Amfani Yin Hakuri Ga Dan Adam:





Allah SWT Ya ambato hakuri a cikin littafin Sa maitsarki na Alkurani har sau 90. Wannan yana nunawa duk wani Musulmi yadda Allah Ya dauki hakuri da matukar mahimmanci.

Babu wani abu na cimma rayuwa da mutum zai yi muddin bai hada da hakuri ba.

A tsari na Mahaliccin mu, hakuri shine daya daga cikin minzanin da ake iya auna mutum a lokacin da yake cikin wata matsi ko kuma walwala. 

Hakuri halayya ce wacce musulunci ya kwadaitar da ita sosai. Shine ikon jure wahala da nutsuwa yayin fuskantar matsala. Hakanan ana daukarta a matsayin kyakkyawa wacce zata girbi lada mai yawa, kamar yadda Allah s.w.t. ya fada a cikin Alqur'ani:

Ka ce: (Allah Ya ce): "Yã bãyĩNa waɗanda suka yi ĩmãni!Ku bi Ubangijinku da taƙawa. Waɗanda suka kyautata a cikin wannan dũniya sunã da sakamako mai kyau, kuma ƙasar Allah mai fãɗi ce. Mãsu haƙuri kawai ake cika wa ijãrarsu, bã da wani lissãfi ba.
az-zumar 10.


Shi kansa shugabanci kowani irine bazai taba yiwuwa ba ga shugaba mara hakuri.
Shi yasa Allah Ya ce mana 
"Kuma Mun sanya shugabanni daga cikinsu, sunã shiryarwa da umurninMu, a lõkacin da suka yi haƙuri, kuma sun kasance sunã yin yaƙĩni da ãyõyinMu."as-sajdah 24.

Don haka ko a zama irin na aure dole sai an hada da hakuri.
Saboda yadda Allah Ya dauki masu yin hakuri da mahimmanci, shi ya sa ya tabbatar musu yana tare da su a sura da aya na 8:46.
Saboda yadda masu hakuri suke samun kusanci da mahaliccinsu a lokacin da suke cikin kunci da bakin ciki Allah Yace zai basu lada mara iyaka.

"Lallai, za a bai wa masu haƙuri ladansu ba da lissafi ba." (Alkurani 39:10)
Rashin hakuri a rayuwa yake saka mutane kasa samun muriyar da ya dace su samu. Mutane suna dauka a lokacinda suka shiga matsi tamkar Allah Baya sonsu ne ko Ya manta dasu. Hakan yasa su kasa hakuri yiwa Allah biyayya da ladabi daga karshe su kasa samun abunda suke buri su kuma hadu da fushin Allah.

Duk da damar da Allah SWT Ya bamu na ramuwar gayya dai-dai da yadda aka mana. Amma kuma Yace idan wanda aka cutar ya hakura hakan yafi masa da ya rama.

"Kuma idan kuka sãka wa uƙũba to ku sãka wa uƙũba da misãlin abin da aka yi muku uƙũbar da shi. Kuma idan kun yi haƙuri, lalle shĩ ne mafi alhẽri ga mãsu haƙuri."
an-naHl 126
Hakuri a rayuwa yakan jawowa mutum martaba, daukaka da kuma jarumta. Quran, 12:90. Shi yasa duk wanda aka sameshi da hakuri za a sameshi kuwa da wadannan abubuwan dana lissafa.
Masu hakuri suna cikin wadanda Allah Madaukakin Sarki Ya yiwa alkawarin gidajen Aljanna mafi daraja da daukaka. Ya kuma ce ga gaisuwa na musamman kuma an amincemusu.

 "Waɗannan anã sãka musu da bẽne, sabõda haƙurin da suka yi, kuma a haɗa su, a cikinsa, da gaisuwa da aminci."
al-furqaan 75.

Musulunci ya kawo hanyoyi guda uku da ake son Dan Adam yayi hakuri a kansu. Na farko shine mutum yayi hakuri akan ibadan da yake yiwa Allah bauta. A nan ne ma Allah Mabuwayi Yake kira ga Musulmai da suyi sallah cikin hakuri. 
Baka iya neman taimakon Allah sai ka hada da hakuri da kuma addu'a. 

"Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku nẽmi taimako da haƙuri game da salla. Lalle ne, Allah na tãre da mãsu haƙuri." 2:153
Hakuri na biyu kuma shine hakuri akan kin aikata duk wani abunda Allah Ya hana koda mutum yana da damar aikatawan amma yayi hakuri ya daure. 
"Suka ce: "Shin kõ, lalle ne, kai ne Yũsufu?" Ya ce: "Nĩ ne Yũsufu, kuma wannan shĩ ne ɗan'uwãna. Hƙĩƙa Allah Yã yi falala a gare mu. Lalle ne, shi wanda ya bi Allah da taƙawa, kuma ya yi haƙuri, to, Lalle ne Allah bã Ya tõzarta lãdar mãsu kyautatãwa."
Haka zancen yazo a suratul Yusuf aya na 90.

Hakuri na uku shine akan duk wata masifa da Allah Ya jarabbci mutum da ita. Muddin mutum zai yi hakuri akan wannan jarabawa, babu tantama zai samu babban sakamako yin wannan hakurin wajen Allah mai komai mai kowa. Kamar yadda yazo mana a suratul Lukman a lokacin da yake yiwa Dansa wa'azi sai yake ce Masa, 
"Yã ƙaramin ɗãna! Ka tsai da salla, kuma ka yi umurni da abin da aka sani, kuma ka yi hani daga abin da ba a sani ba, kuma ka yi haƙuri a kan abin da ya sãme ka. Lalle, wancan yanã daga muhimman al'amura."
Waɗannan sune hanyoyi uku da Allah Yake jaraba bayinsa domin ganin imaninsu a gareShi da kuma irin juriya da hakuri da suke da shi.
Allah Ya karama juriya da hakuri jarabawan da muke ciki. Ya kuma bamu hakurin cinye wannan jarabawan.

REGISTER YOUR PALMPAY 
https://palmpay8.page.link/GKSz

Post a Comment

0 Comments