DOMIN GYARAN JIKI(GYARA DA KANKI):




Wanan hadin nayi shine dan amfanin Ku mata,Kanne, yayye da dukkan masu bukata.

ABUBUWA N DA ZAA HADA

Cikwi- fai fai daya
Aya-cup daya
Gyada-cup daya
Mazarkwaila-rabin fai fai
Dabino-gwangwani daya
Ridi -rabin-cup

YADDA ZAKI HADA 

Cikwi, yana zuwa a fai fai,da manya da kanana, idan manya ne rabin fai fai ya isheki, idan karami ne sai ki samu fai fai daya, kuma wani lokacin ba bausashe bane, dan haka idan kin siya zaki babballa shi ki busar ya bushe sosai.

Aya, zaki wanke ki rege dan fitar da dukkan datti da tsakuwa, sai ki baza ta bushe sosai.

Gyada zaki sayi cup 1(wato gwangwani daya) ki tsince ki fitar da datti, sai ki zuba a frying pan ki kunna wuta, ita kadai babu mai babu ruwa, zaki ringa juyawa, sai ki sauke ki saka hannayenki ki murtsuka zaki ga brown bayan sun fita tas, kuma hakan zaisa ta bushe.

Mazarkwaila, itama a fai fai take zuwa, ana yinta daga rake kai tsaye,sai ki samu rabin fai fai ki ajiye.

Dabino, zaki samu cup daya(gwangwani daya), idan ba busashe bane to sai ki bare shi ki fitar da kwallon ki shanya ya bushe.

Ridi, zaki samu ridi(Soyayye) rabin cup (rabin gwangwani).

Zaki hada dukka kayan dana lissafo ki dake su tas, su zama gari. Amma wasu daga ciki daban daban zaki dake ba ina nufin ki hade su waje daya ki dake ba, sai ki hade garin gaba daya ki samu container mai murfi ki rufe, idan kin tashi amfani sai ki bude ki diba, bazai lalace miki ba har tsawon watanni 2,idan har komai busashe ne babu danshi.

Kayan hadi-Zaki samu madarar ruwa ko yoghurt/nono mara tsami dasu zaki ringa hadawa kina sha.

Zaki diban garin da kika hada, ki zuba masa madara/yoghurt ki ringa sha tsawon kwana 5-7 zaki sha mamaki.

Amfanin wanan hadi dan gyaran jiki na Amarya da Uwar gida, dan kauda duk wata matsalar bushewa da rashin ingantacciyar lafiya a jikin mace.


Post a Comment

0 Comments