RABI AHMAD MU’AZU
Wata sabuwar fitina da ta kunno kai da sunan yayi ce ta sa ni yin wannan rubutu domin fadakar da ’yan uwana mata, musamman ’yan mata da zawarawa.
Guguwar fititanar ta taso ne a daidai lokacin da al’ummar Musulmi ke fafutukar neman abin da za su ci da iyalansu a wannan wata mai alfarma na Ramadan, da ma kayan sallar iyalan nasu.
Ga duk mai bibiyar abubuwan da ake tattaunawa a kafafen sadarwa na zamani, zai lura da yadda matasa suka shagaltu ta da batun suturar yayi ta mata a lokacin Karamar Sallah mai zuwa, wato Abaya.
Daga masu bayyana kwadayinsu na mallakar rigar, zuwa masu ganin bai dace ba mata su tayar da hankalinsu kan lallai sai sun mallake ta don kece raini a sallah, sai tsokaci suke ta yi.
Ke ce sabon shiga a sanya Abaya
Babban abin tambaya a nan shi ne mene ne manufar kirkirar wannan sabon salon ado na yayi? Me kuma ya sa shi jan hankalin musamman mu mata?
Abaya dai ba wata bakuwar sutura ba ce da aka fara yanzu, mata sun jima suna sanya ta, tun ma kafin ta zama gama-gari.
Idan za mu iya tunawa a da can daga wasu kasashen Musulmi ake shigo da ita, don haka ta zama sai wance da wance.
Ina iya tunawa lokacin akwai ‘Dubai Abaya’, ‘Turkey Abaya’ da sauransu. A lokacin sai kin yi oda kin biya webil na jirgi kafin ta iso miki.
Ba yanzu da ta zama ‘gwanjon Kano’ ba, inda ake samun telolin gida suna satar fasahar na waje suna dinkawa.
Mahawarar sanya Abaya
An fara batun Abayar ne a cikin wata Ramada din da muke ciki, bayan mata sun fara daga hankalinsu a kan irin shigar kece raini da za a yi da Karamar Sallar nan; har ta kai ga batun yayin Abaya.
Shin mata sun zama ’yan amshin shata ne?
Wai me ya sa duk abin da ake so shaidan ya samu nasarar kada gangar shi sai dai a saka mata a sahun gaba?
Shin tunaninmu ne ragagge, ko kuma saboda mu ne gwanaye wajen yada abu kamar wutar daji?
A gefe guda kuma sai aka samu wasu mazan da suke kara ingiza mu, suna zolayar mu.
Shin Abayarki za ta burge?
Ni dai ban ga wata wayewa a kan batun saka Abaya ba.
Idan kin sa ta kin burge wasu, wallahi wasu ba za ki burge su ba, saboda su sun dade da daina yayinta.
Kowa da inda Allah Ya ajiye shi, kada fa mu takura cewa sai mun kai kanmu inda Allah bai kai mu ba.
’Yar uwa, a yadda rayuwar nan take, wasu ma lafiya suke nema ba su samu ba, wasu kuma abincin ma da za su yi buda baki gagarar su yake yi!
Kara Abaya ta sa ki zubar da mutuncinki
Mutuncinki da darajarkiya fi Abaya 100 wallahi!
Idan har mutuncinki ya zube a kan maula da wayo, to tabbas ya zube har abada, a lokacin Abayar taki ta dade da zama tsumma.
Bata lokaci kawai
A wannan lokaci da kasarmu ke fama da kalubalen tsaro da na tattalin arziki, maimakon mu mayar da hankali wajen dagewa da addu’a da neman gafarar Allah, sai faman shirme muke ta yi, muna bata lokacinmu da kudadenmu wajen yin muhawarar da ba za ta amfane mu ba.
Ba wai ina nufin kar a yi raha ba ne, amma mu takaita don Allah.
Wallahi wasu matan sun dauki maganar Abayar nan kamar abin a mutu, ko a yi rai – Sun sa shi a ransu kamar farilla.
Ba da Abaya ake kure adaka ba
Wata har gori take yi wasu cewa, duk wacce ba ta sa Abaya a sallar bana ba, ’yar kauye ce!
Ke mai kiran wata ’yar kauye, ke kuma Babbar Yarinya saboda kin sa Abayar Dubu 22, ki manta ne cewa akwai wata mai les ko shaddar Dubu 30 ko fiye da haka amma ba ta fariya?
Ya kamata ’yan uwa mata mu dinga yi wa kanmu fada tun kafin a yi mana.
Wallahi masu zuga mu, sun mayar da mu sakarkaru, abin dariya.
Na tabbata wata garin neman kudin sayen Abaya sai ta sayar da mutuncinta, a wurin da ba ta da sauran martaba da mutunci.
Amma ki tuna cewa ba a kanki za a fara sanya Abaya ba, kuma ba a kanki za a daina ba.
Idan kunne ya ji, jiki ya tsira!
Rabi Ahmad Mu’azu daga Jos, Editan Kungiyar Arewa Media Writers, reshen Karamar Hukumar Jos ta Arewa, Jihar Filato.
0 Comments