GIDAN MIJINKI NAN NE WAJEN NEMAN ALJANNARKI:


📖 MATAN AURE 📖

Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: ☏+2348037538596

Ya kamata duk matar da ta tsinci kanta adakin aure, a wannan zamanin da muke
ciki,ta gode ma Allah. Ba don komai ba,idan ta duba zatanga wasu 'yan-mata irinta, sunfi ta kyawun halitta da iya ado, amma har yanzu basu samu mijin aure ba.

Don haka zai fi alkhairi a gareki ki Qudurce a cikin zuciyarki cewa:

 *GIDAN MIJINKI NAN NE WAJEN NEMAN ALJANNARKI.*

Ki rike mijinki hannu bibbiyu, ki kula da tsaftar jikinki da tsaftar Muhallinku.

Kuma ki zama ko yaushe ashirye kike domin biyan bukatar mijinki ko da bai nema ba.

Ki kiyaye MUGAYEN QAWAYE...

 Ba zasu rasa yi miki hassada ba. 
Tunda ke kin samu miji,su kuwa basu samu ba...
 Dole suyi miki hassada.Ki kiyaye sirrin mijinki,
kar ki gaya ma kowa..

Musamman ma kawayenki zasu so suji abinda yake faruwa..
 Don haka kar ki gaya musu.

Idan kuna da 'ya'ya to ki kula
dasu, ki kula da tsaftarsu. 

in ma 'ya'yan kishiyarki ne, to
ki kula dasu kamar yadda zaki kula da 'ya'yanki.

 Ki kiyaye dukkan amanonin
mijinki.

musamman ma iyayensa da 'yan uwansa da dukiyarsa.

Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: ☏+2348037538596

Post a Comment

0 Comments