: Falalar Dake Cikin Azumin Ramadaan
Daga Mahmud Isa Yola
Bismillahirrahmanirrahim,
Ina mana maraba zuwa wata mai alfarma watan Ramadaan. Muna Godiya ga Allah SWT da ya tsawaita rayuwar mu zuwa wannan lokaci, Allah Ya karbi Ibadun mu.
A rubutun mu na jiya mun kawo muku addu'an da musulmi yakamata yayi a lokacin da ya ga wata ko ya samu labarin ganin watan. A wannan rubutu na yau kuma, zamu kawo muku Ayoyi da hadisai wadanda suka bayyana falalar wannan wata mai albarka na Ramadaan.
Azumi daya ne daga cikin manyan ibadu a wurin Allah SWT Kaman yanda yazo a Qur’ani da Hadisan Manzon Allah SAW. Ga wasu daga ciki:
* Idan watan Ramadaan ya fara, ana rufe kofofin wuta kuma ana bude kofofin Aljannah, kuma ana daure shedanu. [ Bukhari Fat’h 3277]
* Azumtan Watan Ramadaan Daya yake da azumtan watanni goma. [Musnad Imam Ahmad, 5/280]
* Duk wanda ya azumci watan ramadaan da imani tare da yakinin samun yaddan Allah, za’a gafarta masa dukkan zunuban sa da suka gabata. [Bukhari, Fat’h 37]
* Azumi bai da Ibadan da yayi gogayya da shi a lada, kuma ba’a dawo da addu’an mai azumi. [Al-Bukhari, fat’h 1904]
* Mai azumi yana da lokuta guda biyu na jin dadi; daya lokacin da yayi buda baki, na biyu kuma lokacin da ya gamu da Ubangijin sa yana murna akan azumin da yayi. [Silsilatul Saheha 1797]
* Azumi zai yi ceto a ranar hisabi inda zai ce: “Ya Ubangiji, na hana shi abincin sa, da abubuwan da yake bukata bayyanannu a lokacin yini, a bar ni in cece shi” [Sahehul Targib, 1/407]
* Warin bakin mai Azumi yafi kamshi a wurin Allah SWT akan turaren Miski [Sahihu Muslim, 2/807]
* Azumi kariya ne da yake nesantar da mutum daga azabar wutan jahannama. [Saheehul Jaami 3880]
* Duk wanda yayi azumi na kwana daya saboda Allah, Allah SWT zai nesantar da fuskar sa tazarar shekaru 70 daga wuta. [Sahihu Muslim 2/808]
* Duk wanda yayi azumi na kwana daya don neman falalan Ubangiji, kafin ya buda baki ya koma zuwa ga Allah, to zai shiga Aljannah [Saheehul Targib 1/412]
* A cikin Aljannah akwai wani kofa mai suna Al’Rayyan, babu wadanda zasu shige ta sai masu azumi. [Sahihul Bukhari 1797]
* A cikin watan Ramadaan ne Allah SWT ya saukar da AlQur’ani, kuma a cikin ta ne daren Lailatul’Qadr yake, wanda Allah SWT yace daren yafi watanni dubu.
* Duk lokacin shan ruwa bayan azumi, Allah yana zaban bayin sa wadanda zai ‘yanta daga wuta. [Saheehul Targhib 1/419].
(WANNAN RUBUTU NA GUZURIN WATAN RAMADAN ZAI CIGABA DA ZUWA MUKU A SHAFUKAN JARIDUN HAUSA, TARE DA MAHMUD ISA YOLA.)
0 Comments