MU FARKA MATA


♜ ♜
☼✿╥▻MU FARKA MATA╥✿☼▻
▾▿▾▿▾▿▾▿▾▿▾▿▾▿▾▿▾▿▾▿▾▿▾▿▾▿▾▿▾▿▾▾▿▾▿
⁌⁍⁌⁍⁌⁍
⁌⁍⁌⁍
▻▻
✎ SIRRIN ❖RIKE ❖ MIJINKI ✎
❖❖❖❖❖❖❖❖❖❖❖❖
╦╦╦╥╦╦╦╦╦╦╦╦╦╦
╥╥╥╥HIRA DARE╥╥╥╥╥
◘◘◘◘◘◘◘◘◘◘◘◘◘◘◘◘◘
╥ ✆ +2348037538596
╥▻ WhatsApp
╥╥ ✑www.Sirrinrikemiji@gmail

Mu Lura da wannan 'yan'uwa na mata, Hira dare nasa mai-gida ya daina fita yawo da daddare, saboda baya samun hirar dare daga gareki, kuma Galibi idan suka fita, sai sun raba dare Ana tadi a waje, lokacin da zai dawo, ke kuma sannan kin yi barci, kinga irin wannan ina amfaninsa?

 Kin dinga jawo hankalin mai-gida ki, ta wannan sigar, domin ya kaucewa hanyar banza kamar ZINA ya debo cuta, shan giya da sauransu .

A kullum bayan sallah isha'i idan akaci abinci, sai a dasa Hira, har lokacin barci yayi, in ma mijinki baya so, to yau kullum idan ya ga ki na yawan damunsa da hirar.

To Zaki ga ya dawo yana so, muddin ki ka Saba masa da wannan, ba zai dinga fita yawo ba amma idan kika yi sakaci ya Saba da fita, to duk randa kika so ya Bari ba zai Bari ba.

[•MU FARKA MATA•]
+2348037538596
╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥
⊂( ̄ ̄)⊃••ABINCI••⊂( ̄ ̄)⊃
 BARIN MA MAI AIKI RAGAMAR ABINCIN MIJINKI DA GIDANKI
               ✧✦✧
Wannan babbar matsala ce, musamman ga matan masu kudi da kuma mata masu aikin gwamnati da matan sarauta 

Ma'ana anan shine sai kaga mace ta zauna ta mike kafa a gida ba zata tashi ta yima mijinta girki ba.

Koda kuwa yai tafiya ne ya dawo, sai dai ta sa mai aikinta 
    Wai ita Hutu !
MU FARKA MATA 

Duk mai wannan halin gara ma tun wuri ta daina, ko kuma ki sakar ma mai aiki ragamar gidanki, kama daga 

☆^ abinci 
^☆ kula da yara
^^☆ aikin gida 
Gyaran dakin ki Dana mijinki.

Ko kuma idan mai-gida yasa ki aiki, kice ma mai aikin ta tashi tayi!

Sai kace ita ya ajiye, ba ke ba, ya kasance idan ba wurin kwanciya ke babu wani abu da Zaki iya masa komai sai (HOUSE GIRL) wannan kuskure ne babba.

Muddin kika zauna , sai ta zauna miki domin kina da tashin hankali a gabanki , saboda ko mai aiki bata nuna tana son sa ba, shi zai iya nuna yana sonta, ko ya Fara tunanin Kara aure, don haka kar ki bada ragamar dawainiyar mijinki da me aiki, mu gyara wannan halin namu.
             ▻▻▻▻
╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥
✐KOWACE DA MATSALARTA ✎
Ma'ana :
Duk macen da take gidan miji babu wacce bata da matsala.

Amma kowa da irin Nata, don haka hakuri akeyi, ko ba miji ba, sai kin samu da uwar miji ko uban miji ko dangin mijinki.

Ko kishiya, ko yayyin miji, ko kannin miji, shi zama ya gaji Haka, zo mu zauna ,zo mu Saba, duk abinda ya sameki kiyi kokari ki magani matsalarki, ba tare da kowa ya Sani ba.

★ duk sabinin daya sameki tsakanin ki da mijinki, ki yi kokarin boyewa a gaban mutane, saboda gudun wani ya San halin da kuke ciki , kiyi kokarin sharewa, har Ku sulhunta ,saboda masu shigo wa gidanku.

★ KASHE AURE BA NAMU BANE.
 
☆ yaji ba namu bane balle idan kina da yara, kin ga kashe aure ba naki bane, duk abinda ya faru, muddin ki ka nemi Saki ❖

☆ idan da gayya yake miki, kin ga ya samu abin yi dama haka yake so, ga kuma ta samu, kin nema da kanki, amma idan kika share, kin kunsa masa bakin-ciki a daina kawo maganar Saki akan karamin abu.

'YAN-UWA MATA MUYI KOKARI MU SACE ZUCIYOYIN MAZAJENMU 

ta hanyar kyautata masu ta hanyoyi da dama, saboda mu zauna daram dam dam!

A zuciyar su komai aka miki, kiyi hakuri ki zauna, wata Rana sai labari.
┳┳┳┳┳┳┳┳┳┳┳┳┳┳
KADA KI ZAUNA A CIKIN DUHUN KAI 

ma'ana shine duk abinda kika San baki Sani ba.
 ⊂TA FANNIN ⊃

♡ KWALLIYA
♡ KULA DA HAKKIN MIJI 
♡ GIRKI TARAIRAYAR MIJI

to ki nemi mai koya miki a cikin sirrin ko kuma kina iya

Zuwa 
✿ Facebook 
Sirrin rike miji 

✿ WhatsApp
✿ gmail
✿ text message

Kan yadda Zaki kula da mijinki ki karanta ki koya 

Amma ba wai ki zauna cikin duhun Kai ba, kina cutar kanki ne 

Kuma wadannan abubuwan shi a wurin sa mai-gida ba zai taba cewa baki sabi ba, haushinki zai dinga ji, to tun ba azo rikici ba, kije ki koya, idan baki iya ba, saboda haka mu dinga Hulda da mutanen kwarai wadanda zasu wayar mana da Kai, domin idan mijinki dan gayu ne, muddin baki waye ba ta fannin aure da gayu, to fa komai ki ka yi, zai dinga hantararki, yana nuna miki tsana.

Kuma koda fita zai yi, idan kina da kishiya yar gayu ita zai dauka, ke kuwa cewa zai yi babu Inda za shi dake kina masa kauyanci da duhun Kai, 'yan uwa mu kula da wannan, kada mu zauna cikin duhun Kai .

╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥
KADAN DAGA CIKIN FALALAR JIMA'I 
﹏﹏﹏﹏﹏﹏﹏﹏﹏﹏﹏﹏﹏﹏
Zaki samu a duk lokacin da kika farantawa mijinki wajen kwanciya.

★★ ke ma zakiji dadin kwanciyar

☆☆ zai Kara miki so a zuciyar mijinki

★★ ga kuma kyautar da mijinki zai dinga miki, koda ba ki tambaye shi ba, tunda kina kyautata mai wajen shimfidarsa, dole shima ya kyauta ta miki.

☆☆kuma zai rage sabani tsakanin ki da mijinki.

Da sauran abubuwan wadanda masu yawa, Wanda ke zai amfana.

★★
┳┳┳┳┳┳┳┳┳┳┳┳┳┳
HANYAR NALLAKAR MIJI 
________________________________
akwai hanyoyin dama da ake amfani dasu wajen mallakar mai-gida kamar haka:

●♡♡ ki iya kissar kwanciya, da nuna masa kauna a wajen kwanciya

●♡♡ ki so shi, ki so 'ya'yan sa da yan uwansa gaba daya

●♡♡ Bari abinda bai so, da yin abinda yake so

●♡♡ ki kasance mai masa ladabi da biyayya da bin dokokin daya gindaya miki

●♡♡ tarairayarsa da tarba mai kyau a duk lokacin da ya shigo gida

●♡∀♡ tsaftar jiki iya girki, da kula da tarbiyyar yara

●♡∀♡ tausayinsa akan al'amuran da kuma idan yana cikin wani hali

●♡∀♡ son ibada, imani da kyautatawa ga danginsa

    \〇/TUNATARWA\〇/

Babu wani Wanda zai iya juyo miki da hankalin mijinki, da ya wuce ke, saboda haka muddin kika rike wadannan sai kin yi masa mallakar da ba macen da zata iya juya shi sai ke 

               ♡♡♡♡
□SHAWARA GA MATA MASU AIKI□

DON Allah 'yan'uwa mata mu dinga kokari muna kare mutuncinmu Dana mazajenmu a wurin. Da mike aiki, musamman masu aiki a (local government da state) saboda sai kaga matar aure ba ta da kawa a wurin aiki mace, duk abokanta maza ne!
To ko baki da aure, ai bai kamata a matsayinki na mace sai rauni, balle kina da aure
Ace kina abota da maza 

Idan kina wannan kullum mutuncinki raguwa zai yi ba karuwa ba, kuma sai Allah ya kamaki ko kuma ya Kama mijinki ranar gobe kiyama, kin ja masa kenan, tunda shi daya bar ki zuwa aiki, bai yi tunanin haka Zaki yi ba.

Mu dinga kulawa da irin wannan, saboda sai kaga mace cikin kankanin lokacin tana abokai maza da yawa kuma ko ba kya fasikanci wannan fuskar da kika bayar , shi zai sa kare da biri kowa ya nemeki da fasikanci

Saboda kin Saki kanki kin zama kamar haja a KASUWANCI,ki zauna kina Hira da su barkatai, ki na sakin zance da bai dace ba har Tafi da shewa..
┳┳┳┳┳┳┳┳┳┳┳┳┳┳
      ♡SIRRIN NA DAYA ¹♡

amfanin ganyen magarya a jikin mace :

Kadan daga ciki, shine, yana kariyar sirrin haka kuma yana maganin sammu da shafar aljanu.

Musamman idan aka hada da ayoyin alkur'an
→ ayatul-kursiyyu
→ kula'uzai
Da sauran ayoyin alkur'an wadanda suka sawwaka.

Wani Karin amfanin kuma: yana kauda karni a jikin mace a yayin jinin biki, ko na haila yana maganin warin kashi.

Yana magani (INFECTION) yana warke dattin cikin jiki dama waje.

Haka kuma yana Kara ma mace lafiya

HQ an fi son Ayi amfani da shi danyensa.
Sai dai sai in ba a samu danyen ba.

Za a iya amfani da busasshe za a murmushe shine, a sa shi cikin ruwa yayi taushi sai a mutseke shi har yayi kumfa kamar sabulun.

Sai ki dinga wanke HQ da shi, Zaki ga har yana wani yauki yana matukar wanke datti sosai bincike ya nuna babu abinda ke kawar da datti kamarsa da wanke warin gaba da daudar ciki.

╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥╥
      ♡♡SIRRIN NA BIYU♡♡
        ・KARIN NI'IMA・
ki sami 
Kankana 
Gwanda 
Citta 
Abarba 
Lemon tsami 

Habawa ke dai jaraba ki gani 
________________________________
        ⊙SIRRIN NA UKU⊙
ki samu 

Kankana 
Ki murjeta, bayan kin yanyanka sai kitsame kwallayen, ki kawo ruwan 
Kanunfari ki tsiyaya, ki kawo (peak milk) ki juye inki na bukata ki sanya a farji ya danyi sanyi ki wuni kina sha.
Zaki ba wata labari !
________________________________
      SIRRIN NA HUDU
Karin ni'ima
Ki samu
 danyen zogale 
Mazarkwaila
Peak milk

Ki gyara shi, sannan ki wanke shi tsf! 
Sai ki Dora a wuta ki dafa shi ya dahu, sannan ki tsiyaye ruwan, sai ki samu mazarkwaila ki jefa kamar rabi ki kuma samu kanunfari ki jika,sai ki tsiyaye ruwan, ki sa zuma da (peak milk) dai-dai yadda kikeso, amma fa me kyau sai ki sa a cikin frij

Sai ki dawo kan zogelenki ki gyara shi ki zuba (acontainer) ki samu farar albasa, ki yanyanka sannan ki hada da gadali guda

Ki daka kanunfari dai-dai ki zuba, ki kuma sami tumatir masu kyau kamar guda biyu ki yankasu, ki kuma sami kwai kamar guda biyar ki kada ki sa magi ki sa.

In so samu ne, ki soya su da man zaitun ki sami cucumber ki yanyanka bayan kin juye shi daga wuta sai ki juye cucumber a ciki.

Bayan duk kin hadasu wurin daya sai ki dauko wannan hadin da kika sa a farji ki zauna ki cinye wannan kwadon kada ki .
________________________________
       SIRRIN NA BIYAR

ki sami 
Kwakwa 
Kankana 
Sai ki markadesu kisamu zuma kadan ki sa a ciki, sannan kisa a firji ya yi sanyi shi ma sirrin ne na Kara ni'imar mace 

________________________________
       SIRRIN NA SHIDA
ki samu lemon tsami, ki rikka wanke hammatarki tas! Yana wanke hammata da ka'ida warinsa.

________________________________
      SIRRIN NA BAKWAI
ki sami ganyen zogale, da ganyen magarya, ki shanyasu a inuwa, ko ki ajiye a daki har su bushe sai ki dauko idan su bushe sai ki zuba a cikin zuma, ki dinga lasarsa duk bayan la'asar Zaki yaba sosai ki gwada 

________________________________
         SIRRIN NA TAKWAS

ki sami dabino manya masu kyau, ki baresu don cire masu tsutsa, sai ki kika ya kwana sai ki sa a balanda ki markade shi, sai ki zuba madara ta ruwa, ki shanye shi ma Karin ni'imar yake sosai 

________________________________
       SIRRIN NA TARA 

ki sami dabinonki masu kyau da kwakwa ki dinga hadasu lokacin guda ki na taune su wannan hadin shima yana da matukar muhimmanci Zaki yana da shi Uwargida.
________________________________
       SIRRIN NA GOMA
ki sami 
Man zaitun
Farin almiski
Cee-cee cream

Sai ki sami waje mai kyau ki hadesu ki juyasu ki dinga matsi da shi.

________________________________
             KARIN BAYANI 

wani Karin bayani da Zan yi anan shine 'yan uwana mata muyi da gaske mu kame mazajenmu daga shiga gurbacewar rayuwa 

Kuma duk wata mai matsala a gidan ma'aurata da ta samu wannan post na SIRRIN RIKE MIJI to insha Allah zata samu hanyar warware matsalarta.

Saboda haka yasa kuka ga duk wani abu mai bata zamantakewar aure da kuma mai gyara shi 
❖❖❖❖❖❖❖❖❖❖❖❖

Post a Comment

0 Comments