𝐘𝐀𝐃𝐃𝐀 𝐘𝐀 𝐊𝐀𝐌𝐀𝐓𝐀 𝐌𝐀𝐒𝐔 𝐂𝐈𝐖𝐎𝐍 𝐒𝐔𝐆𝐀𝐑 (𝐃𝐈𝐀𝐁𝐄𝐓𝐄𝐒) 𝐒𝐔 𝐓𝐔𝐍𝐊𝐀𝐑𝐈 𝐀𝐙𝐔𝐌𝐈



🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

Ciwon suga yana daga cuttukan da masu shi zasu iya shan azumi duba da hatsarurrukansa sannan ciwo ne da zuwa yanzu bashi da magani. 

Muna da musulmai sama da milyan 70 masu cutar da sunkai munzalin azumi a shari'ance. Toh amma kao tsaye baza ace kwatakwata don mutum nada ciwon sugar saide ya ciyar ba.

Abunda yasa kuwa shine: domin akwai relapse da koda ba ajera ba insha Allahu cikin watanni 11 kafin wani ramadan ya juyo mutum zai iya ramawa koda ta hanyar jefi jefi ne basai ajere ba.

Toh saide in ciwon yakai ga yin illar da ya lalata Ķoda, zuciya, idanu ko magudanan jini, koma watakil mutum anakai ga anfara masa wankin koda, ko kuwa akwance yake kasidin toh wannan ya halasta ya aje azumi saide a ciyar masa.

𝐀 𝐈𝐑𝐈𝐍 𝐖𝐀𝐍𝐍𝐀𝐍 𝐋𝐎𝐊𝐀𝐂𝐈𝐍 𝐍𝐀 𝐀𝐙𝐔𝐌𝐈 𝐆𝐀𝐌𝐄 𝐃𝐈𝐀𝐁𝐄𝐓𝐄𝐒

Nasan masu larurar zasu fara tunanin taya ya kamata su bullowa larurar musamman ganin kullum cikin shan magani suke, wasu kuma kullum cikin allura suke. Kadan din ma da iya abinci ke control din sugar tasu idan akace azumi ne suna shan wahala domin kone fuel din yai yawa...

Kamar yadda nasha fada ko nake jan hankali dukkan mai ciwon suga wajibi ne ace yana da likitan da yake gani, ko kuwa dama yasan yana da likitansa da yake ganin. Don haka matakin farko dukkan mai wannan larurar ya dace daga nan kafin ashiga azumin yaje follow up ya sami likitansa ya tattauna dashi, ko kuma koda ta waya ne, inma wani gwaji zakai toh ya fadama tunda akwai gwajin da yana iya bayanin mizanin sugar ajininka tun daga watanni 3 baya zuwa yau hakan zaisa yagane maida hankalin ga magani tare da kiyayewarka ga larurar... domin shine yasan irin nasarorin da yake gani.

Saboda ciwon sugar ba karya! Inde likita yace ka kiyaye tohfa inma ka koma kaqi kiyayewa dole zai gane, Ba'a wa likita karyarta ba irin sauran cuttuka bane. @𝑰𝒃𝒓𝒂𝒉𝒊𝒎 𝒚. 𝒊𝒃𝒓𝒂𝒉𝒊𝒎

𝐊𝐄𝐍𝐀𝐍 𝐋𝐈𝐊𝐈𝐓𝐀𝐍 𝐃𝐀 𝐊𝐎𝐖𝐀𝐍𝐍𝐄 𝐌𝐀𝐈 𝐖𝐀𝐍𝐍𝐀𝐍 𝐂𝐔𝐓𝐀𝐑 𝐊𝐄𝐆𝐀𝐍𝐈 𝐍𝐄 𝐊𝐄𝐃𝐀 𝐃𝐀𝐌𝐀𝐑 𝐁𝐀𝐒𝐀 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐖𝐀𝐑 𝐀𝐙𝐔𝐌𝐈 𝐊𝐀𝐃𝐀𝐈???

Kwari kuwa; Ai shyasa don kurum kana likita bai wadatar ba wajibi ne sai kasan addini da tarin hukunce-hukuncensa ta wata fuskar domin akwai inda malamin addini ma dakai ya dogara kafin yai hukunci. Don haka kuma dole ya zamto ka karantu kasan me kake inba haka ba ka rika tafka 6arna kana bada bayani ba daidai ba Allah zai kama mutum da kyau-da-kyau 

Don haka Likitan kowanne mai wannan larurar shike da alhakin tsaramasa ko kuwa basa damar yai azumi ko sa6anin haka. 

Domin akwai masu wuyar sha'ani cikin marasa lafiya, wasu korafi kurum suka iya da zagin likita amma sunsan suna da ciwon kuma anja musu kunne amma sam ganin basa jin wani canji ajika basa ta6a damuwa da shan magani ko kiyaye umarnin likita har sai ta 6aci. Domin ciwon suga inbakana da damuwa da lafiya ba saika shekara 5 dashi bakasani ba domin bai zama dole kaji canji ba shyasa sanda zaka fara jin alamomin ciwon sannan ka makaro. 

Don haka wasu kuma suna shan maganin amma basa kiyaye abinci kurum saboda ganin suna shan magani wanda wannan ma kuskure ne mai girma.

𝐖𝐀𝐍𝐍𝐀𝐍 𝐂𝐄 𝐓𝐀𝐒𝐀

Ko yaushe nake jan hankali akan mutane mugane ciwon suga ba wasa bane: duk wanda yai wasa wallahi zaiga bakin ciki domin zaikai ka ga makancewa, bugun zuciya, ciwon koda, ciwon jijiyoyin jiki da kafafu, ciwon hanta, koma akarshe akai ga yanke ma wani sashi na jikinka, dole kurum mutum ya yadda yana da matsala ya kiyaye abunda ake fadamasa.

Wannan tasa wanda ke shan magani kuma yake kiyaye abinci da abun sha shike da chance din iya azumi lafiya kuma complete. Kuma bai cikin hatsarin ciwon da ikon Allah, akwai inda inyakai saboda compliance dinsa ana iya saukesa ma daga kan magani yaci gaba da kiyaye abinci kurum. 

𝐖𝐀𝐍𝐈 𝐙𝐀𝐈𝐂𝐄 𝐓𝐎 𝐀𝐈 𝐓𝐔𝐍𝐃𝐀 𝐀𝐙𝐔𝐌𝐈 𝐁𝐀 𝐂𝐈𝐍 𝐀𝐁𝐈𝐍𝐂𝐈 𝐀𝐊𝐄 𝐁𝐀 𝐓𝐀𝐘𝐀 𝐂𝐈𝐖𝐎𝐍 𝐙𝐀𝐈 𝐙𝐀𝐌𝐀 𝐀𝐁𝐔𝐍 𝐃𝐀𝐌𝐔𝐖𝐀 ???

𝐒𝐢𝐧𝐚𝐝𝐚𝐫𝐢𝐧 𝐢𝐧𝐬𝐮𝐥𝐢𝐧: Shine sinadarin da wata halitta acikin cikin mutum da ake kira 𝐩𝐚𝐧𝐜𝐫𝐞𝐚𝐬 ke samarwa domin wannan insulin din ya saisaita sikari acikin jinin mutum, saboda idan sikari yai yawa to zai cutar da jikin ya haddasa masa sauran matsaloli ajika. Toh amma kada kaji ance sikari ko sugar ka dauka ana nufin sikarin da mutum kesha ta baki ake nufi. 𝑨'𝒂 𝑬𝒉 𝒔𝒖𝒈𝒂𝒓 𝒄𝒆 𝒎𝒆 𝒛𝒂𝒌𝒊 𝒌𝒘𝒂𝒓𝒂𝒊 amma ba daga sikari ko abu me zakin da akasha bane kurum.

Kamar yadda nasha fada akwai nau'ikan abincin da ba masu zaki bane ma amma in munci sunje ciki karshe suna rikidewane su zama sugar, sikari ko glucose aturance domin bamu kuzari. Kai hatta kitse ko ince maiko shima inyai yawa ajika sugar yake zama. 

Irin wadannan rukunin abinci masu zama sugar su ake kira 𝐜𝐚𝐫𝐛𝐨𝐡𝐲𝐝𝐫𝐚𝐭𝐞𝐬 wato irinsu: Shinkafa, masara, tuwo, indomie, flour, taliya, macaroni, wainar fulawa, cincin, doya, dankali, roogo, taliya, fanke, duk inkaci kaci sugar Basai shan zaqi irinsu tea, soft drinks.. lemon kwalabe da robobi, maltina, da sauransu ba.

Sannan ita waccan 𝐏𝐚𝐧𝐜𝐫𝐞𝐚𝐬 din de ha'ila yau tana da wani sinadarin da take saki me suna 𝐆𝐋𝐔𝐂𝐀𝐆𝐎𝐍 wanda daga sunansa zaku iya jin yai kama da Glucose wato sugar.... Eh hakan ne domin ayayin da Pancrease ke sakin insulin domin ya rage yawan sugar cikin jini, Shi kuma 𝐆𝐥𝐮𝐜𝐚𝐠𝐨𝐧 tana sakinsa ne domin ya kara yawan sugar din acikin jini ayayin da mutum yake cikin yumwa. @𝑰𝒃𝒓𝒂𝒉𝒊𝒎 𝒚. 𝒊𝒃𝒓𝒂𝒉𝒊𝒎

𝐓𝐔𝐍𝐃𝐀 𝐊𝐔𝐍𝐉𝐈 𝐒𝐔𝐍𝐀𝐍 𝐒𝐈𝐍𝐀𝐃𝐀𝐑𝐀𝐍 𝐆𝐀 𝐘𝐀𝐃𝐃𝐀 𝐀𝐁𝐔𝐍 𝐊𝐄 𝐅𝐀𝐑𝐔𝐖𝐀

Toh a sakamakon haka tunda ita PANCREAS din tafi sakin wancan sinadarin nata na INSULIN ayayin da mutum ke cin wani abu, 𝐀𝐦𝐦𝐚 𝐚 𝐥𝐨𝐤𝐚𝐜𝐢𝐧 𝐚𝐳𝐮𝐦𝐢 𝐬𝐚𝐛𝐨𝐝𝐚 𝐛𝐚'𝐚 𝐜𝐢𝐧 𝐤𝐨𝐦𝐢 toh jikin mutum zaike kaiwa kwakwalwa sako cewa akwaifa yunwa tunda shi baisan azumi kake ba cewa kana sane kaqin cin abinci saboda ibada don haka akokarin PANCREAS na taimakonka don kaci gaba da samun kuzari karka cutu saita fara SAKIN wancan Glucagon din nata domin sugar ta karu ta baka kuzari wanda akarshe yakan taru yai yawan da yafi karfin jikinka ya amfana dashi saboda ta saki Glucagon din da yawa gashi kuma kana da larurar kasa sarrafa SUGAR ajika dama.

Saboda shi ciwon sugar rashi ko karancin INSULIN ke kawosa wato jikinka bai iya rage yawan sugar shyasa maganin da kake sha kullum ko allurar da akema kullum sunanta INSULIN dinma don taima aikin saita suga tunda insulin din jikinka bata wadatar da bukatar jikin don haka arashin insulin da kuma rashin maganin da bakasha saboda azumi har sai ansha ruwa hakan ka iya sa me ciwon sugar ya hadu da abunda ake kira 𝐇𝐘𝐏𝐄𝐑𝐆𝐋𝐘𝐂𝐄𝐌𝐈𝐀 wato sugar tai yawa acikin jini level din da tana iya haddasa illa amma gashi ba damar rageta duk da gashi mutum baicin komi amma sugar tai over ajikinsa dalilin GLUCAGON da aka sakar masa da niyyar taimakonsa.

Wanda samuwar hyperglycemia hakan ke haddasa: 
■Matsanancin kishirwa, 
■Ciwon kai, 
■Kasa nutsuwa, 
■Ganin hazo-hazo, 
■Yawan fitsari,
■ Kasala; domin in glucose ta wuce kima bazata bada kuzarin ba saita koma sanya kasala
■Matsi ga jijiyoyin jini, illata koda, kasala da sauransu)... 

𝐀 𝐝𝐚𝐲𝐚 𝐛𝐚𝐧𝐠𝐚𝐫𝐞𝐧 𝐤𝐮𝐦𝐚:

Wani abu shine bayan GLUCOSE din tai 𝐇𝐈𝐆𝐇 𝐭𝐚𝐢 𝐡𝐢𝐠𝐡 idan taje TOP inda daga nan bazata kuma iya karuwa ba to kuma wani iko na ubangiji sakamakon bakaci komi ba itama sai ta rasa kuzarin cigaba da hauhawan don haka 𝐬𝐚𝐢 𝐢𝐭𝐚𝐦𝐚 𝐭𝐚 𝐫𝐢𝐤𝐢𝐭𝐨 𝐤𝐚𝐬𝐚 𝐤𝐮𝐫𝐮𝐦 wanda inta rikito dan INSULIN din da ya zamo pancreas na saki duk da karancinsa sai fadowar tasa ya danne glucagon wanda hakan kesa mutum ya sami abunda ake kira 𝐇𝐘𝐏𝐎𝐆𝐋𝐘𝐂𝐄𝐌𝐈𝐀 wato suga tai kasa har tai karancin da bazata ishi jiki ba wanda illar da hakan ke haifarwa tafi ta HYPERGLYCEMIA din domin mutum na iya haduwa da:

■ Faduwa ya rika jijjiga kamar me farfadiya wato seizure, 
■ Mutum na iya fita daga hayyacinsa hankalins ya gushe, ■ Mutum na iya haduwa da larurar kwakwalwa, 
■ Daukewar gani, 
■ Bugawar zuciya aguje aguje farfar, 
■ Tashin zuciya, 
■ Saukar jini
■ Karshe ma mutum na iya mutuwa

Toh kunga kenan da HYPER da kuma HYPO Gycemia din da mai ciwon sugar me azumi ka iya fuskanta dukkansu abun tsorone. Abun kuma a kauce musu ne, shyasa dole likitanka yafi kowa saninka, domin ba duk masu ciwon sugar ne suke iya fahimtar illa da suke ciki ba da mahimmancin bin ka'idoji. @𝑰𝒃𝒓𝒂𝒉𝒊𝒎 𝒚. 𝒊𝒃𝒓𝒂𝒉𝒊𝒎

𝐓𝐎 𝐊𝐔𝐌𝐀 𝐀 𝐒𝐀𝐍𝐃𝐀 𝐆𝐋𝐔𝐂𝐎𝐒𝐄 𝐓𝐀𝐈 𝐇𝐈𝐆𝐇 𝐈𝐍𝐃𝐀 𝐁𝐀𝐓𝐀 𝐑𝐈𝐊𝐈𝐓𝐎 𝐁𝐀 𝐌𝐄 𝐙𝐀𝐈 𝐅𝐀𝐑𝐔 ???

Idan ace bayan da glucose taje Top mutum baida insulin ko kadan dazai iya rikito da ita musamman a masu type 1 diabetes wanda da allura suka dogara tunda magani ma baya musu toh mutum na iya haduwa ne da abunda ake cewa DIABETIC KETOACIDOSIS wanda zai fuskanci alamomin da suka hada da:
■ Tsananin jin kishirwa
■ Yawan fitsari
■ Lalacewar koda
■ Daukewar gani zuwa duhu
■ Tashin zuciya tare da amai
■ Ciwon ciki
■ Numfashi ya rika wari
■ Gushewar tunani
■ Tare da Sumewa

𝐖𝐀𝐍𝐍𝐀𝐍 𝐓𝐀𝐒𝐀 𝐊𝐀𝐌𝐀𝐑 𝐘𝐀𝐃𝐃𝐀 𝐍𝐀 𝐅𝐀𝐃𝐀 𝐀 𝐁𝐀𝐘𝐀

Kaucewa afkuwar kowanne daga cikin wadancan matsaloli ya rataya ga cigaban da mutum ya nuna... idan har yana shan magani yana bibiyar sugar dinsa ta hanyar mallaka abun gwaji yana dubawa akai akai toh yana da chance mafi girma na haduwa complication din ciwon.

Shiyasa duk me ciwon sugar mukan shawarcesu da su mallaki abar da muke kira GLUCOMETER domin su rika duba mizanin sugar acikin jininsu akai akai domin sanin measurements dinsu musamman sau 2 ko 3 ayini.

Kamar yadda nasha fada asauran posts dina wannan cuta rukuni rukuni ce, wasu magani suke sha, wasu kuma allura wasu kuma duk suna allura suna kuma shan magani, wasu kuma saboda antari ciwon da wuri anganosa takai ga kiyaye abinci kadai ma yasa ta dena hawa.

𝐒𝐀𝐈𝐃𝐄 𝐆𝐀 𝐖𝐀𝐃𝐀𝐍𝐃𝐀 𝐊𝐀𝐈 𝐓𝐒𝐀𝐘𝐄 𝐊𝐀𝐃𝐀 𝐒𝐔 𝐊𝐔𝐒𝐊𝐔𝐑𝐀 𝐒𝐔 𝐇𝐀𝐈𝐊𝐄𝐖𝐀 𝐀𝐙𝐔𝐌𝐈

1. Mace mai ciwon sugar wacce take da juna biyu

2. Me ciwon suga rukuni na daya wato Type 1 wanda kuma yasan baya kiyaye magani sam tun farko

3. Wanda sugar din is poorly controlled gwaji ya nuna ta wuce >250mg/dl

4. Wanda yasan baya bin umarnin likitoci abunda ransa yaiwa dadi kurum yake bi

5. Wanda yasan yana da ciwon suga hade da wasu cuttukan kamarsu; Hawan jini kuma baya sha masa magani ko me ciwon suga da ciwon zuciya, ko me ciwon sugar da ciwon k'oda ahade. Kuje kuga likitanku.

Wadannan rukunin mutane 5 din ina jan kunnensu sosai. 
@𝑰𝒃𝒓𝒂𝒉𝒊𝒎 𝒚. 𝒊𝒃𝒓𝒂𝒉𝒊𝒎

𝐆𝐀 𝐊𝐔𝐌𝐀 𝐀𝐁𝐔𝐁𝐔𝐖𝐀𝐍 𝐃𝐀 𝐈𝐍 𝐀𝐍𝐆𝐀𝐍𝐈 𝐓𝐎𝐇 𝐊𝐎 𝐀𝐍 𝐃𝐀𝐔𝐊𝐀 𝐘𝐀 𝐊𝐀𝐌𝐀𝐓𝐀 𝐀 𝐀𝐉𝐈𝐘𝐄 𝐀𝐙𝐔𝐌𝐈𝐍

■ Idan mutum ya duba glucose dinsa da GLUCOMETER yaga ta nuna kasa da <60mg/dl (3.3mmol) koda anyi azahar ina shawartar mutum ya gaggauta aje azumin nan ya sami wani abun yaci inba haka ba inya fadi zai hadu da alamomin can na HYPOGLYCEMIA na sama.

■ Idan mutum ya duba glucose dinsa yaga ta nuna kasa da < 70mg/dl tun a farko farkon awoyin tashi da azumi wato kamar wajen karfe 10 na safe zuwa karfe 1 na rana inyaga haka ya kamata ya aje azumi

■ Wanda bayan yin sahur ya tashi da azumi ko kuma bayan yakai azumin lafiya amma yaga glucose dinsa ta kai >300mg/dl daidai da (16.7mmol) lallai mutum ya gaggauta aje azumin in bayan sahur ne... sannan in kuma bayan yakai ne yaga haka toh kada ya kuma jaraba daukar azumi akashe gari akalla sai bayan kwana uku zuwa 6 in abun ya saitu.

𝐒𝐀𝐈 𝐒𝐇𝐀𝐖𝐀𝐑𝐖𝐀𝐑𝐈𝐍 𝐃𝐀 𝐙𝐀𝐍 𝐊𝐀𝐑𝐀 𝐌𝐔𝐊𝐔 𝐃𝐀𝐒𝐔 𝐀𝐊𝐀𝐑𝐒𝐇𝐄

1- Ina shawartar duk mai ciwon suga da ya mallaki GLUCOMETER hade da strip din, wanda kuma yake dasu ita toh ko yaushe ya sanya ido akan glucose dinsa sanya tashi da zumi akalla ya suba sau biyu zuwa 3 ayini kafin akai azumi. Awa biyu bayan sahur, can wajen 12 na rana, da kuma wajen la'asar.

2- Wanda ke shan magani safe da yamma, sai ya koma sha lokacin sahur da kuma lokacin buda baki musamman masu amfani da magunguna irinsu METFORMIN, GLITAZONE, RAPAGLINIDE wadannan basu cika haduwa da matsala ba matukar sugar dinsu sunyi control dinta da kyau dama. 𝑰𝒃𝒓𝒂𝒉𝒊𝒎 𝒚. 𝒊𝒃𝒓𝒂𝒉𝒊𝒎

3- Masu allurar insulin wadannan ma inde sugar dinku is well controlled shikenan kwa iya dauka amma kusa ido akan sugar din domin allurar malamai sun tafi akan tana karya azumi domin nutritional ce duk da in anbarta rayuwa na iya shiga wani hali, Amma de asa ido ana ganin sugar tai sama tohfa a aje azumin. Saide kamar yadda nace kui kokari kuga likitanku domin tantancewa.

4- Ku rika sahur da abinci mai gina jiki wato protein bame sanya kuzari ba carbohydrates saboda carbs kwai nauyi zaike sa sugar tai sama tare da saurin jin yunwa... (Gara kui amafani da Brown rice in ma shinkafar ce, biredin alkama, Kosai, Awara, abincin Alkama, Oat meal, wake, kifi, Alala, Nama) da sauransu. Ku guji (farar shinkafa, taliya, bread flour, indomie, doya,) da sauransu.

5. Masu shan taba cikin masu wannan ciwon kui hakuri ku dena kwata kwata ku barta har abada, kuje kuga likitocin halayya psychiatricins suna da taimakon da zasu iya baku.

6- Banda sahur da shinkafa, Indomie, Dankalin hausa, ko taliya... saboda da safe insulin baida power sosai. Don haka inma dole sai kunci to ka dunkule hannunka 👊🏻 kada kaci shinkafa ko taliya wacce tafi yawan girman dunkulallen hannunka, sanna kai mixed dinta da ganyayyeki su kabeji, lettuse duk inda hali, su cucumber hakan zai hanaka fama da yunwa insha Allah.

Masu karatu sannunku da kokari... bayanin yai tsayi nasani, toh amma ta hakane zan isar da sakon a dunkule kowa ya fahimta. Ina fatan zaku taimakeni wajen fadakarwa tare da ilmantar da sauran masu larurar da kuka sani domin taimaka musu.

Allah kasa muyi azumi lafiya amin.

[𝐈𝐛𝐫𝐚𝐡𝐢𝐦 𝐘. 𝐘𝐮𝐬𝐮𝐟]

Post a Comment

0 Comments