Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: ☏+2348037538596
Kayan Hadi.
Man zaitun
Lallae
Kurkur
Madarar ruwa
Zaki hade wannan kayan guri daya sai ki kwaba ki shafe jikin ki da fuskarki Idan ya bushe sai ki murje sannan ki yi wanka.
🏵️SABULUN KURAJE🏵️
🏵️ asef soap
🏵️ pharmaderlm soap
🏵️ kanwa
🏵️ jar dilka
🏵️ Zuma
🏵️ lemon tsami
Ki goga sabulun kowanne guda uku, sannan ki zuba kanwarki dakakkiya cikin karamin cokali, kinkwaba dilka da ruwan zafi cikin cokali cin abinci daya ki zuba a ciki, ki matse lemon tsami daya a Kai kisa Zuma cokali biyar ki hada ki kwaba sosai, ki lailaya sai ki dinga shafawa a fuskarki kamar ya rage minti biyar kafin ki shiga wanka, Indan kin shiga wanka sai ki kuma wanke fuskarki da sabulun kamar uku ko Dama da haka.
.
🏵️SABULUN WANKA NA BAKAR MACE🏵️
🏵️ sabulun salo ko sabulun Ghana
🏵️ magiji.
🏵️ Zuma
🏵️ lemun tsami.
🏵️ zaitun
a hada sabulun Ghana da magiji a dake a zuba Zuma a matsa lemun tsami kadan a saka man zaitun cokali daya a bada a kwaba, bakar mace da bata son tayi fari sai ta dinga wanka da shi, zai sa tayi kyau.
🏵️🏵️🏵️🏵️🏵️🏵️🏵️🏵️🏵️🏵️🏵️🏵️🏵️🏵️🏵️🏵️
HANYOYI GOMA (10) WANDA GYARAN JIKI
CIKIN SQUKI:
♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣♣
1⃣- Idan ana so a gyara gashi za a iya hada ayaba da kwai sai a kwaba su sosai sannan a shafa a gashi a jira na tsawon mintuna sha biyar (15) zuwa talatin (30) sannan a wanke.
2⃣- Domin gyara farce, za a iya tsoma hannu a cikin man zaitun na tsawon mintuna biyar (5) sannan sai a cire a kullum. Farce zai yi matukar kyau sosai.
3⃣- Ana amfani da zuma mai kyau domin samun fuska mai santsi da laushi. Ana shafawa a fuska a jira na tsawon mintuna goma sha biyar (15) zuwa ashirin (20) sannan a wanke da ruwan dumi. A gwada wannan hadin sau daya ma a sati za a ga canji.
4⃣- Ana amfani da ruwan amfuna da ruwa ana wanke kai. Yin hakan na cire dattin da ke makale a gefen gashin kai.
5⃣- Domin masu yawan shafe-shafe za su iya yanka lemon tsami biyu sai su rika shafawa a inda ya yi duhu. Yin hakan a kullum na haskaka bakin da ya bayyana a wasu gabbai ko sassan fata.
5⃣- Domin samun fatar jiki mai sulbi, za a iya amfani da man zaitun da gishirin rafi a kwaba sai a rika dirzawa a fatar jiki a kalla sau uku a sati.
6⃣- Man kwa-kwa na matukar gyaran zubewar gashin ka. Za a iya shafa man kwa-kwa a fatar ka, sannan a shafa a jikin gashin. A bari ya jima kamar na awa daya sannan a wanke.
7⃣- Maza masu son man gyaran gemu, za su iya amfani da man kwa-kwa.
8⃣- A samu lemon tsami sannan a zuba zuma a kai. Sannan a rika shafawa a kan kurajen fuska. Yin hakan na kashe su sosai.
9⃣- Man zaitun na sanya santsin fata idan an kasance ana yawaita shafa shi a koda yaushe a matsayin man fata.
0 Comments