Daga cikin abin da ya kamata ga duk wani Musulmi mai hankali ya kama ya kula da shi sosai a cikin rayuwarsa gaba ɗaya a ko da yaushe, musamman ma a cikin watan Ramadan ƙari a kan salloli da zikirai, salati ga Annabi ﷺ da istigfari, shi ne dagewa a kan yin addu'a ba ji ba gani, domin Allah ﷻ Ya yiwa wannan al'umma ta Ma’aiki ﷺ alfarmar da bai yiwa watanta ba daga cikin al'ummatai.
Saboda matsayin addu'a da girmanta, da falalarta, a wajen Allah ﷻ umartar ta kawai ya yi da ta roƙe shi, shi kuma kai tsaye ya yi mata alƙawarin zai amsa mata nan take, babu gindaya wani sharaɗi bayan imani inda yake cewa:
﴿وَقَالَ رَبُّكُمُ ٱدْعُونِىٓ أَسْتَجِبْ لَكُمْۚ﴾ ()
Ma’ana: “Allah ﷻ Ubangijinku Ya ce ku roƙe ni (ni kuma) zan amsa muku.”
Sannan kuma ya yawaita zikirin Allah ﷻ, kamar yadda Allah ﷻ Yake cewa:
﴿فَٱذْكُرُونِىٓ أَذْكُرْكُمْ وَٱشْكُرُوا۟ لِى وَلَا تَكْفُرُونِ﴾ ()
Ma’ana: “Ku ambace ni (ni ma) zan ambace ku, ku gode min kada ku kafirce min.”
A wata ayar kuma Allah ﷻ Yana cewa:
﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱذْكُرُوا۟ ٱللَّهَ ذِكْرًا كَثِيرًا وَسَبِّحُوهُ بُكْرَةً وَأَصِيلًا﴾ ()
Ma’ana: “Ya ku waɗanda kuka yi imani ku ambaci Allah ﷻ ambato mai yawa, kuma ku yawaita tasbihi a gare shi safiya da maraice.”
A wata ayar kuma yana cewa:
﴿وَالذَّاكِرِينَ اللَّهَ كَثِيرًا وَالذَّاكِرَاتِ أَعَدَّ اللَّهُ لَهُمْ مَغْفِرَةً وَأَجْرًا عَظِيمًا﴾ ()
Ma’ana: “Da masu ambaton Allah ﷻ da yawa maza da masu ambaton Allah ﷻ da yawa mata, lallai Allah ﷻ Ya yi musu tanadin wata gagarumar gafara da wani lada mai girma.”
A wata ayar Allah ﷻ Yana cewa:
﴿وَٱذْكُر رَّبَّكَ فِى نَفْسِكَ تَضَرُّعًا وَخِيفَةً وَدُونَ ٱلْجَهْرِ مِنَ ٱلْقَوْلِ بِٱلْغُدُوِّ وَٱلْآصَالِ وَلَا تَكُن مِّنَ ٱلْغَٰفِلِينَ﴾ ()
Ma’ana: “Ka ambaci Allah ﷻ Ubangijinka a cikin ranka, kana mai ƙanƙan da kai, kuma a ɓoye ba tare da kwarmatawa ba, kada ka zamo daga cikin gafalallu.”
Abu Musal Ash’ari رضي الله عنه yana cewa, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Misalin wanda yake ambaton Allah ﷻ Ubangijinsa, da wanda ba ya ambaton Allah ﷻ Ubangijinsa, kamar misalin rayayye ne da matacce.” Bukhari ya ruwaito shi.
Amma a wata ruwayar ta Muslim cewa ya yi: “Misalin gidan da ake ambaton Allah ﷻ da gidan da ba a ambaton Allah ﷻ, kamar rayayyen gida ne da matacce.” ()
Haka nan Abud Darda’i رضي الله عنه ya ce, Manzon Allah ﷺ ya cewa sahabbai رضي الله عنهم, “Yanzu ba na ba ku labarin mafi alkhairin ayyukanku, kuma mafi tsarkinsa a wajen mamallakin ku, kuma mafi ɗaukaka a cikin darajojinku, kuma mafi alkhairi a gare ku daga ciyar da dinare da azurfa, kuma mafi alkhairi a gare ku daga ku gamu da maƙiyanku a filin daga su sare muku wuya kuma ku sare wuyansu ba? Sai sahabbai suka ce, eh, ya Manzon Allah ﷺ gaya mana, sai ya ce, “Shi ne ambaton Allah ﷻ.” ()
Abu Hurairahh رضي الله عنه yana cewa, Ma’aiki ﷺ yana cewa, Allah ﷻ Ya ce, “Ni ina nan tare da bawana, ina tare da shi idan ya ambace ni, idan ya ambace ni a cikin ransa, sai in ambace shi a cikin raina, idan kuma ya ambace ni a cikin wata jama'a, ni kuma sai in ambace shi a cikin wata jama'ar da ta fi tasa alkhairi, idan ya kusanto gare ni da taƙi ɗaya, ni kuma sai na kusanto gare shi da kamu ɗaya, idan kuma ya kusanto ni da zira'i ɗaya, ni kuma zan kusanto shi da kamu ɗaya, idan kuma ya zo min yana tafiya, ni kuma zan zo masa da sauri.” ()
An karɓo daga Abdullahi Ɗan Busrin رضي الله عنه ya ce, wani mutum ya ce, ya Ma’aikin Allah ﷺ Shari’o’in musulunci sun yi min yawa, inaso ka faɗa min wani abu da zan riƙe wanda zai tattaro min sauran gaba ɗaya, sai ya ce masa, “Kada harshen ka ya gushe yana ɗanye wajen ambaton Allah ﷻ.” ()
Haka nan Ummina A’ishah رضي الله عنها tana cewa, Manzon Allah ﷺ ya kasance yana ambaton Allah ﷻ a kowane hali yake ciki.” ()
Abdullahi Ɗan Mas’ud رضي الله عنه yana cewa, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Wanda duk ya karanta harafi ɗaya daga cikin littafin Allah ﷻ yana da ladan kyakkyawan aiki, kowane lada kuma za a ninka shi sau goma, amma fa ban ce, (alif–lam–mim) shi ne harafi ɗaya ba, a’a, (alif) harafi ne (lam) harafi ne (mim) harafi ne.” ()
Haka nan ya zo daga Uƙbata Ɗan Amir رضي الله عنه ya ce, wata rana Ma’aiki ﷺ ya fito muna a mazauninmu na Ahlus-Siffa a cikin masallaci sai ya ce da mu, “Wane ɗayan ku ne yake son ya yi sammako zuwa budhana, ko ya buga sammako zuwa aƙiƙu, ya zo da taguwa guda biyu masu tozo ba tare da ya aikata saɓo ko ya yanke zumunta ba?” Sai muka ce, ya ma’aiki Allah ﷺ muna son haka. Sai ya ce, “Yanzu ɗayan ku ba zai buga sammako zuwa masallaci ba, don ya koyi wata aya ko ya karanta wata aya ɗaya ko aya biyu daga cikin littafin Allah ﷻ ba? idan ya yi hakan sun fi masa alkhairi da a ba shi waɗancan raƙuman guda biyu.
Idan ya koyi aya uku ya fi a ba shi raƙuma uku, ya koyi ayoyi huɗu ya fi a ba shi raƙuma huɗu, da kuma adadin su daga raƙuma.” Ma’an duk san da ka ƙara aya adadin raƙuma za su ƙaru.
Duk waɗannan ayoyi na Alqur’ani da hadisai suna bayyana mana muhimmancin yawaita zikirin Allah ﷻ kowane iri ne, musamman yawaita hailala da karatun Alqur’ani.
Haka nan imamu Tirmizi ya ruwaito hadisi cewa, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Mutane ba za su zauna a wani majalisin da ba su ambaci Allah ﷻ a wajen ba, ba su yi wa Annabi ﷺ salati ba, sai wannan zaman da suka yi ya zame musu tawaya da asara, idan Allah ﷻ Yaga dama sai ya yi musu azaba, idan kuma ya ga dama sai ya yi musu rahma.”
Haka nan hadisi ya zo wanda Abu Dawud da Imamu Ahmad suka ruwaito, kamar yadda ya zo a sahihul jami'i cewa, “Babu wasu mutane da za su zauna har su tashi daga wannan majalisin amma ba su ambaci Allah ﷻ ba, sai sun tashi kamar suna warin mushen jaki, kuma sai hakan ya zame musu asara a ranar tashin ƙiyama.”
Lallai wannan yana nuna mana irin yawan falala da alkhairin da yake cikin yawaita ambaton Allah ﷻ a koda yaushe, musamman ma a cikin watan Ramadan. Shi ya sa malam Ibn ƙayyim ya kawo darajoji sama da (60) a cikin littafinsa da ya yi Alkalamuɗɗayyib, ya yi sharhi a kan alkhairin da mutum zai samu idan yana yawaita ambaton Allah ﷻ
FA'IDOJIN YAWAITA AMBATON ALLAH ﷻ
Daga cikin fa'idojin da ake rabauta da su idan ana yawaita ambaton Allah ﷻ akwai:
Yawaita ambaton Allah ﷻ yana korar sheɗan ya karya shi.
Yawaita ambaton Allah ﷻ yana jawowa mutum samun yardar Allah ﷻ.
Ambaton Allah ﷻ yana gusar da baƙin ciki da ɓacin rai daga zuciya, kuma yana jawo wa zuciya farin ciki.
Yawan ambaton Allah ﷻ yana ƙArfafa zuciya da jiki.
Ambaton Allah ﷻ yana jawowa mutum arziƙi.
Ambaton Allah ﷻ yana jawowa mai yinsa kwarjini a wajen halittar Allah ﷻ da kuma mutunci a wajen Allah ﷻ.
Ambaton Allah ﷻ yana jawowa mutum ya sami soyayya a wajen halittar Allah ﷻ da kuma uwa-uba soyayyar Allah ﷻ a gare shi, wadda kuma ita ce ruhin musulunci, domin idan ka samu Allah ﷻ yana sonka shi ai ka sami komai.
Ambaton Allah ﷻ yana sawa mutum ya riƙa ganin lallai fa Allah ﷻ yana ganin sa a duk inda yake, wannan kuma shi zai jefa shi a babin kyautatawa a tsakaninsa da Allah ﷻ da tsakaninsa da halittar Allah ﷻ kamar yadda Manzon Allah ﷺ yake cewa, “Kai bawa ka ji tsoron Allah ﷻ a duk inda ka sami kanka, idan ka yi mummunan aiki to ka yi ƙoƙarin biyo bayansa da kyakkayawa.”
Ambaton Allah ﷻ yana jawowa mutum komawa zuwa ga Allah ﷻ a kowane lokaci a kowane hali.
Ambaton Allah ﷻ yana gadarwa mutum kusanci da Allah ﷻ, don haka gwargwadon yawan zikirinka shi ne gwargwadon yadda za ka kusanta da shi.
Zikirin Allah ﷻ yana buɗewa mai yin sa babbar ƙofa daga cikin ƙofofin ilimi, domin duk lokacin da mutum ya yawaita ambaton Allah ﷻ yana ƙara samun wani ilimi ne daga Allah ﷻ, wani hadisi yana cewa, “Wanda ya yi aiki da abin da ya sani Allah ﷻ zai sanar da shi abin da bai sani ba.”
Zikirin Allah ﷻ yana gadarwa mai yin sa shi ma Allah ﷻ ya riƙa ambatonsa a cikin cincirindon Mala’iku, domin Allah ﷻ ya ce, “Ku ambace ni, in ambace ku.”
Zikirin Allah ﷻ yana gadarwa mai yin sa rayuwar zuciya, domin zuciyar da take ambaton Allah ﷻ ita ce mai rai, wadda bata ambaton Allah ﷻ kuwa ita ce matacciya.
Zikirin Allah ﷻ yana ba wa zuciya ƙarfi, ya ba wa ruhi ƙarfi da yakini da sakankancewa.
Zikirin Allah ﷻ yana washe zuciyar mai yin sa ya wanke ta ya tsaftace ta daga barin tsatsa, kamar yadda hadisi yake cewa, “Kowane abu yana da magoginsa, (burushinsa ko soso) magogin zuciya shi ne zikirin Allah ﷻ.
Zikirin Allah ﷻ yana kankarewa mutum saɓo, ya sarayar masa da shi.
Zikirin Allah ﷻ yana gusarwa mai yin sa ɗimuwa da gigita da kiɗima.
Zikirin Allah ﷻ yana yi masa komi, wato yayin da mutum ya sami kansa a cikin firgici da ruɗewa, to zikirin Allah ﷻ yana kawo masa gudummawa wajen sanya shi ya riƙa maimaita shi a wannan halin.
Shi zikirin Allah ﷻ duk lokacin da bawa ya kusanci Allah ﷻ da yin zikiri a halin jin daɗi, Allah ﷻ zai kawo masa agaji a lokacin da ya shiga cikin tsanani.
Zikirin Allah ﷻ yana tseratar da mutum daga azabar Allah ﷻ, ya kuma kusanta shi da rahamar Allah ﷻ.
Zikirin Allah ﷻ shi ne yake kawo saukar nutsuwa a zukatan al'umma, da kuma saukar rahama ga bayi gaba ɗaya.
Zikirin Allah ﷻ yana jawo Mala’iku su kewaye masu yin sa tun daga sama har ƙasa, kamar yadda hadisi ya tabbata a kan hakan.
Zikirin Allah ﷻ yana jawowa mai yin sa shagalta da shi ga barin giba da surutun banza.
Majalisin ambaton Allah ﷻ majalisin Mala’iku ne kai tsaye, ba majalisin gafala da rafkana da yasassun kalamai ba ne, ba matattarar sheɗanu ba ne.
Zikirin Allah ﷻ yana jawowa mai yin sa samun arziƙi mai yawa a duniyarsa da lahirarsa, hatta wanda ma ya zauna tare da shi zai sami wannan arziƙin.
Zikirin Allah ﷻ yana amintar da mutum daga asarar ranar ƙiyama, kamar yadda hadisi ya tabbata a kan hakan.
Idan mutum ya haɗa zikirin Allah ﷻ da kuka a keɓe, zai sabbaba masa shiga inuwar Al-Arshi a ranar ƙiyama, za su zauna tare da nagartattun bayin Allah ﷻ, kamar yadda hadisi ya tabbata a kan hakan.
Zikirin Allah ﷻ yana jawowa a baka fiye da abin da aka ba waɗanda suka roƙa, kamar yadda hadisi ya tabbata a kan hakan.
Zikirin Allah ﷻ shi ne mafi sauƙin ibada, shi ne mafi daɗin ibada, shi ne mafi darajar ibada.
Zikirin Allah ﷻ wani dashe ne a gidan Aljannah, wanda mai yin sa yake dasawa na wasu ni'imomi da darajoji da mai yin sa zai riska a gidan aljanna, kamar yadda hadisi ya tabbata a kan hakan.
Zikiri Allah ﷻ shi ne mafificin abin da za a ba wa mutum kyautarsa, wato wanda Allah ﷻ ya yi masa baiwar yin zikiri, lallai Allah ﷻ ya ba shi kyautar da ta fi kowacce kyauta daraja.
Dauwama cikin zikirin Allah ﷻ yana jawo aminci a kan harshen mai yin sa.
Mai yawan ambaton Allah ﷻ yana samun sauƙi a cikin rayuwarsa, wato dukkanin mu’amalolinsa na rayuwa Allah ﷻ zai sauƙaƙa masa su.
Ambaton Allah ﷻ haske ne a karan kansa, sannan kuma zai sabbaba wa mai yin sa samun haske a ruhinsa da rayuwarsa da mu’amalolinsa da cikin ƙabarinsa da filin ƙiyamarsa da cikin ma’auninsa da kan siraɗinsa.
Zikirin Allah ﷻ shi ne tushen komi.
Ambaton Allah ﷻ yana tattara wa mai yin sa abin da ya watse na amfanin duniya da lahira, yana kuma jawo masa alkhairin da ya yi nesa da shi, ya kawo masa shi kusa, ya kuma nesanta masa sharrin da yake kusa shi.
Zikirin Allah ﷻ yana farkar da zuciya daga barcin rafkana da gafala.
Zikirin Allah ﷻ wata bishiya ce da take haifarwa da mai yin sa ilimi mai yawa.
Mai yawan ambaton Allah ﷻ yana kusa da wanda yake ambaton, kamar yadda Allah ﷻ Yake cewa, “Allah Yana tare da masu tsoronSa, su ne masu kyautata ambatonSa.”
Shi zikirin Allah ﷻ daidai yake da yaƙi da takobi, daidai yake da ciyar da dukiya a tafarkin Allah ﷻ.
Zikirin Allah ﷻ shi ne tushen godiya, wato kenan duk wanda ya ambaci Allah ﷻ kamar ya gode masa ne.
Mafi girman daraja da martaba a cikin halittar Allah ﷻ shi ne wanda harshensa bai gushe ba, yana ɗanye wajen ambaton Allah ﷻ.
A cikin zuciya akwai bushewa da ƙeƙashewa, babu kuma abin da zai tafiyar dasu sai ambaton Allah ﷻ.
Zikirin Allah ﷻ waraka ne ga zuciya, kuma kariya ce.
Zikirin Allah ﷻ shi ne asalin soyayyar Allah ﷻ, gafala da rafkana kuma ita ce asalin ƙiyayyar Allah ﷻ.
Babu abin da ya fi jawo alkhairi kusa a cikin sauri, ko tunkuɗe sharri da bala’i nan take kamar zikirin Allah ﷻ.
Zikirin Allah ﷻ yana jawowa mai yin sa salatin Allah ﷻ da na Mala’iku, kun san kuwa wanda Allah ﷻ da Mala’iku suka yiwa salati ya rabauta.
Wanda yake son ya zauna a cikin dausayin Aljannah, to ya zauna ya lazimci majalisin zikiri.
Mazaunin da ake yin zikiri shi ne majalisin Mala’iku, babu wani majalisi da Mala’iku suke zama face majalisin da ake yin zikiri, kamar yadda ya zo a hadisi ruwayar Bukhari.
Allah ﷻ yana yin alfahari a cikin Mala’iku da mutanen da suke yin zikiri, kamar yadda ya zo a hadisi ruwayar Muslim.
Dukkanin ayyukan ibada an shar’antasu ne domin tsayar da Shari’a, saboda mai sAllah zikiri yake yi, mai azumi zikiri yake yi, mai hajji zikiri yake yi, mai zakkah shi ma ambaton Allah ﷻ yake yi, mai karatun Alqur’ani zikiri yake yi, mai salati ga Annabi ﷺ shi ma zikiri yake yi, duk dai wata ibada za ka ga tana da alaƙa da ambaton Allah ﷻ.
Mafi darajar nau'ukan ibada a wajen Allah ﷻ shi ne aikin da aka fi yawan ambaton Allah ﷻ a cikinsa, saboda haka azumin da aka fi yawan zikiri a cikinsa shi ya fi kowane azumi daraja, haka nan aikin hajjin da aka fi yawan zikiri a cikinsa shi ya fi kowane aikin hajji daraja, saboda haka dai aikin da aka fi yawan ambaton Allah ﷻ a cikinsa shi ne mafifici a wajen Allah ﷻ.
Yawaita zikirin Allah ﷻ yana mayema makwafin wasu ayyukan ɗa'ar da ba a sami damar yinsu ba.
Zikirin Allah ﷻ shi ne mafi girman abin da yake taimakon bawa, wajen bin Allah ﷻ domin shi yake sa bawa ya ƙaunaci Allah ﷻ ya ƙara jin tsoronsa, ya kuma sami nishaɗin biyayya a gare shi.
Zikirin Allah yana yayewa mai yin sa damuwa da kuncin rai.
Zikirin Allah ﷻ yana tafiyar da tsoro daga cikin zuciyar mai yinsa.
Zikirin Allah ﷻ yana ƙara ƙarfin zuciyar mai yin sa, ya bata nutsuwa a tsakanin ta da Ubangijinta ﷻ.
Dukkanin ayyukan lahira ayyuka ne na gasa a tsakanin bayi, don haka masu ambaton Allah ﷻ su za su tserewa kowa a cikin gasar.
Zikirin Allah ﷻ yana tseratar da mai yin sa daga shiga cikin munafuƙai, domin Allah ﷻ ya zargi munafuƙai da cewa, ba sa yin zikiri sai kaɗan. Ka’abu رضي الله عنه ya ce, wanda ya yawaita ambaton Allah ﷻ ya kuɓuta daga munafunci.
Wannan kaɗai ya nuna mana muhimmancin mutum ya dage wajen yawaita zikiri da addu’a a koda yaushe tsakaninsa da Allah ﷻ musamman ma a watan Ramadan.
Bugu da ƙari, wajibi ne ga duk wanda zai yi zikiri, ko zai ambaci Allah ﷻ da nau’in abin da ake cewa zikiri, wajibi ne ya ambaci Allah ﷻ ko ya kirawo Allah ﷻ ko ya roƙi Allah ﷻ ko ya yi wannan zikirin da sunayen Allah ﷻ masu tsarki, ko da sifofinsa kyawawa. Malamai sun ce, zikirin Allah ﷻ ya kasu kashi bakwai:
Yin zikirin Allah ﷻ da harshe, ta yadda harshen zai furta sifa daga cikin sifofinsa, kamar ya ce, ya Allahu, ya Rahmanu, ya Rahimu, ko kuma ya ce, La'ilaha illAllahu. ko ya ce, ya Hayyu ya ƙayyumu, ya Malikal mulki, HasbunAllahu wani’imal Wakilu. Da dai makamantansu wannann shi ake cewa zikiri da harshe.
Yin zikiri da zuciya, wato yin zikirin da harshe amma laɓɓa ba su motsa ba. Shi kuma wannan yana kasancewa ne, ta dalilin zuzzurfan tunani da Ɗan Adam zai yi a cikin hikimar samar da shi da sauran halitta, wanda wannan zai bayu zuwa ga samun hasken girman halarar zatinsa, mabuwayi, wanda zai nasu zuwa sauran gaɓoɓinsa, daga nan sai ya nitse a cikin ɗa'ar Allah ﷻ, ya manta da kowa da komi sai Allah ﷻ kawai.
Yin zikiri da ido, shi kuma ana samunsa ne a yayin da zuciya ta tuna da tsananin azabarsa da uƙubarsa gaba ɗaya, a matsayinsa na mahaliccin halitta, mamallakinta, mai ƙarfin iko a kanta da adalci.
Shi kuma Ɗan Adam raunanne mai saɓo, sai idaniyarsa ta kwararar da hawaye don girman zatin mahaliccinta, kuma mamallakinta, halin kasancewar ta tana cike da tsoro kamar yadda Allah ﷻ Yake cewa:
﴿وَیَخِرُّونَ لِلْأَذْقَانِ یَبْكُونَ وَیَزِیدُهُمْ خُشُوعًا﴾ ()
Ma’ana: “Kuma suna sulmiyawa ƙasa da fuskokinsu, suna kuka, saboda fahimtar abin da Alqur’anin ya karantar da su.” suratul isra'i: aya ta (109). A wata ayar kuma yana cewa:
﴿أَفَمِنْ هَذَا الَحَدِیثِ تَعْجَبُونَ وَتَضْحَكُونَ وَلاَ تَبْكُونَ﴾ ()
Ma’ana: “Shin daga wannan zancen ne kuke mamaki? Kuke sheƙa dariya ba kwa kecewa da kuka?.”
Zikirin kunne, shi kuma yana samuwa ne a yayin da mutum ya saurara, ko ya kasa kunnensa yana sauraron karatun Alqur’ani, ko hadisan Ma’aiki ﷺ, ko kuma wani wa’azi, ko wata nasiha da ake yi masa, ko wanin wannan, wannan nutsuwar da mutum ya yi yana jin abin da ake faɗa, abin kuma yana ratsa cikin zuciyarsa, jininsa, tsokar jikinsa, da yarda da abin da kunnuwan suka ji, wanda daga nan kuma sai ya fashe da kuka saboda miƙa wuya da ya yi ga Allah ﷻ, wannan shi ake cewa zikirin kunne kamar yadda Allah ﷻ Yake cewa:
﴿إِذَا تُتْلَى عَلَيْهِمْ ءايَاتُ الرَّحْمَنِ خَرُّوا سُجَّدًا وَبُكِيًّا ۩﴾ ()
Ma’ana: “Idan kuma aka karanta musu ayoyin Allah ﷻ mai rahama sai su sulmiya ƙasa su yi sujjada, suna kuka.”
Haka nan hadisi ya tabbata cewa, Ma’aiki ﷺ ya umarci Ibn Mas’ud رضي الله عنه da ya karanta masa Alqur’ani ya ji, sai ya ce, ya zan karanta maka Alqur’ani bayan kuma kai ake saukarwa da shi? Sai ya ce, “Ina son in ji shi ne daga bakin wanina.” Sai Ɗan Mas’ud رضي الله عنه ya karanta masa cikin suratun nasa’i, da ya zo daidai wata gaɓa sai karatun ya ratsa Ma’aiki ﷺ sai ya ce masa, “Tsaya haka, tsaya haka.” Sai Ibn Mas’ud رضي الله عنه ya ce, sai na waiga na ga ɓangarensa, sai na ga idanunsa suna zubar da hawaye yana kuka.” ()
Zikirin Allah ﷻ da hannu, shi kuma yana samuwa ne ta hanyoyi da dama. Misali, kamar yawaita kyauta da sadaƙa da yin jihadi don ɗaukaka kalmar Allah ﷻ da kuma rubuce-rubucen ilimin addini, domin Manzon Allah ﷻ ya ce, “Idan Ɗan Adam ya mutu, komi nasa ya tsaya cak sai dai abu uku, sadaƙa mai guɗana, da ɗa na kirki wanda zai yi masa addu’a, da kuma ilimin da ya rubuta ya bari.”
Zikirin ƙafafu, shi kuma yana samuwa ne ta dalilin tafiye-tafiye na ɗa’a, kamar tafiya aikin hajji, tafiya jihadin ɗaukaka addinin Allah ﷻ, tafiya neman ilimin addini don Allah ﷻ, tafiya domin hidima ga iyaye ko malaman addini na ƙwarai, tafiya domin sada zumunta, ko daidaita tsakanin mutum biyu da suka sami saɓani, da makamantansu. Allah ﷻ ya umarci Annabi Musa عليه السلام da ya ɗauri aniya ya tafi mahaɗar teku biyu domin haɗuwa da wani bawa daga cikin bayin Allah ﷻ wato Halliru, saboda Musa ya ga wasu abubuwa na mamaki cikin ƙudirar Allah ﷻ waɗanda za su sake ƙara masa wani ilimin akan nasa, domin hakan ya sa shi ya nitse a cikin tuna Allah ﷻ kamar yadda suratul kahfi ta zo da cikakken labarin yadda abin ya faru, kuma Imamul Bukhari ya ruwaito dogon hadisi a kan hakan.
Sannan kuma akwai hadisin Anas رضي الله عنه, da ya ce, Manzon Allah ﷺ ya ce,
))مَنْ عَادَ مَرِیضًا أَوْ زَارَ أَخًا لَّهُ فِي ﷲِ نَادَاهُ مُنَا دِیَانِ طِبْتَ، وَطَابَ مَمْشَاكَ وَتَبَوَّأْتَ مِنَ الْجَنَّةِ مَنْزِلًا((
Ma’ana: “wanda duk ya ziyarci mara lafiya, ko ya ziyarci wani ɗan uwansa wanda suka yi haɗuwar Allah ﷻ da shi, to wani mai kira daga cikin Mala’iku zai kira shi ya ce, Allah ﷻ ya yi maka albarka ya daɗaɗa rayuwarka a duniya da lahira, kuma Allah ﷻ ya yi albarka a cikin wannan tattakin naka, kuma ka yiwa kanka tanadin wani masauki na musamman a gidan Aljannah.” ()
Zikiri da ruhi (rai), shi kuma yana samuwa ne ta hanyar miƙa wuya da sallamawa gaba ɗaya ga Allah ﷻ da kallon hikimarSa a game da samar da halittarSa, kamar yadda Allah ﷻ Ya yi nuni a kan hakan, inda yake cewa:
﴿وَإِلَٰهُكُمْ إِلَٰهٌ وَٰحِدٌۖ لَّآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلرَّحْمَٰنُ ٱلرَّحِيمُإِنَّ فِى خَلْقِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَٱخْتِلَٰفِ ٱلَّيْلِ وَٱلنَّهَارِ وَٱلْفُلْكِ ٱلَّتِى تَجْرِى فِى ٱلْبَحْرِ بِمَا يَنفَعُ ٱلنَّاسَ وَمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مِن مَّآءٍ فَأَحْيَا بِهِ ٱلْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا وَبَثَّ فِيهَا مِن كُلِّ دَآبَّةٍ وَتَصْرِيفِ ٱلرِّيَٰحِ وَٱلسَّحَابِ ٱلْمُسَخَّرِ بَيْنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلْأَرْضِ لَآيَٰتٍ لِّقَوْمٍ يَعْقِلُونَ﴾ ()
Ma’ana: “Ubangijin ku ﷻ, Ubangiji ne guda ɗaya, babu wani abin bautatawa da gaskiya sai shi, mai rahma ne mai jinkai. Lallai haƙiƙa a cikin halittar sammai da ƙassai da kuma sassaɓawar dare da rana, da jiragen da suke kai-komo a cikin teku suna ɗauke da abubuwan da suke amfanar mutane, da kuma abin da Allah ﷻ ya saukar daga sama na ruwa, sai ya raya ƙasa da shi bayan mutuwarta, ya kuma yaɗa dukkanin dabbobi a cikinta, da kuma sarrafa iskoki, da giza-gizan da aka horesu a tsakanin sama da ƙasa, lallai a cikin samuwar waɗancan abubuwan akwai ayoyi ga ma’abota hankali.”
Allah ka saka mu cikin masu ambaton ka da yawa.
0 Comments