Shawarwari 10 Zuwa Ga Matan Aure, Zawarawa Da 'Yan Mata -



☏+2348037538596


Da sunan ALLAH mai gamammiyar rahama mai jinkai, tsira da aminci su tabbata ga Annabin rahama, Annabi Muhammadu (SAW) da alayansa, da sahabbansa, da duk wadanda suka bi tafarkinsu har ya zuwa ranar tashin al-kiyama.

 Bayan haka, shakka babu, a wannan zamani 'yan mata da zawarawa kai harma da matan aure suna cikin zullumi da tsoro da rashin kwanciyar hankali, saboda yadda auren su yake yawan mutuwa, bayan kuma, an dauki dogon lokaci ana soyayya a tsakani, kafin a yi auren.

Ga wasu shawarwari 10 wadanda idan matan suka yi la'akari da amfani da su da yardar ALLAH za'a samu kyautatuwar zaman aure.

1- Aurenki ya zama domin neman yardar ALLAh kikayi ba dan tara abin duniya ba.

2- Kada ki zama mai kwadayi wajen zaben mijin Aure.

3- Ki zabawa 'ya 'yanki uba ta hanyar Auren wanda ki ka yarda da addininsa da dabi'unsa harma da dangantakarsa.

4- Ki zama mai riko da addini a gidan mijinki.

5- kada ki zama mai kauracewa shimfidar mijinki.

6- Ki zama mai hakuri da halayyar mijinki.

7- Ki zama mai matukar biyayya ga mijinki.

8- Ki zama kwararriya wajen iya kwalliya kala-kala.

9- Ki zama kwararriya wajen iya girki kala-kala.

10- Ki zama kin iya barkwancin magana wajen baiwa mijinki dariya.

Post a Comment

0 Comments