Image result for lemon grass plant png
Amfanin Lemongrass ga Lafiya (Ciyawa-mai-kamshin-lemu)
Lemongrass (Cymbopogon citratus) shuka ce mai dadin kamshi, wato wata irin ciyawace doguwa mai launin kore da kamshin lemun-zaki. Duk da yake dai bata da alaka da lemun-zaki, kamshin ciyawar mai karfi da dandano yayi kama dana lemun-zaki (amma bata da zaki). Ana samun ciyawar a kasashe masu yanayin zafi ko yanayin dumi. Anfi yawan amfani da ita a kasashen Asiya, Afurka da Australia . Haka kuma, anfi yawan amfani da wannan ciyawa a kasashen Asiya wajen girki. A kasar Indiya kuwa akanyi amfani da ita a matsayin maganin gargajiya (herb). Ana amfani da busassar ciyawar ko danyarta domin amfani na daban-daban. Kuma anfi amfani da ita wajen hada shayi , miya ko kori (curry) domin ta zamo hadin kayan kamshin girki. Ana samun manta (lemongrass oil) a kasuwa wanda shima ake amfani dashi na daban-daban.
Amfaninta:
Mai yiwuwa ne kana da wannan shuka a gida ko a lambunka , koma kana amfani da ita, to amma baka san ainahin amfaninta taba ga lafiya, kawai dai ka dauketa shuka ce domin k'awata gida, ko filebo maisa kamshi a kofin shayin ka a lokacinda kake kurɓawa. To ka bude idanunka, domin kuwa wannan ciyawa amfaninta ya wuce na adon gida kadai ko kamshin shayinka da kake jin dadin sha saboda dandano da kamshin da take baka a lokacin da kayi amfani da ita. Ciyawar Lemongrass nada ado da zata iya yima lafiyarka domin inganta ta. Wasu daga cikin amfanin wannan ciyawa mai albarka sun hada da:
1. Kariya daga ciwon-daji/kansa (Anti-cancer). Shukar lemongrass nada sinadari mai kamshi na "citral", wanda binciken kimiyya ya nuna cewa yana kashe kwayoyin halitta da ciwon kansa ya harba a jiki (cancer cells). Haka kuma yana inganta lafiyar kwayoyin halittar jiki gaba daya (improving cellular health).
2. Karin-jini da hana rashin-jini (Anaemia). Lemongrass nada sinadarin "iron" mai yawa, wato sinadari maisa karin-jini domin cikakkiyar lafiya da kuma hana wasu matsalolin rashin jini.
3. Rage hawan-jini (Reducing high blood pressure). Yawan sinadarin "potessium" a cikin lemongrass, sinadarin mai inganta lafiyar zuciya, koda da sauran sassan jiki, na taimakawa wajen hana hawan-jini, cututtukan zuciya, mutuwar sashen jiki, ciwo kansa, matsalolin rashin narkewar abinci da rashin haihuwa, cikin yardar Allah.
4. Kariya da hana girman kananan halittu masu haddasa cututtuka a jiki (Anti-septic) da kuma hana kumburi, wuri yayi ja, da radadin ciwo a jiki (Anti-imflammatory), musamman taimako ce ga masu ciwon gabobi da sassan jiki da sauransu (gout, arthritis, etc).
5.Yaki da cututtukan bakteriya dana fangas (Anti-bacterial and anti-fungal). Don haka, tana maganin zazzabin cizon-sauro da taifot (Malaria and typhoid) [yi shayi] , da sauransu. Haka kuma, tana maganin cin-ruwa na yatsun kafa da makero [yi amfani da manta] da sauransu ( athlete's foot, ringworm, etc).
6. Maganin mura, zubar hanci da hawaye, kaikayin ido, atishawa, toshewar hanci (Cold,flue and hay fever).
7. Tace duk wani abu mai guba ga jiki , musamman na abinci, ko wani abu mai cutarwa da fitar dasu daga jiki (Detoxifying). Tana tsaftace hanta, koda, mafitsara da sauransu.
8. Inganta bacci / yakar da rashin bacci (Fighting insomnia). lemongrass nada tasiri wajen kwantar da hankali da fada da rashin bacci domin samun cikakkiyar lafiya.
9. Taimako ga masu ciwon-suga (Diabetes). Tana rage yawan suga cikin jini, tsarkake saifa da inganta aikinta.
10. Inganta kwalwa (Improving nervous system). Lemongrass na taimakawa kwalwa wajen maida hankali don lakantar karatu, rike karatun da kuma taimakawa wajen sarrafa karatun/ilimi. Sinadarin "magnesium", "phosphorus" da "folate" da ake samu a cikin ciyawar nada tasirin kyautata lafiyar kwalwa.
11. Rage kiba (Weight loss). Shan lemongrass musamman a shayi na narkarda kitshe. Tana sanya yin fitsari akai-akai a lokacinda take fitar da duk wani abu mai yawa da jiki baya bukata wanda zai iya cutar da lafiya.
Da sauransu.
Medical Disclaimer: Wanda ya rubuta wannan bayanai ba likita bane, mai bincike ne kawai akan magungunan gargajiya, masani akan abinda ya rubuta sakamakon bincike daya gabata. Wannan bayanin amfanin ciyawar lemongrass da duk kanin bayanan magunguna daya wallafa a wannan shafin yanar gizo, baya nufin masu matsalolin lafiya zasu iya barin yin amfani da magungunan da aka basu a asibiti ba domin su lazimci yin amfani da maganin gargajiya, a maimakon magungunan. A nemi shawarwarin likita da masana ilimin maganin gargajiya akan yanda za'a iya amfani da magungunan da kuma sanin wanda zai iya amfani da ciyawar da wanda bazai iya amfani da ita ba wasu lokuttan.
0 Comments