MANUFOFIN KARA AURE.




Kishi wata dabi'a ce da Allah ya halicci mata akanta, Nana A'isha tanacewa :"Ban taba yin wani kishi ba, irin kishin da na yiwa Khadijah, kuma ban taba ganinta ba, saboda yadda na ji Annabi s.a.w yana ambatonta" Bukhari 1388
Kishi mai tsafta, shi ne : kishiya ta yi rige-rige da kishiyarta, wajan kyautatawa mijinsu, akwai hikomin masu dimbin yawa da suka sa shari'ar musulunci ta yi umarni da Karin aure, ga wasu daga ciki :

1. Musulunci ya yi kallo na adalci zuwa ga mata gaba ki dayansu, don haka sai ya tausaya musu, ya umarci maza su kara aure, saboda mata sun fi maza yawa, idan har kowa ya tsaya a mace guda, ina za'a kai matan da mazajansu suka mutu, da wadanda aka saka ?

2. Allah ya azurta wasu mazan da tsananin sha'awa, don haka za su iyashiga wani hali duk lokacin da matarsu take haila ko kuma ta haihu, sai Allah ya halatta sama da mace daya, don karnamiji ya fada cikin haramun.

3. Wani lokacin za ka ga mutum ya auri matar da ba ta haihuwa, to kin ga idan har ba'a halatta Karin aure ba, sai mutum ya mutu ba shi da zuriyyar da Annabi s.aw. zai yi alfahari da ita ranar alkiyama.

4. Wani lokacin mace ta kan yi dogowar rashin lafiya, ta yadda mijintaba zai iya amfana da ita ba, to kin ga inhar ba'a hallata sama da mace daya ba, saidai ya sake ta kenan ya auro wata ! amma idan akwai wata zai iya hakuri ya cigaba da zama da ita a haka.

5. Annabi s.a.w. yana so ya yi alfaharida yawan al'umarsa ranar alkiyama, mata kuma yawancinsu daga sun wuceshekaru arba'in sai su daina haihuwa, sabanin namiji, kin ga idanaka ba shi dama ya kara aure, zai haifi 'ya'ya da yawa tun da shi ba ya gajiyawa da wuri.

6. Wata kishiyar za ta iya zama hutu gare ki wajan ayyukan gida.

7. ALLAH MADAUKAKIN SARKI SHI NE WANDA YA HALLATA KARIN AURE, YAFI KOWA SANIN HIKIMAR YIN HAKAN, SABODA HAKA YA KAMATA KI SALLAMAWA HUKUNC INSA YAKE 'YAR'UWA.
¨…¨…¨¨…¨…¨¨…¨…¨…¨¨…¨…¨¨…¨…¨¨

Post a Comment

0 Comments