🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
PARACETAMOL Wannan shahararren magani ne akasar mu wanda manya da yara, maza da mata, tsoffi da dattawa kowa yasan shi, kuma kowa yasan sunan. Kai intakaice muku ma duk chemist din da aka rasa wannan maganin toh ba chemist bane.
Maganin yayi popular ba wanda bai bude ido dashi ba; sannan magani ne cikin rukunin OTC wato wadanda basa bukatar sahalewa ko ganin rubutun likita wato (prescription sheet) kafin abaiwa mutum shi. Ba irin Antibiotics, Anti hypertensive, antimalarial, anti motility ko anti histamine bane dake bukatar rubutun likita.
🌻🌻
Paracetamol akowacce irin kasa aduniya mutum na iya zuwa pharmacy stores asayar masa.
Mutanen mu na amfani dashi wajen maganin ciwon jiki, ciwon kai, zazza6i, da kasala.
🌻🌻
TOH SAI DE MENENE AIKIN MAGANIN A ZAHIRANCE
Paracetamol magani ne daga dangin ANALGESICS wato magani me rage zugi ko radadin ciwo. Aikinsa kenan karka dad'a karka rage.
🌻 🌻
TOH AMMA YA MUTANEN MU KE AMFANI DASHI ?
Ba al'ummar dake haikewa magani sui masa duk yadda sukeso aransu irin mutanen mu, koma wanne irine. Su abunda suka bude ido suka san magani akai toh fa bazasu ta6ajin cewa abun zai iya canzawa ba, ko kuwa bazasu ta6a tsayawa suce kai abun nan mun dade haka muka taso mukaga ana bamu wai asalinsa na menene? Ya aikinsa yake? Shin bashi da illa?
Sam, sam mutanen mu basu da wannan, kai in takaice muku akwai ma masu yiwa wasu suggesting na magani.... kurum da sunji mutum yace ciwo iri kaza nakeji.... zasu ce dauki ga magani can kasha, ko kuwa kwanaki nima da naje asibiti da matsala abu kaza likita ya bani kaima jeka ka nema kasha.......😥
Jama'a waccan halayyar tamu tayima magungunan da muka raina shan gaba gad'i ta kashe muna mutane da yawa, ta naqasa tsoffi,
Kananun yara kuwa paracetamol ya kashe muna su ba wanda yasan adadin sai Allah. Iyaye sun kashe yayansu sanadiyyar paracetamol batare da sun san sun kashe ba.
🌻🌻🌻
MEYE ILLARSA
■ Koya uwa taji jikin danta ya canza farko za6insu da yawa bashi ne suje asibiti ba, kurum asayo paracetamol adura masa... sannan ajira idan ya warke shikenan inbai warke ba acigaba da banka masa hade da jikejiken maganin hausa har zuwa wasu kwanaki shine kurum. Sai in anga ba sarki sai Allah sannan za'a nufi asibiti yayin da ciwon ya gama nakasa yaro. Azo ana likitoci sun fiye wulakanci
■ Kuma har a manya ma akwai masu wannan halayyar haka suke yiwa kansu, suita shan paracetamol suna hadawa da jiqon maganin gargajiya suma bazasu asibiti ba sai sunji ba dadi. Akarshe in mutum yaji labari mara dadi hankalinsa ya tashi.
Shyasa da yawa sai kuji ance dikadika zazza6in kwana 2 yayi sai gani mukai ya rasu..
■ Paracetamol magani ne lamba daya wajen haddasa CIWON HANTA ta hanyar dasa mata guba ashi karan kansa. BALLANTANA ka hadasa da concussion.... A duk lokacin da ka hada shan paracetamol da MAGANIN GARGAJIYA rana guda.... subahanallahi kasani tamkar kaine ahadaka da cire wando taka....kasan de ba sauki kam... Toh kamar haka hantarka ke shiga wahala wanda akarshe tai FAILING....
Toh Saide dake hanta tana da wani abun al-ajabi idan ta sami rauni tana iya farfadowa ta gyara kanta da kanta batare da kasan anyi ba.... toh amma idan shan paracetamol ya wuce kaida ya zame ma jiki... toh wataran bazata farfado ba. Shyasa yanzu gashi nan kananun yara da matasa masu ciwon hanta sai yawaita suke.
Sannan masu MIXED din paracetamol da maganin gargajiya suma ba iya hanta ba kai tsaye suna gayyatar CIWON KODA ne. Shyasa karasa dalili gashinan ciwon koda sai hauhawa yake a al'umarmu.
Mutum matashi amma ka samu KODARSA tana Failing; wasu ayanzu haka da nake wannan rubutun kodarsu na nan ba lafiya amma basu sani ba, domin k'oda saita dau shekaru bata nuna alama ba randa zata bayyana sai tana gab da kai mutum kabari.
■ Su kuma mutanen mu inde zakace suke zuwa asibiti check up lokaci lokaci.... toh ba mahaukaci ko wanda baisan zaman lafiya ko kuwa me son sasu kashe kudi abanza irinka kai me cewa suje asibiti gwaji haka kurum batare da suna jin ciwon komi ba.
■ Sannan kunga yadda SEPTRIN Ke kone jikin wasu mutanen insunsha wato abunda muke kira steven Johnson syndrome toh Paracetamol ma zai iyasa jikinku gobara irin wannan in dose yai yawa.
🌻🌻
ABUN DA BAKU SANI BA
Paracetamol ba maganin zazza6i bane azahirin gaskiya... magani ne da inya hadu da maganin kwayoyin cuta ke dada taimakawa zazza6i ya lafa... shiyasa ba akira da ANTI FEVER ba sai akace me? ANALGESIC wato rage radadi.
Sannan Paracetamol ba ayisa domin ciwon kai ba. Sam sam ba aikinsa bane. Domin ciwon kai abubuwa da yawa na iya haddasa kama daga migraine, hawan jini, karancin jini, rashin ruwa ajika, rashin bacci da sauransu.
Shyasa sai akayo maganin da ake kira ANTI INFLAMMATORY irinsu Ibuprofen, Cataflam, Sudrex da sauransu sune magungunan ciwon jiki.... ba Paracetamol ba. Kuma kosu nafada muku illar shansu batare da umarnin likita ba.
Toh amma mutanen ba ruwansu, komi paracetamol, shaysa da yawa sun mutu batare da ansan me ya kashe su ba. Sannan da yawa sun tafi asibiti jinya me zafi wacce bai kamata ace sunkai ga haka ba, amma dogaro da Paracetamol a matakin farko shi yakaisu ga hakan.
🌻🌻🌻
KU SANI AL'UMMA
Eh in anji zazza6i ana iya ba mutum paracetamol amma ya zamto akan hanyarku ta zuwa asibiti kuke, bawai kurum abashi akoma a zauna ba. Duk wanda ka ta6a jikinsa kaji alamun zazza6i Tempreture dinsa tai high abunda hakan ke nuna shine AKWAI kwayoyin cuta dake yawo yanzu haka acikin jikinsa wato ONGOING INFECTION walau acikin jininsa, tsokokinsa ko lymphatic drainage nasa... sannan zai iya kasancewa Bacteria, Virus, Fungi ko Protozoa irin su malaria..... shyasa malaria ke zuwa da zazzabi me zafi domin cikin jini take bi kaga kuwa ba inda inka huda jikin mutum bazakaga jini ba.
Toh inka bashi paracetamol ciwon bazai tafi ba domin Paracetamol baya maganin infection ita kuwa fever ko yaushe kajita to infections ne.... shyasa sai infection yaci gaba da nuqurqusa mutum inba anyi sa'a yana da garkuwar jiki me karfi ba karshe mutum sai ankai ga karin ruwa ko jini, koma ya mutu kurum
🌻🌻🌻
GARGADI GA KOWA
Ku guji shan magunguna barkatai tare da sabawa jikkunanku dasu, PARACETAMOL din nan koda likita ya bakashi ya kamata kasan akwai abubuwan da ba'a hadasa dashi;
■ Ba'a shansa a empty stomach
■ Ba'a ba me ciwon hanta paracetamol
■ Ba'a ba me ciwon matsalma ma paracetamol
■ Ba'a hada paracetamol da maganin gargajiya wato concussion
■ Ba'a hada shi da maganin fungal infection irinsu Ketoconazole, Fulsin da sauransu.
Kuma kafin abaka sai an auna nauyinka, domin sanin DOSE din da ya dace dakai, da kuma irin maganin da kake sha ayanzu na wani ciwon in akwai.... dade sauransu
Shyasa ko yaushe nake cewa koda ma'aikacin lafiya ne kai matukar baka fahimci mechanism of action na magani ba, kuma in ansamu side effects wato toxicity nasa bakasan ya zaki reversing din abun ka gyara ba, Bakasan Half life na magani ba, Baka kuma iya calculating DOSAGE ba toh GASKIYA HARAMUN ne akanka kake rubuta magani. Inba haka ba zakai ta kisan kai batare da kasani ba kuma inka mutu Allah bazai kyaleka ba domin babu uzuri ga aiki cikin jahilci irin wannan
Domin da yawa sun dauka PARACETAMOL tunda duk kwaya 1 yana da 500MG toh kurum Babban mutum ya dauki bibiyu sau 3 a rana (II-II-II) karamin yaro kuma araba daya biyu abashi rabi ½.... da yawa haka kuka dauka wannan babban kuskuren shike hana FEVER tafiya ko kuma ya haddasa illa ma domin sam wani zaku cikamasa dose din wani kuma zaku bashi kasa da abunda yake bukata, don haka dole kusan wannan kowanne mutum mace ko namiji nauyinsa da jinsinsa nada tasiri wajan bashi dose din magani bawai kurum JAMA'U ake ba.
🏵🏵
■ Don haka duk ciwon da kaga yaqi ci yaqi cinyewa ka tura mutane zuwa ga asibitin gaba inda babban likita yake.
■ Sannan mu koyi zuwa asibiti mudena SELF MEDICATION jama'a, mu dena ingiza mutane kan cewa su sha magani iri kaza muma shi muka sha. Duniya ta wuce wannan wurin
■ Shyasa duk wani mugun ciwo in kan karanta Journals sai kaji ance AFRICAN AMERICAN sunfi kowa hatsarin kamuwa..... Ba wasu bane African American illa mu Bakaken Fata kurum an sakaye ne amma mu likitoci munsan da mutanen mu ake.
🏵🏵
GA MAIKATAN LAFIYA
Wajibi ne ku koyi kyakkyawan amfani da internet dinku karku shagala sai chatting, sai shirme da surutan siyasa ko labaran ban dariya. Ku rika ware lokaci kullum kuna consulting medical journals online kuke downloading pdf kuna karantawa... ta haka ake kwarewa a aiki.
Duk wanda kagani da ilimi ba akwance ilimin ya taho ya shiga kansa ba, aiki yai tuquru ya takura kansa har ya iya... ba wanda aka haifa ahaka. Kaima inka tashi zaka iya canza abubuwa. Ka nemi accredited journals ka rika karantawa ba kowanne tarkace a google ba.
Duk minti 5 sai ansami sabon abu a fannin lafiya karka zauna kurum treatment din shekaru 20, 10, 5, 3, ko 2 baya har yau shi kasani ba canji. Musamman masu ulcer kuita hargitsa musu magani ba lisaafi. Wani kaga H2 blockers har kala 2, ga proton pump 1 ga paracetamol, ga anti biitic har kala 2 ko 3 duk wai maganin ulsa.... taya mutum bazai sha wuya ba.
Ku sani harkar lfy is all about TRUST duk abunda kai rashin sani ya illata mutum Allah ma bazai barka ba, ba ayi don wane yana yi... kai kanka dole kasan me kakeyi. Ya magani yake... tukun
■ Sannan babban assignment din da zan barku dashi shine daga yanzu inbakusan ya ake CALCULATING DOSE na kowanne irin drugs ba toh ku dage ku cije sai kun koya kun haddace wallahi inkukai haka kuma sai kunfi ganin improvement daga marasa lafiyarku. Kunga wannan takardar ta cikin kwalin magani me mitsimitsin rubutu ba abanza take ba. Wani 4mg/ml, duk wadannan da mahimmancinsu anan zakuga drug interaction maganin da ba ahadasu da wannan.
Don haka mui karatun ta nutsu ....
0 Comments