YADDA ZAKI HADA KALOLIN MIYA:


Miyar Ogno

Ingredients

Nama
Kifi danye da busasshe 
Ogbono 
Ganda 
Kayan miya
Man ja 
Maggi da gishiri 
Curry da tafarnuwa
Preparation:

Ki tafasa namarki da gishiri, tafarnuwa, albasa, ki soya man ja amma kadan, ki zuba markadadden kayan miyarki a kai, su ma ba da yawa ba, idan ya soyu sai ki zuba dakakken crayfish kamar cokali biyu, ki zuba busasshen kifinki da kika gyara, ki zuba ruwa a kai, idan ta dahu sai kisa baking powder kadan dan tayi yauki sosai, dama kin sulala danyen kifi kin bare, kin cire kayar, kin gutsuttsura, shi ma sai ki zuba, ki rufe zuwa minti biyar ko goma shike nan kingama miyarki.

Miyar Shuwaka

Ingredients:-

Nama
Shuwaka 
Busasshen kifi 
Albasa
Tafarnuwa 
Kayan miya
Thyme da curry 
Maggi da gishiri 
Man ja
Preparation:

Ki wanke shuwakarki idan ba kya son dacin da yawa, sai ki dinga murje ta kina mutsittsike ta kina tace ruwan da rariya, sai kinyi kamar sau biyar ko sau shida, in kuma kina son dacin sosai sai ki wanke sau biyu ki tafasa namarki da thyme, da albasa da tafarnuwa da gishiri, ki zuba markadadden kayan miyarki da soyayyen man janki a kan tafasasshen namanki, idan ya dahu kamar minti bakwai, sai ki zuba shuwakarki, da gyararren busasshen kifinki, da yankakkiyar albasarki, da maggi, gishiri da curry, ki rufe tayi ta dahuwa, ba'a so tayi ruwa anfi sonta sa kauri.

Miyar Kantu (Ridi)

Ingredients

Kantu (ridi)
Nama
Kifi busashshe
Albasa
Attarugu
Ugwu or Alayyahu
Maggie
Salt
Thyme
Spices
Mai
Preparation

Zaki tafasa namanki da seasoning da spices saiki soya kayan miyarki acikin mai saiki zuba namanki wanda kika tafasa ki sanya har da ruwan da kika tafasa naman acikin kayan miyar saiki sanya kifin ki busashshe bayan kin gyara shi da ridin ki bayan kin daka shi watau (kantu) wadda akeson yanwan shi yakai kamar one cup saiki rufe tukunyar ki barshi ya dahu zuwa kamar 20 mnts saiki yanka ganyenki ki xuba ki barshi zuwa kamar 5mnts shikenan kin gama.

Miyar Kifi

Ingredients

Kifi sukumbiya
Tattasai
Attaruhu
Cabbage
Albasa
Curry
Maggi
Man ja ko Man gyada
Preparation

zaki wanke kifinki da lemon tsami ko toka domin fidda qarninsa da kuma yaukin dake jikinsa sai ki yanyanka amma sai kinyi sauri domin idan kankarar kikinsa ta narke xai iya dagargaje miki wajen aikinsa, sai ki barshi yasha iska domin ya tsane, in ya tsane sai ki barbadeshi da maggie ki jerashi a farantin gashi kisa shi a oven idan kuma daki da oven din sai ki soyashi a mai amma karki yawaita juyashi gudun dagargajewa.

Idan yayi sai ki ajei ki dauko attaruhu da albasa tattasai da cabbage da kika yanyanka kika wanke ki dora kasko q wuta Kisa mai ki soyasu kisa maggie da curry idan sun fara hadewa jikinsu sai ki dan sa ruwa a ciki, sannan ki kawo kifin kisaa ciki yayi Kaman 10minutes saiki sauke, kisa mai ki soyasu kisa maggi da curry idan sun fara hade jikinsu sai ki dan sa ruwa a ciki, sannan ki kawo kifin kisa a ciki yayi kaman 10minutes saiki sauke

Miyar Kabeji Da Nama

yadda ake miyar kabeji mai nama. Wannan irin miya tana kara lafiya a jiki sannan tana da dadi idan aka hada ta da farar shinkafa ko da dafaffiyar doya da kuma farar taliya da sauransu. Yana da kyau uwargida ta koyi yadda za ta rika canza dandanon miyarta a koda yaushe. Samun canji a dandanon girki na da alaka da irin kalar magi da kuma kayan kanshin da ake sa wa a lokacin girkin.

Abubuwan da za a bukata

Kabeji
Nama
Man gyada
Attarugu
Albasa
Tumatir
Magi
Kori
Tafarnuwa
Preparation:

Da farko za a samu kabeji sannan a yayyanka manya-manya sannan a wanke da ruwan gishiri domin kashe kowace irin kwayar cuta da ke ciki sannan a yayyanka albasa da tumatir kwaya biyu kacal sannan a jajjaga attarugu da tafarnuwa.

Daga nan sai wanke nama sannan a silala da albasa da gishiri kadan bayan ta yi laushi, sai a yayyanka kanana sannan a soya sama-sama. Bayan haka, a dora tukunya a wuta, a zuba man gyada kadan sannan a zuba albasa da tumatir da kuma jajjagen attarugu da tafarnuwa a soya. Sannan a dauko naman a zuba ba tare da romon ba. A zuba magi da kori a gauraya a jira su tafasa sau daya sannan a zuba kabejin a gauraya a dan rufe. Bayan mintuna biyu, sai a sake budewa a gauraya sannan a rufe na tsawon mintuna uku sannan a sauke.

A dora a kan shinkafa dafa-duka zazzafa ko kuma farar shinkafa da makamancinsu. A ci dadi lafiya!

Miyar Egusi.

 ingredients.

Egusi
Ugo leave
Stock fish
Dried fish (bushashen kifi)
Kpomo (ganda)
Seasoning cubes Maggi
Palm oil (Manja)
Scott bonnet (attaruhu) naira
Onions .(albasa)
Beef meat (Naman saniya)
Daddawa yar kadan.
Spices kadan
Preparation.

Na jajjaga attaruhu na da albasa guri daya nasa manja a wuta yayi zafi sai na zuba attaruhu da albasa na dan da daddawa

soyasu kadan sai na kawo egusi na xuba a ciki na cigaba da juyashi occasionally har sai da manja ya ratso jikin egusi din sai na kawo ruwan tafashen nama na xuba na juyashi sosai sai na rufe.

Dama kin wanke kpomo (gandarki) ki dan dafata tayi laushi.

Sai ki bude tukunyarki sai ki xuba kpomo dinki ki kara ruwan zafi ki juya ki rufe bayan wasu mintina sai kisa beef meat dinki wato naman sa sai ki juya bayan minti kadan sai kisa stock fish da dried fish dinki ki juya ki rufe ki barshi y kara dahuwa sai kisa seasoning cubes da cray fish dinki dakakke ki juya sosai ki rufe xaki iya kara dafaffen ruwa kadan sai ki rufe ki barshi for some minutes sai kisa spices dinki ki Kawo ugu leaves dinki da kk wanke kk tsane ki xuba ki barshi live 5 minutes sai ki sauke.

Miyar Zogale

Kayan hadi

Zogale
Nama
Albasa
Attarugu,
Mai
Tattashe,
Tumatir
Gishiri
Seasonings of choice
Gyada markadadde
Preparation

Ki gyara zogale ki ajiyeta aside. Ki daura tukunya a wuta kisa mai inya danyi zafi kisa onion, meat, tomato, attarugu, tattashe ki Dan soyasu then add cube, salt da seasonings naki ki juya in suka soyu yayi Dan kauri sai kisa ruwa dai dai miyar da kikeso inya tafasa sai kisa gyadar in yadan nuna sai kisa zogale. Ki rufe in ya nuna ki sauke.

-Ana sa wake a miyar zogale tamafi dadi da wake. Idan zakiyi using wake bayan kin soya miyar ki sai ki kara ruwa kisa wake idan waken ta kusa nuna sai kisa zogale da gydarki su karasa nuna tare.

Miyar Ganda

Ingredients

Kpomo
Scotch bonnet
Onions
Onga
Spices
Manja
Maggi
Preparation

    Da farko na wanke ganda ta nacire duk wani baki na jikinta ta fita sosai sena wanketa na Dora akan wuta tafasa daya-biyu na xubar da ruwa in case ko da daci nasake zuba mata ruwan zafi na maidata wuta nasaka two paracetamol,data dahu sena taceta a colander nayi keeping dinta aside........sena dauko scotch bonnet dina da onions dina na yi grating dinsu sena dora mai dina a wuta na soya naxuba kayan miyana na soya nasaka onga da spices da maggi na barshi suka dan dahu seki zuba kpomo dina nasake mixing after some minutes nasauke

Post a Comment

0 Comments