ZAMAN AURE | KYAUTATAWA MATAYE GIDAN AURE:



✆ WhatsApp
☏+2348037538596
🌍www.sirrinrikemiji@gmail.com

kamar yadda bayani ya gabata cewa, Annabi (S.A.W) yayi wasiyya a rike mata hannu bibbiyu cikin tausasawa da mutuntawa , haka kuma a wadansu hadisan yayi nasihohi daban daban a inda ya gargadi magidanta a kan kula da hakkoki mata saboda rauninsu.

MANZO ALLAH {S.A.W} yana cewa.
Mafificinku shine wanda yafi kyakutatawa iyalinsa, ni kuwa duk na fi ku kyautatawa iyalin Duk abinda ake kira kyautatawa da nau'o insa ya shiga cikin wanna. Lallai ne mutum ya bawa iyalansa abinci mai dadi kuma wadatacce. Ba daidai bane mutum yaje waje/hotel yaci abincinsa mai kyau a gida kuma ya bar iyalinsa da karsa kafira mara dadi ko kuma ya bari iyalinsa da abinda shi da kansa ya san ba zai ishe su ba.
Haka kuma idan mutum yana da mata fiye da daya to dole ne ya zama mai adalci a tsakaninsu,Kada ya fitatawata da soyayya ta zahiri, ko kyauta, rana kwana, ko ya dinga nuna bambanci a tsakanin ya'yansu duk wanna bai halatta ba.
 Manzo Allah (s.a.w) yace duk mutumin da yake da mata biyu, sai ya fi karkata izuwa dayarsu, to zai tashi ranar kiyama da barin jikinsa a shanye".
Amma a wannan zamanin wasu mazaje sun mayar da matansu na aure kamar bayinsu.
 Komai suka yi na kuskure sai a hau su da fada, kai wadansu mazan ma har da zagi mijin da yake dukan matarsa kuwa aim ni ban ma dauke shi mai hankali ba. Tunda har ubangiji yace abin kunya ne ga mutum bayan ya sadu da mace kuma rabuwa tazo yace zai karbi wani abu da ya taba bata na dukiyar aure ko na kyauta.
 Inaso nayi amfani da wannan dama nayi kira da kakkausan harshe ga mazaje muji tsoron Allah na kiyaye amanar Allah a kan matan mu, domin manzon Allah (s.a.w) yana cewa dukkan ku masu kiwo ne kuma kowanne ku abin tambaya ne a kan abin kiwonsa.

           MATA ABOKA RAYUWAR MU NE:

Kowa yana da bukatar abokoyar rayuwa, haka su ma matan suna da bukatar mazan don su samu kariya da natsuwa a cikin rayuwarsu.

 Ubangiji (SWT) yana cewa. Yana daga cikin ayoyinsa, ya halici mataye daga gare ku, kuma ya sanya soyayya da tausayin juna a tsakaninku.

To wannan soyayya da jin tausayin juna sune sirrin zaman aure, ba wai don ba a samun sabani ba amma inda da soyayya to sai a dinga
Bahaushe ma yana cewa, so hana ganin laifi, kada ka manta lokacin da kake zuwa neman aurenta, yadda kake lallabata da zantuka dadada da kyautuka da salo iri iri na daukar hankali, har ka samu nasara ka rabo ta da iyayenta da sauran yan uwa da masoyanta, kuma shine yanzu zaka mayar da ita wulajantacciya mu ji tsoron Allah a gyara zamantakewar aure mu mazaje da mata domin ribar gobe kiyama.
▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓
        [SALON SOYAYYA] 

a yayin da masoya suke gudanar da soyayya a tsakaninsu, dole ne sai an dinga yin ta cikin kaffa-kaffa.

Nuna zumudi da matukar fito da maitar soyayya a fili, shi ke sanya gajiyawa ga dayan da ya zamo abokin tarayya a soyayya, don haka dole ne sai anyi ta cikin taku da nuna kulawa amma ba'a zake da yawa ba.

Masu iya magana suna cewa, "ido wa ka raina...? Amsar kuma itace, wanda nake gani kullum" ba a ce kar ki/ka dinga kula masoyayarka ba sai dai ana so kar ka cika nuna zakewa. 
Ko a wajen zuwa tadi/zance/hira, kar ya zamo ka nace har a gaji da kai.

Da yake yanzu zamani ne na amfani da social media ko waya hannu ,to ko ba ka je ba zaka iya aikawa da dan gajeran sako don masoyi/
masoyiya ta san kana tare da ita.

Don haka masoya su kula da wannan, domin yawan naci yakan haifar da matsala, nacin zuwa hira a kowanne lokaci nacin kiran waya, har ma da tura sakon text messeges a wasu lokutan wasu lokuta masoyi/masoyiya za taiya warewa don turawa masoyinta sakon nuna soyayya da kulawa haka nan wani lokaci masoyi zai ware wanda zai iya ziyartar masoyiyarsa domin zantawa, da gabatar da wasu batutuwa don kara dankon soyayya a tsakaninsu rashin kulawa kuma zai iya jawo wasu matsaloli su faru ga masoyan, amma dai an fi son kulawar ta zamo mai tsari, tsari mai kyau ta yadda masoyi/masoyiya ba zata gaji da masoyinta ba, ko kuma masoyi ya gajiya da masoyiyarsa ba
dole ne ya zamo an samu kyakkyawar mu'amala ta soyayya da kauna tare da amincewa juna ta hanyar da zata zamo mai tsafta kuma ya kasance ana dan bada gaf saboda yin nazarin abinda kanfi saurin farantawa masoyi ko masoyiya rai tare da samar da kyakkyawan nishadi mai armashi.

   SAKONNIN MASOYA:


➽ na tabbatar so yanayin sa yakan sauya daga farin launi zuwa kore.

➽ sonki yana cikin zuciyata, amma ina kokwanton kada ya zama tsuntsu ya tashi, idan har na ya kasance kin ci gaba da nuna rashin kulawarki a kaina.

➽ kyakkyawa mai kyan tsari,a duk lokacin da nake kallonki, tamkar kyakkywar fulawa mai furanni ma'abota debe kewa da sanya nishadi a zuciya ki kan zamo min.

➽ kiyi min agaji, ki tausaya min, ki tallafe ni, ki amince dani a cikin zuciyarki, sonki ya gama shiga jikina.

➽ kada ki bar ni shawagi tamkar tsuntsu a sararin SAMANIYA.

                 SONKI NAKE HAR ZUCI:
MAZA 




➽- kyauta ta musamman a gare ki, ke kadai, domin faranta ranki ya abar kaunata, baya ga kaina dana baki, ga kuma kyautar FUREN SO.

✦ abar alfaharina, ina sonki fiye da adadin lissafinki, adadin da zai iya zamowa tamkar zubar ruwan sama a lokacin damina.
Ke kadai ce tawa

✦ na zamo tamkar agwagwa, ina iyo a cikin kogin sonki.

Da za ki tallafa, da kin kawo karshen iyon da nake yi da ninkaya domin gudun gazawar gwiyawuna a lokacin da igiya ruwa ta nadeni.
Na kasance tamkar kifi a cikin ruwa, idan nayi gabas sai kuma na dawo nayi yamma,
idan nayi kudu, sai kuma na dawo nayi arewa.

                   MATA:

✥ dawainiya nake da sonka a cikin zuciyata, da sannu zaka fahimci ni masoyiyarka ce ta hakika, na zana zanen fulawar so a tafin hannuna nayi nufin nuna maka domin ka fahimci yanayin zancen da sonka yayi a cikin zuciyata.

✥ ina sonka tamkar yadda ba zan iya bayyana maka ba, ina sonka tamkar yadda baza ka iya kirga adadin ruwan sama ba kada ka zubar da hawayenka, yayin da wani ya bata maka rai, tuna da wacce kake so, ka ke kauna, sai zuciyarka tayi fari.

 ina sonka abin kaunata

na kasance a cikin masi kasa bacci yayin da dare ya tsala, bani da komai sai tunaninki, har wani lokacin gari kan waye ban iya runtsawa ba
nasan wannan yana faruwa ne saboda irin tsantsar soyayyar da nake miki.

Shin ko kema haka ne?

Tattausan lafazin ki abin kwatantawa.
Komai naki daban dana sauran 'yanmata
da zan kwana ina misalta kyawun halittarki, ba zan iya kaiwa karshe ba, koda kuwa zan wanzu ina yi har karshen rayuwata.

Hmm wanna harda matar aure ko mijin aure yana iya aiki text messege ne.

KU KASANCE TARE DA SIRRIN RIKE MIJI
YABO NA MUSAMMAN
GA DUKKAN MASOYAN DA SUKE RIKE ALKAWARIN JUNA TSAKANI DA ALLAH,
 BEGE
 KAUNA
 MASOYA
 MURMUSHIN
▇▇▇▇▇▇▇▇▇▇▇▇▇▇▇▇▇▇▇▇
     

Post a Comment

0 Comments