YADDA ZAKI BUDE GMAIL KO YOUTUBE

YADDA AKE BUDE GMAIL ACCOUNT
Gmail account dinka, shi ne Google account, kuma idan ka mallaki Gmail Account, zaka iya amfani da username da password din daka bude kayi amfani dashi wajen bude wurare kamar haka;

+ YouTube,
+ Google+,
+ GTalk
+Google Play, da kuma
+ Google Drive.

Wadannan sune sauran google Product, wadanda basa sarrafuwa sai da gmail account.

Idan nace Gmail Account wasu sukan dauka, shi Gmail, yana matsayinsa na Gmail saboda da haka Yahoo shi ne email. Ba haka bane, dukkansu kowannensu mail ne, hasalima Gmail yafi yahoo muhimmanci, saboda akwai abubuwan da basa sarrafuwa yadda ya kamata matukar babu shi, kamar wadanda na lissafo asama, amma shi Yahoo bashi da irin wadannan wuraren dayawa, imma akwai.

Sannan zaka iya bude Gmail ta cikin ko wanne daya na wadancan account dana. Lissafa, kuma yayi aiki adukkansu, sannan shi Gmail account zaka bude shi ne, sannan ka samu Google+ kai tsaye, saboda suna tare da Gmail a hade, zasuyi amfani da profile dinka ne, su kirkirar maka Google+.

Misali idan ka bude gmail ta Youtube, ko kuma ka shiga Youtube kasa Gmail dinka, zaka samu damar dora Video akan shafin, baima tsaya nan ba, zaka samu damar yadaa Document dinka a Google Documents.

Da farko idan kana bukatar bude Gmail Account, saikaziyarci shafin gmail.com zaka inda kasa "Create Google Account" saika latsa wurin.

Ka zabi sunan kasarka, sannan Kasa Lambar wayarka idan sun bukaci hakan, kuma kasa lamba wacce ka tabbatar tana aiki, kuma. Tana kusa da kai, domin idan kasa lambar wayarka zasu turo maka da Link wanda zaka bi domin ka Mallaki Gmail dinka kai tsaye.

Amma ka tabbata kasa Username dinka wanda ya dace kuma bazaka manta ba, sannan kasa password dinka wanda kasan bazaka. Manta da shiba, username dinka shine kamar. Haka;

username@gmail.com
Sirrinrikemiji@gmail.com
Sirrinrike miji@gmail.com
Facebook@gmail.com

Wadannan duka musalai ne nake baka, saika tsara naka. Yadda ya dace, sannan ana iya sa masa lamba agabako a farko, ko a tsakiya, misali:

Sirinrikemiji@gmail.com
Sirrinrikemiji@gmail.com

Amma shi wannan yana faruwane a dayan biyu.

1. Zaka iya amfani da lamba idan kasa naka amma akwai wani mai irinsa, dole bazasu karba ba, saika bam-banta.

2. Ko kuma kana da ra'ayin saka lambar.
Kasanipassword na gmail naka, dole ya zama daga harafi 8 zuwa 32, sannan. Basa karbar Dictionary words.

Kana iya bude. Gmail akowanne wuri, sannan kuma tayi maka amfani aduk inda ya dace.

Domin mallakar YouTube channel, sai ka bi wadannan matakan:

1. Ka fara bude Google account ko kuma Gmail ( Shiga nan don ganin yadda ake bude gmail )

2. Sai ka shiga YouTube (idan son samu ne kayi amfani da computer don yafi sauki)

3. Bayan ka shiga sai ka je daga can saman page gefen dama (idan da computer kake amfani), ko kuma can kasan page din (Idan da waya kake amfani), zaka ga inda aka sanya sign in, sai ka shiga nan.

4. Da ka shiga sign in za ga inda za ka sanya Username da password, sai ka sanya gmail address naka a matsayin username, da kuma password dinka da kayi amfani da shi wajen bude gmail din. Idan ka sanya komai dai-dai, wannan zaya ko ma da kai a page din YouTube.

5. Idan da computer kake amfani, sai ka duba daga banagaren hagu akwai waya ‘yar alama sai ka taba ta. Wannan zaya buda maka zabukan da ke a gurin, sai ka shiga ‘My Channel’

6. Da ka shiga ‘My Channel’ zaka ga wani page da za ya bukaci kayi setting na Channel dinka (kamar sunan channel din dai sauransu)
7. Da zaran ka shiagar da bayananka sai ka sanya create.

Wadannan sune matakan da kake bukata domin bude channel ko kuma tasharka a shafin YouTube. A cikin kasidarmu ta gaba, in Allah ya so, za mu yi Magana akan yadda zaku iya dora videos a saman wannan channel naku na YouTube.

Post a Comment

0 Comments