By Idris Aliyu Daudawa
Ciwon ciki lokacin da ake yin jinin al’ada wani abu ne wanda yake da matukar matsala matsala ne da kuma yawancin mata, ke fama da shi. Mafi akasari ‘yan matan da su ka fara yin al’ada sabuwa, sun fi fama da shi. Idan mace na girma matsalar kan ragu ne, har in ma ta yi sa’a ta rabu da ita gaba daya.
Dalilin da suke kawo shi:
Matsuwar mahaifa (Uterus Contraction): A lokacin da mace ke fama da jinin al’ada mahaifarta kan matsu, bayannan kuma sai ta takura hanyar jinin da ke kusa da ita, wannan takurar na hana iskar odygyn shiga mahaifar na wani kankannen lokaci. Wannan rashin iskar shi ke kawo wannan ciwon ciki.
Wasu da ga cikin wadanda suka fi fama da shi a cikin mata sun hada da:
‘Yan mata kasa da shekara 20
‘Yan mata da ke fara balaga daga Shekara 11 ko kasa da haka
Zubar da jinni mai yawa yayin al’adar
Rashin haihuwa
Alamomin ciwon cikin kan zo da wa su abubuwa kamar haka:
Ciwon baya da cinyoyi
Tashin zuciya da amai
Hada zufa
Jin Jiri
Gudawa ko sakakken bayangida
Daurewar ciki (constipation)
Ciwon kai
Lalacewar ciki (bloating)
Wasu da ga cikin hanyoyin magance ita cutar a gida:
Zama cikin ruwa mai zafi na dan lokaci (hot bath)
Gasa kasan cibi da ruwa mai dumi ta hanyar amfani da ruwa mai zafi a gora ko tawul da makamantansu
Kokarin ganin likita in har abin ya tsawaita
Wasu daga cikin hanyoyin da za a bi don rage shi:
Yawaita cin ‘ya’yan itace (fruits) da ganye (begetables)
Rage cin abinci mai maiko, abinci mai caffeine (sinadarin kofi) da gishiri da kayan zaki (sweet)
Motsa jiki lokaci zuwa lokaci
Rabuwa da shan taba
Rage shiga damuwa (stress)
Daga karshe duk lokacin da matsala ta dame ki kar ki zauna a gida. Ki yi kokarin ganin likita cikin gaggawa.
0 Comments