Abubuwa 4 da ya kamata masoya su sani game da junansu kafin aure:




  by Muhammad Auwal:

Sanin kowa ne aure wani abu ne da ake yi da nufin zama dindindin, aure mu’amala ce da ake kullawa tsakanin namji da mace da zimmar zasu kula da junansu, kuma su zauna tare. Sai dai, dole ne yayin da ake soyayya tsakanin mace da namiji, ya kasance akwai bayanan da kowanne zai bayyana ma abokin soyayyarsa domin a samu daman fuskantar alkibla daya. 

Ga wasu daga cikin muhimman batutuwa guda hudu da ya kamata masoya su yi a tsakaninsu domin samun cikakken fahimtar juna, kamar yadda TheCables ta kawo su; 

Abubuwa 4 da ya kamata masoya su sani game da junansu kafin aure Hoto:TheCable Source: 

UGC Burin rayuwa: Dole ne masoya su fahimci burace buracen abokan soyayyarsu, ta hanyar kokarin jin na su, tare da bayyana musu na su. 

Kamar su wani aiki kake so/kike son yi bayan an yi aure.

 Ya kamata masoya su fayyace ma junansu abin da suke muradin cimmawa a gaba yayin da suke zaman aure, domin da haka ne zasu taimaki juna, tare da shawartar juna don cimma burin. 

Tun da wuri, idan har burace buracen masoyan bai dace da ra’ayin juna ba, sai a samu maslaha, idan kuma bai yiwu ba, shi kenan, sai a rabu, Allah Ya hada kowa da rabonsa. 

Yara da tarbiyyarsu: Ra’ayi ya bambanta tsakanin mutane game da adadin yaran da kowa yake muradin haihuwa a aure, da kuma tsarin tarbiyyar da kowa yake da muradin daura yaransa a kai.

 Don haka ya kamata masoya tun kafin su yi aure su tattauna batun iyali, yara nawa suke so, batun tazarar haihuwa, yanayin tarbiyyar da zasu baiwa yara, daga nan zasu fahimci junansu. 

Kudi da hanyoyin samun kudi: Dole ne akwai batun kashe kudi a lamarin aure, kudi na taka muhimmiyar rawa a aure, wasu lokuta kudi na zaunar da aure, rashin sa kuma na lalata zamantakewar aure.

 Don haka yake da kyau masoya su san aikin da suke yi, domin tabbatar da halaccinsa da ko akasin haka, idan na gyara ne sai a gyara, idan kuma akasin haka ne, toh ana iya rabuwa. Kamar yadda ya kamata mace ta san sana’ar mijinta, shi ma ya kamata ya san nata, bashin dake kansu, nawa ke shigo musu a shekara, nawa suke kashewa, da sauransu. 

Addini: Tattauna batun addini na da matukar muhimmanci a tsakanin masoya masu shirin auren juna, baya ga addini, dole ne masoya su fahimci akidar junansu don gudun samun matsala a gida. 

Masoya su bayyana ma junansu tsarin addini da akidarsu, tare da irin ayyukan Ibadan da suke yi domin sanin yadda za su tsara rayuwarsu tare.

 Daga karshe, manufar sakon nan shi ne masoya su tattauna batutuwa da dama masu muhimmanci kafin su kai ga amince ma junansu da aure don gudun yin kitso da kwarkwata.

Post a Comment

0 Comments