.:
Da farko dai ya kamata ma’aurata su san cewa akwai abubuwa da dama da kan iya shafar lafiyar zamantakewa a bangaren samun haihuwa.
Wadannan abubuwa sun hada da shekarun ma’auratan da lafiyarsu da kuma ilminsu. Miji da mata, kowanne zai iya zama shi ne sanadin rashin haihuwa, ba mace kadai ba kamar yadda aka fi alakantawa a al’adance.
A bangaren shekaru, macen da ba ta wuce shekaru 25 ba ta fi saurin samun iri, fiye da wadda ta gota. Yawancinsu (kashi 90 cikin dari), cikin wata shida na aure suke samun juna biyu. Wadda ta haura 35 sai an dan sha wahala domin kwayayenta na raguwa ne daga wadannan
shekaru. Shi ma namijin da ya haura shekaru hamsin, kwayayensa na kasa sosai.
Amare masu son samun juna biyu da sauri, kamata ya yi da sun shiga gidan miji su fara shan kwayoyin magunguna na bitaman da folic acid domin taimakawa kwayayensu A bangaren lafiya masu cututtukan suga ko hawan jini ko ciwon sanyi ko na damuwa, namiji ne ko mace, su san
cewa su ma a lokuta da dama sukan dade kafin su samu rabo. Yawan aiki ba hutawa da taba sigari da barasa duk sukan lalata kwayayen mace da na namiji, haka ma kiba.
kwayoyi ko allurar hutun haihuwa ma za su iya kawobjinkirin samun juna biyu ko da an bar shan su. Ta bangaren ilmin zaman aure kuma dole mace ta sanbcewa akwai ranakun da ko mai gidanta ya kusance ta ba za a samu komi ba, akwai kuma ranakun kuma da akan yi dace. Ya kamata mace ta san cewa ranaku goma zuwa sha biyar bayan al’ada su ne ranakun da ba kwai a
mararta, kuma da wuya a samu juna biyu, ranaku goma zuwa sha biyar kafin wata al’adar su ne na kyautata zaton samun rabo. Daga lokacin da mace ta saki kwai a mararta zuwa fitowarsa cikin mahaifa, da yin jinin al’ada kwana biyu ne zuwa uku kacal.
A daidai wannan lokaci kuma idan mace ta auna duminbjikinta da na’urar thermometer, za ta ga ya dan yi sama kadan, idan ita mai amfani da wannan dabara ta sanin ranakun fitowar kwayayenta ce ke nan.
Shi kuma kwan namiji yakan iya kwanaki hudu ko ma biyar a mahaifar mace yana jiran kwan nata. Ke nan kwanaki biyar zuwa bakwai na dab da al’ada su ne aka fi alakantawa da sa’ar samun juna biyu.
Yawan tafiye-tafiyen mai gida ke nan kan sa irin
wadannan ranaku su subuce.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
SHAWAR-WARI GA MACE ME CIKI:
Y'ar Uwa a musulunci: wadannan wasu shawar-wari ne da likitoci suke baiwabMace me goyon ciki, da fatan zaki kula da su da kyau.
1. Ki baiwa abinda ke cikin ki kula matuka, saboda kisami lafiya da kubuta, ke da abinda ke cikinki insha Allahu.
2. Yakmata ki dinga cin abinci sosai, irin wanda yake gina jiki, ta yanda zaki sami lafiya, da d'an dake ciki.
3. Ki dinga cin kayan mar-mari, kaman su kwad'on ramabko latas da makamantansu a kowace rana.
4. Ki dinga shan kaman kofi hudu na madara, ko nono a kowace rana.
5. Kada ki dinga yawan Shan Shayi mara madara, ko Nescafe, ko cin albasa, ko cin yaji a abinci, domin ha………
6. Kada ki dinga shan magani, ba tare da shawartan likita ba, saboda hakan ze cutar da yaron, kai yana temakawa wajensa Yaron Muni.
7. Yanada kyau a rage saduwa da Iyali, lokacin da cikinbyake wata uku, da kuma watan karshe na haihuwa, yawan aikata hakan yana tasiri ga lafiyarki da ta Yaron.
Sannan saduwa da mace lokacin da take cikin jinin haihuwa yanada cutarwa ga mace, saboda hakane musulunci ya haramtashi.
8. Rashin yin barci da wuri, ze sanya maki damuwa, saboda haka dolene kiyi barci na Awa tara a kowace rana, a tsawon lokacin goyon cikin.
9. Kada ki dinga yin aiki me wahala da d'aga abubuwa masu nauyi, domin hakan ze Iya samar da matsala gab cikin.
10. Ki lazimci Natsuwa, da rashin yin fushi, sakamakon wasu matsaloli na gida, ko na Y'an Uwa, saboda ki samu kwanciyan hankali, ana buk'atan hakan dan cikin yatafi yanda akeso, batare da wata matsala ba.
11. Kada ki dinga ziyartan marasa lafiya, masu dauke dabciwon daza'a iya kamuwa dashi, don ze zama hatsari agareki da kuma danki.
12. Kada ki dinga sanya tufafi masu matse jiki, ko daure ciki da k'arfi tsawon lokacin goyon cikin, dan yin hakan ze saki gajiya, da shan wahala wajen yin numfashi.
13. Kada ki dinga sanya takalma masu tsawo, wato masu dogon k'wauri dan ze sabbaba rashin walawa a gab'ubb'an jikinki, wanda hakan ze samaki ciwon baya.
14. Dolene ki dinga yawan ziyartan likita akai-akai,
tsawon lokacin goyon cikin, Sau d'aya cikin l kowani wata cikin wata shida na farko, da kuma sau d'aya cikin kowani sati biyu, a watana bakwai da na takwas, da kuma sau daya cikin kowani sati, a watana tara har zuwa lokacin haihuwa.
15. Ki dinga yin gwajin jini da na fitsari, lokaci zuwa lokaci saboda ki tabbatar cewa: jikinki baya dauke da wani ciwo da yaron ze iya kamuwa dashi, kaman ciwon sukari da makamantansu.
16. Dolene ki dinga yin wanka a kowace rana, a duk Lokacin tsawon goyon ciki, da lokacin shayarwa, dan ki kare lafiyarki, da na yaronki. Insha Allahu.
17. Ki dinga kula da mamanki, tun daga wata na biyar da samun cikin, saboda shayar da danki mama na asali.
18. Ki dinga tafiya da k'afa a kowace rana, gwargwadon iyawarki, hakan ze kyautata maki jinin jiki lokaci zuwa lokaci, ya zama abinci ga danki, kuma ya sauwak'e maki haihuwa.
19. Anason haihuwa a asibiti, saboda samun kula da Uwa da danta, kuma babu laifi ta haihu a gida idan ta shawarci kikita ya tabbatar mata da cewa duk abinda ya shafeta da d'anta yana tafiya daidai, kuma ya nisantarda samun wata matsala, kuma yazama akwai abubuwan da suka shafi samun lafiya a gida.
20. Ki dinga yin ayyukan gida, ke da kanki bayan kin haihu da y'an kwana kadan, domin hakan zesa mahaifarki ta koma yanda take ada, ya karfafa maki gab'ob'in jiki, kuma ya hana …..ciki da k'irji, kuma ya temaka wajen samar da mama ga jariri.
Allah nake roko da ya sauwak'e maki wahalhalun
haihuwa kuma ya baki zurriyya.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
ABINCI MAI CIKI:
GUZURIN JIKI :
Abinda gangar jikinta yake bukata sune kamar haka :
- Hutu tare da kwancyar hankali.
- Ta yawaita cin ganye (Kayan lambu) da kuma 'Ya'yan itace.
- Ta rika motsa jiki lokaci lokaci domin jinin jikinta ya rika zagawa sosai.
- Ta rika shan shayin ganyen Na'a-Na'a domin samar da Qarfin jiki da kuma Kaifin basira ga jaririnta.
- Ta rika amfani da Zuma domin samar da kuzari da kuma riga-kafi gareta da kuma jaririnta daga chututtuka.
- Idan lokacin haihuwarta ya kusanto ta nemi dabino danye nunanne (irin wanda ake kira Siki) ta rika yawan cinsa. Idan bata sameshi ba, oda busashen ne ta rika amfani dashi.
- Shan dafaffiyar garin hulba shima yakan yi amfani ga masu tsohon ciki. Yakan bama mahaifar Mace karfin turowa jaririn idan lokacin fitarsa yayi.
Ki rika shafa Man Tafarnuwa ko man Jirjir ko man
Habbatus sauda domin magance ciwon Qafa din.
Wadannan duk ba zasu chutar da mai ciki ba. Koda shansu akayi.
Amfanin da shan rake ya ke yi wa mace mai ciki, da wasu 9 Duk inda ka hadu da gungun mutane suna zaune ana ta yada zantuka ba birki, sannan baki kuma na ta motsawa, to ina tabbatar maka cewa ana shan rake a wannan wuri.
Ko da yake sau da yawa, akan dan daga wa mai shan rake kafa a bashi uzuri saboda ganin yakan shiga wani hali na zautuwa idan ba a taro shi ba musamman idan anyi dace da raken mai zakin gaske.
Sai dai kuma wani hanzarin ba gudu ba, rake na da matukar amfani a jikin mutum wanda da yawa ba su sani ba.
Ga amfanin da rake take yi a jikin mutum.
1. Rake na kara karfin kashi domin tana dauke da
sinadarin ‘Carbohydrates’.
2. Rake na dauke da sinadarin ‘Vitamin A’ wanda ke kara karfin ido.
3. Shan rake na kare mutum daga kamuwa da zazzabi musamman idan aka matso ruwan aka sha.
4. Rake na hana lalacewan kumba,karyewa ko canza kala.
5. Rake na sa rauni ya warke da wuri.
6. Yana kuma taimakawa wajen samun kaifin
kwakwalwa.
7. Shan ruwan rake na taimakawa wajen kawar da warin baki da lalacewar hakora
8. Shan rake na kwara da matsalar rashin haihuwa ga matan da ke fama da wannan matsalar, yana kuma bunkasa girman jinjiri a cikin uwar sa sannan yana hana mata masu ciki yin bari.
9. Rake na taimaka wajen hana jiki ya nuna tsufa da wuri.
0 Comments