakin abubuwan da ke haddasa irin wannan matsalar.
Ga duk wata matar da take son more zaman aurenta, ya zama wajibi ta sha maganin zama da uwar mijinta ko da kuwa ba a gida daya suke ba ko kuma gari guda kai koma kasashen da suke zaune ya babbanta. Muddin uwar miji ba ta yi da ke, to ko bangon duniyan kika tafi da mijinki kuka zauna don gudun matsala ko tashin hankali, to kin yi a banza muddin dai suna haduwa da danta ko tana magana da shi. Don haka abun yi kawai shi ne, duk irin son da take miki kamin aure, to ki tabbata kin kara samu wasu dabarun iya zama da ita.
Kuskuren da akasarin mata suke yi shi ne, rashin yi wa uwar miji ladabi da biyayya don wai tana tunanin cewa mijinta yana sonta. Babu dan kwarai da zai bar matarsa ta wulakanta masa uwa don dai yana sonta. Dole ne duk darajar ki ko na gidanku ki nuna wa uwar mijinki ladabi da biyayya fiye ma da iyayen da suka haifiki domin ke dolen iyayenki ne amma ba dolen uwar mijinki ba ce.
Komin tsufanta, komin talaucinta ya zama babu raini ko tsana tskanin ke da ita, koda kuwa a zahiri ba ta sonki, ki ci gaba da yi mata biyayya wata rana dole ta saduda.
Wani abun kula kuwa shi ne, kada ki sake ki aure namijin da kika tabbatar da cewa uwarsa ba ta kaunarki komin son da kike masa ko kuke wa juna ki hakura, idan kuwa kika yi auren ba zai jima ba kina iya zama bazawara.
Ki nemi amincewar uwar mijinki ta hanyar gamsuwa da cewa tabbas tana wa danta sha’awar ya zauna da ke a matsyin matarsa.
Ko wace uwa tana son mai son danta, don haka ki nuna wa uwar mijinki kai tsaye ko a kaikace cewa kina fa son mijin nan naki.
Ta hanyar nuna damuwa a lokacin bakin ciki ko wani bacin rai da ya faru, haka kuma nuna ki murna da farin ciki idan abun alkairi ya same shi. Kuma kada ki boye mata wajen kokarin da kike yi wajen kula da dukiyoyinsa da ya bari a karkashin kulawarki kuma kada ki nuna kyashi ga kyauta da zai yi wa ‘yan uawansa a gaban mahaifiyarsa. Ki kasance mai kula da ‘ya’yanki sosai, kuma ki kula cikinsu wanda uwar mijinki ta ke so ke ma ki daukake shi.
Kada ki furta wata bakar magana ko dukan ‘ya’yanki a gaban uwar mijinki kuma kada ki bari suna aikata wani mugun abu a gabanta baki hanasu ba.
Kamar yadda kowace mace take kishin mijinta, haka uwar miji take kishin danta. Kada ki sake ki nuna wa uwar mijinki ai ke ce da gidan sai yadda kike so za a yi, idan kika bari uwar mijinki ta fahimci hakan, da ke da ita babu sauran zaman lafiya kuma. Domin uwa gani take ita ce ta dace da ta juya danta amma ba wata mace ba.
Ki yawaita yi wa uwar mijinki kyauta musamman na abin da kika san tana sha’awa na cine ko kuma na sanyawa a jiki.
Idan kina da hali, ki rika daukar surukarki kuna fita ziyarar ‘yan’uwanki ko nata tare. Ki kula da al’adunta ko addininta domin ki girmamasu. Yana iya yiwuwa al’adunki dana surukarki daban, haka kuma addininku shima daban, to kada ki kyamace ta, abin da kika ga suna yi na al’adunsu ko addinsu wanda bai saba da naki ba ke ma ki yi, wanda kuma ya ci karo da naki cikin hikima da dabara sai ki nuna musu rashin amincewarki da su.
Kada ki sake ku rika zagin wani ko wata da uwar mijinki, haka kuma kada ki amince da duk wata shawarar da za ta zo miki da ita wacce ba ta da kyau, kamar zuwa wajen bokaye da ‘yan bori domin neman wata biyan bukata.
Ko kuma zagin kishiyoyinki, ki yi kokarin kaucewa duk wata bakar al’adar da za ta yi kokarin cusa ki ciki, yin hakan zai yi miki tasiri nan gaba, domin ko wani ne ya ce mata kin yi makamancin hakan za ta miki kyakkyawar shaida. Ki yi zaman aure domin Allah.
0 Comments