SHAWARWARI GA MATAN AURE :


・・
Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: ☏+2348037538596

①. Koyi sana’a: Yawan tambayar mijinki kudi na nufin kina takura masa.

 Domin ba kullum ake kwana a gado ba. Idan yau zai iya, mai yiwuwa gobe ba zai iya ba. To, mafi kyawu gare ki shi ne, ki koyi sana’a domin biyan wasu kananan bukatunki. Wata rana ma za ki taimake shi. Shin ba za ki yi farin ciki a ce mijinki ya nemi taimakon ki kin amsa ba?

2. Ba shi goyon baya: A matsayinki na matar aure, kada ki yarda ki goyi bayan makiyansa. Kada ki rika fadin sirrinsa a wajen wasu. Ki zama mai kare mijinki da kyawawan halayensa.

3. Rike baki: Idan kuna fada da mijinki kada ki rika fadin wasu maganganun da ba su kamata ba saboda bacin rai. Don haka ki guji yin kace-nace da mijinki. A duk lokacin da ya taso miki, ki yi shiru har sai ya huce, sannan ki same shi ki ba shi hakuri ko da ke ce da gaskiya, ta hakan za ki iya fahimtar da shi kuskurensa har a samo fahimta da daidaita a tsakaninku.

4. Kada ki manta ke wace ce: Komai matsayinki, kada ki manta cewa ke mace ce, kuma za ki zauna a karkashin namiji.

5. Kyautata wa iyaye da ‘yan uwan miji: Idan har kina da jituwa da ‘yan uwan mijinki, to tamkar kina jituwa da shi ne. Ki zama mai farantawa da kyautatawa da kuma taimaka wa ‘yan uwan mijinki. Ki dauke su tamkar naki ‘yan uwan.
Allah Ya sa mu dace.
Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: ☏+2348037538596

Post a Comment

0 Comments