📖 RAYUWAR MA'AURATA 📖
Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: ☏+2348037538596
Babbar matsala ta farko da ake samu a Rayuwar Aure shine idan ya kasance ka auri macen da bata dace da kai saboda daya daga cikin wadannan dalilai:
1. Macen da aka aura maka ita ba dan tana sonka ba, sai dan anfi qarfinta a gidansu.
2. Macen da ka aura wacce ka tabbata dan abin duniya (kudi, suna, sarauta dss) ta aure ka.
3. Macen da kaima ba dan soyayya ka aure ta ba sai dan sha’awa, kyawunta, dangantakarta dss.
4. Macen da kake tunanin ta aure ka ne kawai saboda bata da wani zabin.
5. Macen da bata gama yin hankali ba.
Wadannan da ma sauran dalilai da yawa wanda sukan kawo rashin dacewa tsakanin ma’aura suna kawo babbar matsala a Rayuwar Aure, wanda yawanci sai bayan anyi auren ake gane haka, lokacin da an riga an makara da ayi wani gyara akai.
Saboda haka ina kira garemu ‘Yan Mata da Samari mu daure mu yaqi zuciyoyinmu mu auri masoyan da muka tabbatar zabin zuciyoyinmu ne kuma sun dace damu domin samun ingantacciyar Rayuwar Aure!
Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: ☏+2348037538596
0 Comments