Daga cikin manyan ibadu da ake aiwatar da su a cikin watan Ramadan don neman ƙarin kusanci ga Allah ﷻ, kuma waɗanda suke da lada mai yawa, sun haɗa da ciyarwa da shayarwa a cikin watan azumi, wato baiwa mai azumi ko a tanadar masa abin da zai yi buɗa-baki da shi na ci ko na sha, da abin da zai yi sahur da shi gwargwadon abin da mutum zai iya tare da kyakkaywar niyar neman kusanci ga Allah ﷻ da wannan ciyarwar da shayarwar.
Misali, wani zai iya yin kunu da ƙosai, wani kuma zai iya yin koko, wani zai iya yin lamurje, zoɓorodo ko kunun zaki, wani kuma zai iya dafa shinkafa, wani kuma zai iya bayar da ruwan sanyi, wani kuma zai iya bayar da wani abu na ci ko na sha, kowa dai gwargwadon abin da zai iya bayarwa, da adadin mutanen da ya ga zai iya ciyarwa, wani kullum zai iya yin abincin mutum goma, ma’ana, da abincin da ruwan shan na mutum goma.
Ka ga idan kullum zai iya ciyar da mutum goma, idan Ramadan ya wuce tamkar ya ciyar da mutum ɗari uku kenan. Wani kuma zai iya ciyar da mutum biyar, kullum har ƙarshen Ramadan, wanda ya ciyar da mutum biyar kullum har ƙarshen Ramadan kamar ya ciyar da mutum ɗari da hamsin kenan.
Idan kuma abincin mutum ɗaya tak zai iya ciyarwa a kullum ka ga ya ciyar da mutum talatin kenan.
Falalar da ke cikin aikata hakan ita ce, wanda duk ya ciyar ko ya taimakawa mai azumi ya yi buɗa baki ko ya yi sahur, Allah ﷻ zai ba shi ladan ya yi azumi cikakke, wato kenan idan ka ciyar da mutum biyu za a ba ka ladan azumi biyu, idan ka ciyar da mutum uku za a ba ka ladan azumi uku, wato kenan adadin mutanen da ka ciyar a watan Ramadan shi ne adadin ladan azumin da za a ba ka, ban da ladan naka.
Azumin da ka yi shi ma yana nan sai a haɗa maka tare da waɗancan.
Don haka ana buƙatar duk wani Musulmi ya zage damtse ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen ciyarwa, domin wata ne na falala da samun lada, musamman ma idan muka kalli falalar da ciyarwa take da shi.
A cikin siffofin da Allah ﷻ ya lissafa na mutanen kirki da za su shiga Aljannah, akwai waɗanda Allah ﷻ ya bayyana su inda yake cewa:
﴿وَيُطْعِمُونَ الطَّعَامَ عَلَى حُبِّهِ مِسْكِينًا وَيَتِيمًا وَأَسِيرًا إِنَّمَا نُطْعِمُكُمْ لِوَجْهِ اللَّهِ لَا نُرِيدُ مِنْكُمْ جَزَاءً وَلَا شُكُورًا إِنَّا نَخَافُ مِنْ رَبِّنَا يَوْمًا عَبُوسًا قَمْطَرِيرًا فَوَقَاهُمُ اللَّهُ شَرَّ ذَلِكَ الْيَوْمِ وَلَقَّىهُمْ نَضْرَةً وَسُرُورًا﴾ ()
Ma’ana: “Suna ciyar da abinci irin wanda suke so, suna ciyar da shi ga miskini da maraya da kuma ribatacce. (Suna cewa), Lallai haƙiƙa mu muna ciyar da ku ne domin neman fuska Allah ﷻ, ba ma neman sakamako a gare ku ba ma neman ku gode mana. Mun yi haka ne saboda muna jin tsoron wata rana da Ubangiji ﷻ zai kawo ta mai ɗaure fuska. Sai Allah ﷻ ya tsare su sharrin wannan rana.” (saboda imaninsu da ciyarwa da suke yi).
Sannan ciyar da abinci da shayar da ruwa da kuma taimakon mai jin yunwa suna daga cikin abin da za su jawo mutum ya zo daga cikin ‘yan dama-dama a ranar ƙiyama. Allah ﷻ yana cewa:
﴿أَوْ إِطْعَامٌ فِي يَوْمٍ ذِي مَسْغَبَةٍ يَتِيمًا ذَا مَقْرَبَةٍ أَوْ مِسْكِينًا ذَا مَتْرَبَةٍ ثُمَّ كَانَ مِنَ الَّذِينَ آَمَنُوا وَتَوَاصَوْا بِالصَّبْرِ وَتَوَاصَوْا بِالْمَرْحَمَةِ أُولَئِكَ أَصْحَابُ الْمَيْمَنَةِ﴾ ()
Ma’ana: “Ko kuma ciyarwa a cikin wata rana ma’abociyar yunwa, wadda suka yi ga maraya ma’abocin kusanci, ko talaka ma'abocin turɓaya, sannan kuma ya kasance daga cikin waɗanda suka yi imani, suka yi wasiyya da haƙuri suka yi wasiyya da rahama, waɗannan su ne waɗanda suke ‘yan dama.”
Sannan yana daga dalilan da yake jawo shiga Aljannah ciyar da abinci. Abdullahi Ɗan Amru Ɗan As رضي الله عنهما ya ruwaito hadisi cewa, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Ku ciyar da abinci, ku sadar da zumunta, ku yi sAllah da daddare lokacinda mutane suke barci, za ku shiga Aljannah da aminci.” Imam tirmizi ya ruwaito.
Haka nan hadisi ya zo daga Barra’u Bn Azib رضي الله عنه ya ce, wani mazaunin ƙauye ya zo ya cewa Ma’aiki ﷺ ya Ma’aikin Allah ﷺ gaya min aikin da zai shigar da ni Aljannah ya nesanta ni daga shiga wuta. Sai ya ce, “Ka ciyar da mai jin yunwa, ka shayar da mai jin ƙishirwa.” Imamu ahmad ne ya ruwaito shi..
Haka nan ya tabbata daga abin da yake tserar da mutum daga shiga wuta ciyar da dabino, wato ko da tsagin dabino ne, domin Ma’aikin Allah ﷺ ya ce, “Ka ji tsoron shiga wuta koda da tsagin dabino ne.” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
Abdullahi Ɗan Amru Ɗan As رضي الله عنهما ya ce, wani mutum ya tambayi Ma’aiki ﷺ wane musulunci ya fi alkhairi? Sai ya ce, “Ka ciyar da abinci ka yi sallama ga wanda ka sani da wanda ma ba ka san shi ba.” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
Haka nan hadisi ya zo Manzon Allah ﷺ ya ce, “Aikin da Allah ﷻ ya fi so shi ne, ka sawa Musulmi farin ciki a zuciyarsa, ko ka ya ye masa baƙin ciki, ko ka kare masa yunwa ta hanyar ba shi abin da zai ci ko ya sha, ko kuma ka biya bashin da ake binsa.”
Idan muka lura ashe babu aikin da Allah ﷻ Yake so fiye da irin waɗannan ayyukan guda huɗu. Wato ka sanya wa mutum a cikin farin ciki, ka ya ye masa damuwa, ka kore masa yunwa, ka biya masa bashi.
Haka nan dai ciyar da abinci yana daga cikin ayyukan da Allah Yake so, domin Ma’aiki ﷺ ya ce, “Mafi alkhairin ku shi ne wanda yake ciyar da abinci ga ma buƙatansa.” Imamu Ahmad ne ya ruwaito shi.
Hadisi ya zo a cikin musnad na imamu Ahmad daga Ummina A’ishah رضي الله عنها cewa, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Haƙiƙa Allah ﷻ Yakan raini dabinon ɗayanku da lomar ɗayanku, kamar yadda ɗayanku yake rainon raƙuminsa ko ɗan raƙuminsa, har sai ya kai kamar girman dutsen uhud.”
Kuma ciyarwa tana daga cikin abin da yake ƙara kusanta mutum ga Allah ﷻ, kamar yadda ya zo a sahihi Muslim daga Abu Hurairahh رضي الله عنه cewa, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Allah ﷻ Ya faɗa a hadisil ƙudsi cewa, “Ya kai Ɗan Adam na yi rashin lafiya ba ka duba ni ba.” sai ya ce, ya zan je dubiyar ka bayan kai ne mahaliccin talikai? Sai Ya ce: “Ba ka san bawana wane ya yi rashin lafiya kuma ba ka je ka dubo shi ba? Ba ka san cewa da ka je dubiyar sa da ka same ni a wurinsa ba? Sai Allah ﷺ Ya ce, “Ya kai Ɗan Adam, na nemi ka ciyar da ni amma ba ka ciyar da ni ba.” Sai ya ce, ya zan ciyar da kai bayan kai ne Ubangijin talikai? Sai ya ce, “Ba ka san cewa kuma da ka ciyar da shi za ka sami sakamakon abin a wajena ba?” Imamu Muslim ya ruwaito wannan hadisin.
Haka nan ana ninninka lada ninkin-baninki ga wanda yake ciyarwa don Allah ﷻ. Imam Tirmizi ya ruwaito hadisi daga Nana A’ishah رضي الله عنها cewa, sun yanka tunkiya a gidan Ma’aiki ﷺ sai aka rabar da namanta, sai ya zamo abin da ya rage saura kArfata ɗaya. Sai Ma’aiki ﷺ ya tambayi Nana A’ishah رضي الله عنها “Mai ya ragu daga naman tunkiyar?” Sai ta ce, abin da ya ragu shi ne kArfata ɗaya, sai ya ce, “Kun sami ladan dukkanin naman tunkiyar nan amma ban da wannan kArfatar.” Ma’ana abin da aka bayar a waje shi ne ake da ladansa.
Haka nan da wannan ciyarwar ake samun taimakon Allah ﷻ domin Ummina A’ishah رضي الله عنها ta ce, yayin da Ma’aiki ﷺ ya haɗu da Mala'ika Jibriluعليه السلام a cikin kogo ya tsorata sosai, da ya zo ya sami Ummina Khadijah رضي الله عنها sai ta ce masa, ka kwantar da hankalinka, ka yi farin ciki, lallai Allah ﷻ ba zai taɓar da kai ba, har abada, (saboda dalilai kamar haka)
Na ɗaya: Kana sadar da zumunta.
Na biyu: Kana yin gaskiya a wajen magana.
Na uku: Kana ɗaukar nauyin wanda ba shi da shi.
Na huɗu: Kana tanadarwa mara shi.
Na biyar: Kana yin garar baƙi.
Na shida: Kana taimako a kan hanya ta gaskiya.” Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.
Waɗannan ayoyin Alqur’anin da hadisan da muka kawo suna bayyana mana falalar ciyarwa a cikin watan Ramadan da ma sauran watannin, da kuma garabasar da ake samu ga wanda ya ciyar ɗin.
💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧
Shirin Bada Ƙanƙarar Ruwa domin masu Azumi
Ku bada Sadaƙar Naira Ɗari biyar ₦500 kachal domin taimaka wa Bayin Allah yayin Buda Baki.
Za'a riƙa sayen a ƙallah Ƙanƙara ta Naira Dubu Biyu ƙosai na Naira Dubu Ɗaya kowace rana a rabama Mabukata domin rage radadin wannan zafin rana da muke ciki.
Ku bada taku Gudummuwar ta Lambar Asusun ajiya kamar haka:
Account number: 7810335410, Bank name: WEMA BANK, Account name: Sirrin rike miji
Allah yasa mudace ya Karbi Adduo'in mu da Ibadun mu yasa mudace da Alkhairan dake ciki wannan watan Mai Alfarma Amin.
Share ma sadaka ce 💧💧💧💧💧💧
Account number: 9101637863, Bank name: Sparkle Bank, Account name: Sirrin rike miji
0 Comments